← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 104

Sashe 55

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page5 Malamai zan shiga, ke koh yawo tsirara zanyi don naga bayan sumayya sai nayi Amma dai kamila baki da imani habba don Allah kin wulakanta bawan Allah ya fita a Rayuwan ki sannan yanzun kice zaki wargaxa masa farin ciki ai wannan baso bane Wace farin cikin bayan nice farin cikin sa har gobe ina da gurbi a zuciyar sa Hhh hayya lallai kamila kina da gurbi a zuciyarsa ya hankad'aki akan matar sa koh an gaya miki so na dauwa mane a zuciya? duk mai sonka muddin baka kyautata masa toh fa kamar fure ka shuka baka ban ruwa tum tana bushewa aje aje wata rana zata mutu Kee sadika na fahimci daman ke yar hassada ce shiyasa kwata kwata tafiyyar mu bata kyau dake Nidai gaskiya nake fad'a miki kamila kuma gaskiya d'aya ce da wannan haukar ai gwara kije garesa da soyayya koh xai dawo ku daidai ta kinga sai ayi na biyu dake Ina ma yake fita kullun yana gida, naje inda akace min yana bude sana'a ma naje Amma shuru bantaba ganin sa ba, kuma ni nafi karfin kishi da sumayya sai dai ta fita tabar min shi iii in kamila karkije kikai kanki a mahallaka wallahi wani rabon kashe ki zaiyi Ya kashe ni mana indai akan Al'ameen ne kowa ma ya mutu Wallahi badai kowa ba, nidai mai sonki ce zan fad'a miki gaskiya koh kinki koh kinso rabuwa da bayin Allah nan shiyafi miki mutunci Akasinsa kuma bismillah zaki ga. Bakin ki ya sari d'anyen kashi ba abinda zan gani sai Alkhari Ai baki neme Alkharin ba mutumin da keson kashe Auren wasu shine zaiga Alkhari?tace tana Mikewa tayi ba tare da tajira Amsar kamila ba tayi mata sallama ta fita a asibitin Sumayya na shiga cikin gidan kofar su ta wuce da mamaki take kallon kadija dake zaune tana rusa kuka"ke khadija lfy"? Da gudu ta tashi zuwa wajen sumayya rungume ta tayi tana kuka'Aunty ina yaya? ina dawowa daga makaramta ake ce mini wai an tafi dake da yaya,. "Babu inda akaje damu khadija yayan ki na waje shine kika kama kuka koh uniform baki cire ba kika zauna haka" Toh ni Aunty fisabililah yazanyi na cire uniform yayana da Aunty na na station "Toh gani na dawo ki ibi ruwa kiyi wanka na baki kaya kisa dai dai yayan naki ya shigo" Toh kawai tace tana d'aukar boket, wanka tayi sumayya ta bata kayanta ta saka abincin da suka girka na karyawa daba su ciba shi ta ibawa khadija Khadija na cikin cin abinci sai gashi ya shigo da sallama Amsa wa khadija tayi hade da gaidashi, yaya sannu da zuwa Yauwa khadija ya makarantar Lafiya yau subject 6 aka mana a rana d'aya Assignment biyu Masha Allah ki gama ci sai muyi assignment in Hhh yaya ka iyya ne? Toh khadija ba nayi secondary ba koh azatan ki duk abinda na koya ya gudu ne? Yi hakuri yayana D'akin ya shiga sumayya kam daman tana kitchen Bayan khadija taci abinci wanke uniform nata tayi ta shanya,school back nata ta d'auko ta bude Assingment ne aka busu na physics sai English, yaya na gama inzo muyi Assingment in? Bara na fitoh khadija, Toh yaya Fitowa yayi suka zauna a dakali sumayya na kallon sa yana ma khadija bayanin assingment in yanda zata fahimta sannan yana fad'a mata Amsa tana rubutawa Bayan sun kammala gida khadija ta tafi tabar uniform nata a shanye, mikewa yayi ya ibi ruwan wanka ya shiga yana fita yayi Alwala ya wuce masjid Bayan fitarsa da ido sumayya ta bisa haka kawai yau taji tana jin shakkarsa sosai abinci ta juye a kula takai d'aki tayi sallah sanin baya dawowa sai bayan isha yasa tayin wanka d'akin ta shiga zani fille da T-shirt ta saka sai hulan bacci. TV ta kunna tana kallo gabaki d'aya yau ta rasa nutsuwar ta gabaki d'aya zuciyarta cike yake da tsoro Bayan ya dawo sallah abinci ta gabatar masa baiyi magana ba kawai ya zauna ya fara ci Itakam taji ba dadi koh fad'ane ya mata akan wannnan shariyan ba karamin damunta yake ba Bayan sun kammala cin abincin wanke baki sukayi, Al'ameen kwanciya yayi a gadon yayi shuru baice mata kome ba Sumayya dake kwance a gefensa hawaye ne ya cika a idanunta itakam ta shigesu da mutumin nan Sunfi, minutes 30 a haka baice kome ba itama batayi magana ba Amma kowa yasan d'an uwansa baiyi bacci ba A hankali sumayya ta matso garesa kwanciya tayi a gabansa sosai ta shige jikinsa Al'ameen yana jinta kala baice mata na shuru kawai yayi don so yake ya mata horo ta ruwan sanyi yanda gobe baza tayi Abinda bayaso ba. Hannu tasa a hankali ta na cire botur in shirt insa nan ma baiyi magana ba "Ni da wannan fushin ai gwara duka da wannan shariyan" Kala baice mata ba sai kama hannunta dayayi wanda ke yawo a jikinsa "Dan Allah ka kulani" Kinsan Allah sumayya in baki rabu dani ba sai na sauka a gadon na koma kan kujera habba Ana dole ne? "Kayi hakuri bazan kara bafa" Sauka yayi niyar yi da sauri ta riko sa hade dasa ihu"wallahi nidai ban yarda ba kayi hakuri toh na tuba" Fasa saukar yayi ya koma ya kwanta itama kwanciyar tayi a gabansa sosai ta mannu a jikinsa Haka suka kwana tsakanin su babu shiri sumayya dai na makale da muhammad duk yanda yaso cireta a jikinsa taki Washe gari haka suka tashi salam Al'ameen yasha mata mur sosai duk yanda tad'au abin da sauki abu fa ya wuce nan don da gaske muhammad yake Bayan sun karya ta d'aga ido tana kallon sa"yayan khadija" Na'am "Daman maganar make-up inda zan ma yar kanwar Deputy ne saboda tsaro bazasu iyya zuwa ba shine wai naje na musu a gida har kwana biyar ana biki" Saikin dawo kawai yace yana fita a d'akin Sosai shariyan Al'ameen ya damu sumayya, haka dai ta lallaba ta shirya tad'au hijab nata ta saka rufe kofar tayi ta fita. Bakin titi ta tsaya idonta ya sauka a kan Al'ameen ne zaune a bakin masallaci kusa da masu bara suna hira dasu, kara sowa tayi inda suke bakin ta d'auke da sallama, "Assalamu Alaikum" Mutanen bakin masallacin gabaki d'aya suka zubawa sumayya ido suna mamakin ina zata, wa'alaikumu salam su Al'ameen suka had'a baki wajen Amsawa shikam cike da mamaki meya kawo sumayya gunsa bayam tace gidan deputy zata, tashi yayi ya matsa gefe Binsa sumayya tayi inda ya tsayan ba mutane, itama tsayawar tayi batace kome ba Lafiya? "Lafiyar kenan koh laifine in nazo wajen ka"? Babu laifi... "so nake ka rakani" Rakaki ina?da mamaki a fuskar sa "Gidan da zanin mana" Hala baki gani ne? "Ah ah ina gani so nake ka rakani" Bazani ba, yace yana tafiya Ai da sauri sumayya ta riko rigansa Keee menene haka? koh baki ganin a gaban mutane muke ne "Toh sai me in a gaban mutane muke koh ba mijina na rike ba kuma wallahi in baka shige mun tafi ba saina rungume ka a gabansu" Uhmm Allah ya kyauta shige mu tafi Mutumin da ke saida ruwa kusa dasu Al'ameen ne ya dubi abokin sa, Kai Amma yariyar nan bata da kunya har masallaci zatabi miji bata maji kunyar idon mu ba muna zaune? wama yasan dalilin da yasa aka aura masa yarinya kamar wannan? Gaskiya ne haruna daga gani idon yarinyar a tsatsaye yake.. Haka sumayya tasa muhammand a gaba har gidan kanwar deputy har falon baki aka kai Al'ameen aka had'asa da abin motsa baki sumayya kuma ta shiga falon matan gidan Har yamma suna gidan sallah kawai ke d'aga Al'ameen yaje yayi ya dawo Sai kusan 5:43 na yamma suka fitoh gida gaskiya sumayya ta yaba da karamcin y'an gidan don Take Away na abubuwan da aka shirya na biki aka iba mata" yanzun ina zamu"? Sama jannati zamu, Al'ameen ya bata Amsa "Ni kake fad'awa bakar magana"? Eh an fad'a in ai nafi mai Ashar kuma bakar ma agunki na koya "Badai aguna ba kuma in kayi tsiya saina gudu na barka ka bata" Kanki kika ma Asara bani ba. "Akan me xan ma kaina asara kuma"? Aikan mijin da kike dambe mana "Dambe ni banyi dambe akanka ba" Au habba daman tabaryar ta burgane? "Ai na razana tane, karka wani zata fad'a nake akanka" Na nawa kuma. "Allah ba wani" Ke kika sabi dai mutum sai taurin kai "Kamar kai" Shuru ya mata don ya fahimci sumayya inya biye mata fuskar da ya d'aure bazai san lokacin da zai sake ba. Keke suka hau suna isa gida ana kiran mangari ba masalaci ya shiga ita kuma ta wuce cikin gida Bayan ya dawo sallah take Away in ta bude musu donut da kaza rabi sai drinks d'ayan take away in kuma fried rice ne da lafiyayyen naman shanu suna kammala ci, muhammad kam kwanciyan sa yayi Sumayya TV ta kunna ta koma ta kwanta tana kallo a kwance"yayan khadija"ta kirasa tana kallonsa ganin ya natsu waje d'aya yana tunani, jin bai Amsa ba yasa ta dafa kafad'an sa Da sauri yace Am Ammar kudin nan basuyi yawa ba, sai kuma da sauri ya fara kame kame don sam subutar baki ne abinda ke zuci shiya fitoh fili "Wani kudi kuma Waye Ammar"? Am ba kome. Akan me zakace ba kome duk kabi kasa kanka a damuwa in ma bashi ake binka bazaka fad'amin na biya ba duk kudin da nake tarawa Wallahi tatali nake maka naga kudin yayi yawa sosai kafun na baka ka kama sana'a mai d'an kauri mu samu murufawa kan mu asiri, amma ina dalili ina dana rufin asiri kabar kanka a rikici" Ba haka bane sumayya ba'a rikici zansa kaina ba wannan magana ne daban. "Wace magana kenan?koh bankai naji damuwar kaba"? Daman Ammar ne ya mini magana jiya zai bani jari dubu d'ari uku na kama shago kafun azumi tunda saura sati biyu ne ga kayan marmari a azumi akwai kasuwa. "Bazai yuba wani ma Ammar inne d'aya? akan me zaice zai baka kudi tun da baisan zai Taimake kaba sai yanzun" Sumayya bamu fa dade dashi ba kuma insha Allah ba abinda zai faru
Chapter 55 · 0% Book details