← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 104

Sashe 6

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yace mini "No ba kome tunda kayan miyar safiya zai Mana kwana biyar Koh hudu" kaga daidai ya kare ka biyani kudina, Ok sai na dawo"toh" nace Masa yasa kafa ya fita *Komawa nayi na zauna Ina maijin haushin kaina Dana sake baki Ina tanka masa, kunna TV nayi ga fanka na kadawa k'wanciya nayi Ina kallo,Tashar zee cinema ana kallon wani film Mai suna bang bang sosai film in yamin dadi, 10:00pm naji sallaman Khadija mikewa nayi Ina amsawa na fito waje itace tsaye hannunta d'auke da kulan jiya, Ina kwana Aunty, "Lafiya Alhamdulillah ya Goggo"? Lafiya tace a gaidaki, "Aiko Ina amsawa" "Ki shigo mana" ah ah Aunty tafiya zanyi yanzun " Aiko baki isaba shige muje ciki yau ini zamuyi" Ba musu ta shigo dakin Muka zauna muna kallo sai 11:00 na mike na shiga kitchen Zan fara aiki, sai ganin Khadija nayi itama ta shigo, "Ah ah fa Khadija yau Kam zama zakiyi ki huta" Yanzun Zan kammala " Ah ah Aunty wallahih bazan iyya zama kina aiki ba Zan dai tayaki, Ba yanda na iyya haka Muka Kama aiki sai 1:30 Muka kammala tuwo da miyar kuka, nayi Tuwon da yawa harda na dare kawai, na huta d'aura sabo, zubawa yayan khadija,akula na zuba na dare a wani kulan na rufe, mukayi sallah ta Kai masa nasa, tana dawowa na zuba Mana munaci muna Hira, "Nikam Khadija wani school kike zuwane"? Aunty bana zuwa makaranta ai "Ban gane ba Khadija" Eh na kammala junior set. "Shine zakice kin Gama karatu"? Eh Aunty na Gama jss 3 Amma ban daura senior set ba "Me yasa"? Shuru tamin Naga alama batason bani Amsa ,Nima ban takurata ba, Na chanja zancen da, wani, "Khadija nikam akwai Wanda kika sani ne? ta iyya kitso, budurwa haka tazo tamin a gida Koh guda shida so nake na wanke kaina" Aunty Baga kanki a tsefe ba bazaki wanke ba sai an kitsa? "Aii Khadija bana iyya wanke Kai a tsefe sani ciwon Kai yake" Lallai Kam aunty bara mu kammala ci na kama Maki Kan in mun gama, "Au kin iyya kitson kenan"? Zandai Kama Miki, "Koh Zaki chanchara mini ba" Hh toh na yarda. Muna Gama cin abinci Khadija ta Kama mini kaina guda shida, na tashi naje nayi wanka na hada da Kai, *Sai dana rike Khadija har yamma kafun na barta,ta tafi, Sai yamma ya dawo Kamar yanda ya Saba haka yauma yayi wanka da sallah sai Isha mukaci abinci yau akwai NEPA tun na safe har yanzun Basu dauke ba dukan mu muna zaune a daki Ina kallo shima dai idonsa biyu, sai 10:25 na sa kayan bacci muka kwanta, Misalin karfe daya na dare na farka da wani irin azababben ciwon ciki Wanda tunda nake da wayo bantaba yin irinsa ba, Mai tsanani gaskiya tun Ina daurewa har dai na fara kuka Ina nishi duk iskan fankar da yake kadawa a dakin gumi nake, Cikin bacci yakejin kuka-kuka, Nishi daga ji na azaba ne, cikin D'an hanzari ya mike ya sauka a kujiran cikin azama yake magana muryarsa na rawa,Jin da gaske Sumayya ce Mai kuka da Nishi Sumayya!! Sumayya!! Lafiya kuwa ya fada Yana laluben inda nake, nikam saban azaba nama tsullubo kasan cafet daga Kan gado Ina durkushe reke da ciki,Koh amsa na kasa basa, Da lalube ya lalubo ni kafada ta ya dafa yana cewa, muryar sa na rawa,Sumayya lfy meke faruwa ne kimin magana mana, "cikina " nace Ina Kara fashewa da kuka, Hankalin sa in yayi dubu ya tashi, hannu yasa ya dauke ni cak kamar ya dauki Yar baby da lalube ya daurani akan gado. Nikam tashin hankali Bai barni nama San ya dauke ni ba, tsaban azaba, jikina har bari yake ,, sosai hankalinsa ya Tashi ,mikewa yayi zai fita cikin rawan jiki na kama Masa hannu na damke cikin nawa dake rawa sosai, ciki muryan ciwo yaci karfina nake cemai"D'an Allah karka tafi ka barni Zan mutu ka mikamin waya ta na Kira babana karna mutu" Sosai zuciyarsa ta tsinke Jin tana am batar mutuwa,Amma ya daure cikin sanyi murya yake cemin Kinga yanzun dare ne Bai kamata ki kirasa a daga Masa hankali ba, bara naje Koh Allah zaisa na samu iro ya kaimu asibiti da keke napep NASA kinji, sannu, **Gaskiya ya fada hakan yasa na sakar Masa hannu ya fita, Waje ya fita Yana lalube ya dauki sandar sa a dakali da lalube ya fita a kofar shashen Yana lalube harya Isa hanyan kofar gida wanda ke dauke da d'akunan samarin kusan bakwai, a kofar dakin iro ya tsaya ya fara buga Masa kofa Yana Kiran sunan sa, Cikin bala'i ya bude kofar ya fitoh kai don Allah lafiya Ina cikin bacci karfe daya zakazo ka bugamin kofa Dan wulakanci kome,? Don Allah iro ka taimake matatace ba lfy sosai shine nace Koh zaka taimaka mini ka kaimu asibiti, Buran uba a Daren nan ba shegen da ya isa yasani in fitoh wallahih Koh inno ne ba lfy ba inda zani bare wata banxa Wai matarka don Allah ware ka ban waje nikam, Yana Gama masifar ya koma daki ya banko kofar, Haka ya juya don yasan tunda har iro yace bazai taimake Saba ba Wanda ya Isa yasa sa daukan su , waje ya fita Amma titi shuru. Ba motsin kome,yakai minutes 30 baiji motsi ba dole ya hakura haka ya juya da sanyin jiki ya koma cikin gidan,kofar ya shigo cikin hanzari ya Isa dakin har yanzun dai kukan take,gadon ya hau a hankali ya Isa gareta cikin sanyi yake ce mata, don Allah Sumayya kiye hakuri wallahih ban samu abin hawa ba, cikin muryar kuka nace "ka dubamin wayata tana Kan dressed mirror,ka bani na Kira Abie" Ba yanda ya iyya dole ya Bata wayar ganin irin azabar da take Sha gashi ya kasa Nemo Mata mafita ga ciwo na cinta, Sauka yayi a gadon Yana lulube harya gane dressed mirror in, har Allah yasa ya samu wayar mikamata yayi, Karba nayi cikin Nishi nake lalubo number Abie na na Kira yakai sau biyar baya dagawa Daman tun Randa aka kawoni gidan nan Koh na Kira sa baya dagawa sai ana biyar in nayi sa'a ya daga cikin muryar kuka nake cewa abie Zan mutu cikina ciwo kazo ka kaini asibiti,, abinda naji abina ya fada shiya Kara hargitsamin k'wak'walwa, yau nice yau abie ke cewa Inna mutu baida asara Kuma karna sake kiransa tsakiyar dare Yana bacci, **Anya abie nane kuwa? Mai Sona da tausayina Mai son ganin farin ciki na yake furta wannan magana gareni,shikinan shima abie yanzun baya Sona wayar na sake daurawa a kunne na Amma abie ya kashe call in ban daddara ba na sake kiransa wannan Karo Kam line busy ya Danna mini. **Me nai Masa lfy lfy Muka rabu cikin kewan juna da Addu'a tare da fatan alkhari hade da nasiha, bansan lokacin da wani sabon kukan ya barke,min ba Sosai hankalin Al'ameen ya Tashi baisan lokacin da ya iso garita ba ya Kamata ya runguma cikin wani irin yanayi na tashin hankali yake lallashin ta, **Kara rungumar sa nayi na yenyene Masa ajikinsa Ina kuka maitaba zuciya wannan kukan bana ciwo bane kadai harda na bakin ciki Abiena shima ya juyamin baya adaidai lokacin da nafi bukatar sa, Haka nayi ta fama da ciwo daga ni harshe bamu rintsa ba sai addu'i yake tufa mini har hudu na asuba, Yaji taja numfashi da karfe sai Kuma yaji kome nata ya sake Daman har lokacin tana jikinsa, cikin wani irin rikice wa jinta ta Bata motse yasashi mikewa ya sabeta cak a kafada Yana lalube ya fita a dakin Koh kofar Bai rufe ba tsabar tashin hankali,fita yayi a shashen yayi hanyar kofar gida.............. *masu Tambaya na complete in MATAR MAKAHO* , *A Ranan 30/8/2021 na fara Post na novel innan bani da complete* My WhatsApp number *MATAR MAKAHO* ~ Na ~ *Rukayya Ibrahim* Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa Free book *More comments* *More post* Page9 Haka ya ringa lalube don Koh sanda Bai rike ba ya fita waje, da ita,yaje titin shuru haka ya ringa takawa a Gefen titi ba tare da yasan inda zai nufa ba, cikin ikon Allah sai ga wani Mai mota yazo wucewa ganinsu cikin wani Hali yasa shi tsayawa a saitin, Al'ameen Yana tambayar sa lfy kuwa ya gansa da mace a bakke a kafada Bata motse gashi Koh takalmi babu a kafarsa da asuban nan? Da sauri ya juyo wajen da yakejin muryar Mai motan don Allah ranka shi Dade ka taimaka mini matatace ba lfy wallahih tun jiya yanzun haka Suma tayi Ina son kaita asibiti Amma ban samu abin hawa ba, Allah sarki shiga muje Nima kwanace ta kamani a hanya sai yanzun na shigo gari, Allah ya saka nagode,ya fada Yana laluben murfin mota tsabar tashin hankali Yama kasa budewa ,abin ya bawa Mai mota mamaki, yadai malam lafiya Naga kana lalube baka shiga ba,? Bana ganine,ka taimaka ka bude mini, Ba karamin mamakine ya Kama Mai mota ba ace mutun Kamar Wannan baya gani lallai Koh wani bawa da kaddaransa, Fita yayi yazo ya bude Masa A hankali ya shimfida Sumayya asset in baya shima ya shiga Mai mota ya rufe ya zagaya shima ya shiga mazauninsa yaja motar , Wani asibiti Zan kaiku? Duk asibitin da yafi kusa damu ka kaimu Ok ya kara gudun motar lokaci kankani suka iso FMC don yafi kusa da SINTALI ( sunan unguwansu Al'ameen) Suna Isa emergency Mai motar ya kaisu fita yayi ya shiga Hall in ya Kira nurses za'a d'auki Mara lafiya suka fitoh da sauri aka aza Sumayya bisa keken marasa lfy aka wuce da ita dakin taimakon gaggawa, Likituti suka,rufu a kanta don Bata taimakon. Gaggawa shi kuma nurse tace Masa yaje ya sai Mata card a bude mata file, Wajen sai da card in ma da taimakon Mai motar ya gane, kudin card naira 300 matar da ke windown tace, ba karamin tsinkewa yayi ba sai yanzun tunaninsa ya dawo jikinsa, don Koh sisi baida shi sai naira dari da hamsin na cinikin jiya, ya Allah ka taimake ni abinda ya
Chapter 6 · 0% Book details