← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 104

Sashe 34

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page 3 Kamila kice Koh dai Mai irin muryar tane, Al'ameen yace cikin d'unbin mamaki Ikon Allah Ashe da rabon za'a sake ganin juna Muhammad,kamila tace tana me Kara kallon Al'ameen Wallahih fa kamila yace Yana isowa kusa dasu sumayyar Oh duniya Muhammad Daman a unguwan nan kake? Anan nake kamila,ya bayan rabuwa ya maigidan ki da yara? Jiki a sanyaye kamila tace,hmm muhammad mijikam aure ya kare, yara Kuma Allah Bai kawo ba tukum. Allah ya kawo masu albarka Ameen Muhammad,Amma nayi mamaki wallahih wannan ce matar ka,ta fad'a jikinta na Kara sanyi tunawa da abinda ya faru a shikarun baya da suka wuce Eh kamila matatace sunanta Sumayya Masha Allah gaskiya matakam tabar kalla Masha Allah wallahih gata kyakkyawa son kowa kin Wanda ya rasa,tace tana kallon Sumayya har lokacin Haka Allah yake abinsa sai ya baka abinda baka taba tunani Koh tsammani ba, shiyasa duk abinda bawa ya samu a rayuwa rabonsa ne ba Mai hanasa muddin Allah ya basa Gaskiya ne muhammad,Aiko shikenan Daman kwalliya nazo tambaya Allah dai yasa madam in zaka barta ta koya mini,tace tana Mai Al'ajabin Rayuwa su kamila kenan yaushe Kika dawo Jala ne? Shap aini na jima a Jala, Amma Dad nawa transfer mun dawo nan Allah sarki toh ya gidan naku da aiki? Gida Alhamdulillah aiki Kam Babu sai karatu. Karatu Kuma,kamila? Eh Mana ai kasan bayan rabuwar mu aure nayi sai karatun ya tsaya sai yanzun na samu na Shiga TSU Gaskiya ne Allah ya bada sa'a.. Ameen, muhammad Kai ya lbrn karatun? Kai kamila wani karatu Kuma makaho talaka zaiyi ba kudi ba ido ya fad'a Mata maganar cikin murmushi Sosai taji wani abu ya Tukare Mata makoshi Jin kalaman da ya fad'a ya tuna Mata da kuskuren da ta tafka a rayuwar ta tabbas Al'ameen Mai hakuri ne da wanine haduwarsu yanzun bazai ma saurare taba Cikin sanyin jiki tace,toh nikam Zan tafi Sumayya saina jiki Koh,ta fad'a tana kallon Sumayya dake zaune a Kan darduma Sumayya Kam ba karamin haushi taji ba Kamar ta tashi ta Basu waje, Amma saita maze gudun karta bada kanta agun kamila,"yauwa"kawai tace tana kallon kamila dake Shirin fita a kofar Sumayya! Al'ameen ya Kira sunan ta Kin amsawa tayi Tamar kunnen uwar shegu Sumayya Koh kin tashi a wajen ne? Nan ma Sumayya kin amsa Masa tayi. D'aki ya shiga a zatonsa ta koma d'akin ne Amma ya Gama laluben ta bai jita ba Sumayya Kam na zaune duk haushi ya Gama kasheta Jin yanda Al'ameen ke wani sake baki Yana Hira da Yar banzar bazawaran (Kai Sumayya harda zagi) Ji kawai tayi Al'ameen ya rungume ta a zaune da take "Menene"tace tana zame jikinta a nasa "Me yasa kika ki amsa mini bayan kinji Ina kiranki,yace Yana Kara lafewa a bayanta "Oho Kuma ka sakeni" Meye Kuma nayi Miki haka hajiya "Bansani ba nika sakeni nace maka" Habba bakutuwa "Ka sakeni fa" Green sum...... Sumayya Bata bari ya karasa ba kawai ta dasa Masa hakoranta a hannunsa D'aya zagayo dashi Kan kirjinta Washhhh Allah na yatsata,yace Yana yarfa yatsar don harga Allah da gaske Sumayya ta cijesa,ni Kika ciza? "Eh din kuma,ka sakeni nikam" Wai menene Kam? "Bansani ba" Karki sani Kuma kamila zata fara zuwa make-up gobe nace Mata na, Amince kamar yanda Kika Bata umurni,yace ya na son gane dalilin fushin nata Koh saboda kamilane, don shidai lfy suka rabu kafun ta fitoh waje "Bazan Yi ba ai ba'a dole karta kuskura tazo mini gida don kurinta zanyi" Kishi kike da ita? "Akan me zanyi kishi da ita kuma" samayya tace tana Jin bugun zuciyarta na karuwa Akan mijinki,Mana "Ina mijin yake" Au bakisan inda yake ba? "Eh ban sani ba saika sanar dani" Jin abinda Sumayya tace yasa Al'ameen zabura da karfi ya fizgota jikinsa ya juyarda ita suna fuskantar juna,kikace in sanar dake Ina mijin yake? Sumayya ni kike fadawa wannan magana saboda Ina miskini Kuma kina ciyar dani,ya fada ransa a matukar bace Sosai Sumayya ta razana harga Allah batasan maganar ta fita ba Sam ita Karan kanta bazatace ga abinda ya harzukata ba yanzun yanzun nan Tambayar ki nake Sumayya saboda kina ciyardani? Koh saboda bana gani shine kike wulakantamin aure? Sosai ta Shiga rud'ani Bata d'auka Al'ameen da ta sani yanada irin wannan fuskar ba"Kayi hakuri"tace tana zame damtsen ta a hannunsa D'aya damke Kala baice ba mikewa kawai yayi ya d'auke sandarsa da ciny'ayyen takalmin sa yafita Bayan fitar Al'ameen sosai Sumayya ta Shiga Dana sani,tabbas magana zarar budu inta fitoh Bata komawa,da tasan haka zai Bata Masa Rai da Bata fara ba Mikewa tayi ta Shiga d'aki ta kwanta sosai zuciyarta ke Mata zafi Bangaren Al'ameen Kam bayan fitarsa gida Tashan kayan marmari ya nufa, duk yanda yaso ya samu bashin Kaya abin ya gagara haka yayita yawo Amma shuru Bai samu kome ba ,tabbas irin wannan yake gudu Sam bayason mace ace ita ke ciyar da miji,Sam maganar Sumayya Ada Baya Masa ciwo Amma yanzun yaji wani irin ciwo akan maganar sosai,sanann ya Mata hakan ne don ta kiyaye gaba in zata Masa magana ta ringa taunawa,ya fahimci kishine kawai ke d'awainiya da ita Jin ana Kiran azahar yasa Sumayya mikewa sallah tayi ta d'aura shinkafa da wake,zubawa tayi a flasks don itakam Sam bazata iyyacin kome ba yanda take Jin tsananin damuwan nan,gashi batasan Ina Al'ameen ya Shiga ba,har yanzun Bai dawo ba Har yamma Al'ameen shuru Bai dawo ba duk inda hankali Sumayya yake ya Tashi sosai ta Shiga damuwa matar Bashir data ma alkawarin lalle day uku tana Aiko yaro karshe ma Sumayya tace yaron yace Mata bazata samu zuwa ba "ya Allah ka dawo mini dashi lfy"tace tana zabga tagumi Sai bayan Isha'i Daya idar da Sallah Aljuhunsa ba kome yanda ya fita haka ya dawo Koh abinci Bai Karaci ba bayan na karyawa,da sallama ya shigo d'aki Sumayya dake cikin dogon tunani tana zaune akan sallaya Koh hijab Bata cireba , da sauri ta amsa"waalaikumu salam yayan khadija lfy kuwa baka dawo ba sai yanzun"tace tana isowa garesa Uhmm sai yanzun, kawai yace Mata Yana k'wabe rigansa,jallabiya ya d'auko a cikin kayansa ya fitoh waje Bai Kara Mata magana ba Baki a sake Sumayya ta Bisa da kallon mamaki harya fita,ta koma ta zube a jikin kujera hawaye na cika Mata ido,ta Shiga uku sauran hope natan Daya saura shine shima yake kokarin juya Mata baya Wai meke faruwa da itane me yasa duk Wanda zai sota daga baya sai ya kaurace Mata,kuka kawai ta sake "nikam na Shiga uku"tace tana cigaba da kukanta, Al'ameen Bai taba fushi da itaba sai yau menene Bata Masa ba Abaya Bai taba fushi ba sai yau daya ga kamila. Al'ameen Kam wanka ya Shiga Yana fita yaji muryar Sumayya kasa kasa tana kuka da sauri ya aje kayanda ya cire,Wanda yaso wankewa Amma baida omo. D'akin ya shiga Amma saiya maze ya kwanta akan kujera Bai kulata ba Sumayya Kam Jin yanda Koh damuwa baiyi da kukan da yaji take ba yasa a hankali cikin muryar kuka tace"yayan khadija ga abincin ka"ta fada tana mikewa ta dauko a saman freezer Na gode Amma bazanci ba yace, ba tare da ya Koh motsa a inda yake ba Kuka kawai Sumayya ta sake kamar ana yankata"nikam na shiga uku tunfa safe banci kome ba bayan karyawa saboda Ina jiranka ka dawo Amma shine ka dawo kace bazaka ci ba" Na hanaki cine ai ban hanaki ba kici Mana ni indai nace bazanci ba "Wayyo Allah na ni Sumayya Yaya zanyi da Raina ne" Da na Miki me? "Kaci abincin toh kaji" Ah ah naci ai "Waya baka kudi ka saya" Ai Ina da sana'a Koh? "Nidai don Allah Kayi hakuri kaci kaji" A matsayina nawa Kika damu da sai naci abincin ki?ya tambaye ta "A matsayinka na"...... Sai Kuma tayi shuru tana kallonsa Uhmm ,kawai yace Yana lumshe idanunsa so yake ya kitsema wannan baiwar Allah Koh Amafarkine Yana son kallonta, tunda ya makance Bai tanajin yanason kallo ba irin haduwarsa da Sumayya sosai yakeson ganinta da idanunsa "Wa.....i mi...jin..a.."tace cikin eeii eiiina Waine ma kenan? "Mi..ji...na" Sumayya!ya Kira sunanta "Na'am" Meya Bata Miki Rai d'azun? "Babu" Akwai Kam? "Babu"tace hawaye nabin kumatunta Nine Koh kamila?ya Kara tambayarta "Koh D'aya" Ki fadamin gaskiya wannan shine kad'ai zaisa na hakuri. "Kaine" Me nayi Miki har zakina fad'amin magana irin Wannan "Toh ba Kaine ba" Nine me? Kaketa Mata dariya harda wani.....sai kuma tayi shuru Jin subutar baki da tayi Shikam murmushi ne ya subuce Masa hade da wani irin farin ciki tunda Sumayya na kishinsa,Kuma duk inda akwai kishi akwai alamun so, sai Kuma akace ki gaggaya min magana? "Kaye hakuri don Allah"tace tana mikewa a hankali ta matso garesa fadawa tayi kansa da karfi ta sake kuka Rumtsa idanunsa yayi Jin saukan hawayen ta a kirjinsa tamkar ruwan guduma haka yajisu, Sumayya!ya Kira sunan ta Yana Mai Kara matseta a jikinsa "Na'am"ta amsa Masa hade da cusa kanta a kirjinsa ji take Kamar numfashin ta zai d'auke Sumayya na hakura Amma karki sake mini Wasa da aure kinji banaso. "Wallahih bazan sake ba" Allah yasa,yace Yana shafa rigan jikinta Sumayya wannan ba kayanda kikasa da safe ba? "Shine" Ta basa Amsa Miya hanaki wanka? sai tsami kike ma,ya fada hade da shafa Mata baya "Damuwa ne ya hanani,Kuma ni bana tsami" Bagashi ba sai tsami kike, yace Yan sunsunar wuyanta,dake tsananin kamshin Turaren ta "Zakaci abincin na baka"?ta tambaye sa cikin damuwa A koshe nake ki bare sai da safe sai naci. "Nidai ban yarda ba wallahih Koh kaci saikaci nawa" Toh zanci,kije kiye wanka ki wanke tsami kisa Kaya "Bayan na Gama sai muyi me"? Saina karbi hakkina,ya Bata Amsa shima "Niii..... niii.. Babu ruwana,abinci nake nufi" Ai kema abinci ne,ya Bata Amsa "Wacece kamila"? Uhmmm abinda ya hanaki sukuni kenan? "Nidai ka fad'amin kawai malam" Toh malama bakutuwa kije kiyi wanka sai kizo kici abinci sai mu k'wanta da safe saina fad'a miki,. "Har gobe kuma"tace tana hada fuska Eh na gaji bacci nakeji yanzun yace Yana cire Mata riga "Bacci Kuma kake kwabeni"? wanka zakiy i,ya Bata Amsa hade da karasa cire Mata rigan Wanka Sumayya ta Shiga tana fitowa lokacin karfe 8:00 dai dai,
Chapter 34 · 0% Book details