Sashe 58
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Page5 Akan ibada don naga d'an changen rayuwa da kuka samu haryasa kuna sanyi da ibadan koh, toh bari kuji irin wannan daman makiyan ku suke jira sumu ku mai gabaki d'aya in kukayi sake da ibadah toh tabbas zasuga bayan ku sarkin yawa yafi sarkin karfi, watan da muka shiga wata ne mai Albarka ni'ima da falala ku dukufa wajen neman tsari da kariya a wajen mahaliccin mu. Sake baki sumayya tayi tana kallon matar da bata santa bama gashi dare ne ba nepa bare ta mata kallon sap"malama wani irin magana ne haka sannan suwaye makiyan mu"? Baki bukatar ji nidai na fad'a miki tace tana fita a kofar Sumayya kam kamar doluwa haka ta kuma sai bin hanyar da matar ta fita kawai take tana Al'ajabi"yayan khadija kaji wani magana kuwa"? Uhmm sumayya maganar matan nan koh bamu gaskata ba, Amma tunda ibadah tace toh mu dage koh ba makiyi Addu'a makamin mumini ne "Gaskiya ne" sumayya tace duk jikinta yayi sanyi sosai abincin ma kasa cigaba daci tayi Al'ameen dake cin abinci tsayawa yayi jin sumayya shuru hannu yasa ya tabata sumayya yadai? "Uhmm babu kome kawai dai ina mamaki ne" Mamakin me kuma? inna matan nan ne ai ba abin mamaki bane don duniya da fad'i kika san menene Alakarta da su kedai mu rike ibadah hannu bibiyu insha Allah ba Abinda zamu gani sai Alkhari kici Abinci pls? Toh tace tana cigaba dacin abincin"yayan khadija me zan dafa mana na sahur"? Me kike so? "Uhmm aikai na tambaya koh"? Nima saina tambaye ki "Toh ai mata ke tambayar miji abinda za'a dafa" Au yanzun kam an yarda ni mijine kenan? "Oho dai nikam ka fad'a mini abinda zan dafa so nake mu kwanta da wuri samun mu tashi da wuri" Ki mana tuwon shinkafa miyan shuwaka "Nama koh kifi"? Duk wanda ya dace ki saka "Ok" kawai tace tana tashi kitchen ta shiga ta barshi zaune akan taburma Girki sumayya tayi sai kusan 10:30 ta kammala aikin girki juyewa tayi a kula takai d'aki tayi tatan kamu da khadija ta karbo mata a inji tana gamawa tattara taburman tayi, ta rufe kofar su zuwa lokacin Al'ameen yayi bacci tuntuni itama kwanciyar tayi bata tashesa ba don bacc i takeji itama Misalin karfe 1:30am Al'ameen ya farka jin sumayya ajikinsa yasa sa tata bata, sumayya!! sumayya!! "Menene"? Ki tashi mana "asuba yayi ne"? Baiyi ba sallah zamuyi tashi maza kinji "Uhum"tace tana mikewa sauka tayi akan gadon ta kamo hannunsa suka fitoh waje bayan ta kunna hasken wayan ta Alwala sukayi suka tada sallah Sai karfe uku suka sallame sosai suka dukufa suna Addu'an neman tsari wajen mahallincin mu da neman gafaran sa 3:41 sumayya ta d'auko musu tuwon ta bude da zafin sa kamar yanzun akayi zuba musu tayi sukayi sahur basu koma bacci ba sai data cika ruwan randa a laida fari ta d'add'aure ta cika firij nata bayan asuba suka koma bacci Dayake Cikin Ramadan ba'acika sayan kaya da safe ba sai yamma yasa Al'ameen yabiye wa sumayya suka cigaba da bacci basu suka tashi ba sai kusan 9 Al'ameen ya tafi masallaci tafsiri sumayya ma islamiyar unguwan taje wata babbar malama ke tafsir wa matan aure a ciki sai bayan Azahar Al'ameen ya fita shago, sumayya kam sallah tayi ta shiga kitchen abinci ta dafa dankali ne da kwai ta soya sai ruwan tie ta musu macaroni da miya duk ta zuzzuba a kula ta zuba wasu goggo ma a manyan kula guda biyu, kiran yaro tayi ya kira mata khadija bayan ta dama kunu cikin bokatin penti fari babba, wanka ta shiga kafun ta fitoh saiga khadija ta shigo bayan sun gaisa ta bata boket in da cups na roba wanda ta saya jiya ta had'a mata takai masallaci sadaka sai ruwan da tasa da asuba a firij sunyi guda shima boket ta cika ta d'aurawa Almajiri yabi khadija Rarra bawa khadija tayi a masallaci sosai jama'a ke sawa abin Albarka don koh masu kudin unguwan basa kawo kome a azumi sai talakawa ke kokarin ciyar da masu azumi (Allah ya kyauta) Bayan khadija ta dawo da bokata yen, kulan abinci sumayya ta bata ta kaima goggo suyi bud'a baki Al'ameen ne ya had'a kankana da dabino sai sweet milo, yasa a laida biyu ya rike a hannunsa barin shagari yayi a shago hade da basa kudi yasai abin bud'a baki shima Gidan goggo ya wuce ya bata laida d'aya ya kamo hanyar gida Tun akan hanya ake ta masa godiyan kunu da kankara sosai yayi mamaki wani kunu kuma amma baiyi magana ba amsa musu yayi ya shiga gida daidai lokacin aka kira sallan mangari ba Assalamu Alaikum "Wa'alaikumu salam" Jin bakin sumayya cike da abinci ta amsa sallamar yasa sa da mamaki yace toh yau koh jira babu hajiya har an kai loma? "Ai a azumin nan ba jira kaji in gaya maka ana kiran sallah sai ci yaushe zan jiraka kuma" Uhmm yayi kyau yace yana zama akan dakalin da take, mika mata laidan yayi ganin yau koh karba batayi ba sai jin karan shukali kawai yake Amsa tayi ta bude dabino ne guda biyar ta damka masa a hannu sai ruwan shayi a kofi Karba yayi ya bude baki da addu'a bayan yaci dabinon ruwa ya kurba kawai yayi Alwala ya tafi masallaci Sumayya kam sai da ciki ya d'auka kafun ta zakud'a itama sallar tayi bayan ya dawo masallaci shima yaci nasa Abincin sauran kayan marmari da ya rage ta saka a firij Da misalin karfe 11 bayan ta gama aikace aikacen girkin asuba yake tambayar ta akan kankara da kunu "Yanzun don zanyi aikin lada saina fad'a maka yayan khadija watan azumi ne fa" Allah ya karbi ibadun mu "Ameen, FATAN MU(next novel)kenan insha Allah" Ta bangaren kamila Alhamdulilah jiki yayi sauki sosai harma an sallame ta sai dai fa fatar hannu kam ba kamar nada ba Yau dai gidan kawarta ta nufa Assalamu Alaikum Wa'alaikumu salam wanake gani anan koh dai idanuna ne kemin gezo lallai kamila duniya ashe ana iyya tunawa damu Ke matsalar ki kenan Harira daga mutum yazo gunki koh wajen zama baki bani ba kin kama mini korafi Ai dole na miki kamila tun auren ki na sake saki a idanu na? koh wayarki na daina samu sai dai inji a gari kinzo kin koma yar buru uba har zaki ce ban baki mazauni ba Yanzun dai kiyi hakuri ki zauna wata magana ce ta kawo ni Aikam sai ta kawo ki badai kika kawo kanki ba Kee habba don Allah jarabar ta isa haka Naji meke tafe dake kamila Yauwa zancen dai na muhammad ne Wani muhammad in? Ki jiki da wani banzan tambaya muhammad nawa nake dashine wai Nidai nasan tsohon mijinki dai ba muhammad bane MAKAHO... Kwal uba yanzun kuma tsohon zuma aka koma Ai daman tafi magani, ke Harira kinsan meya kashe min aure? Ah ah Toh rashin biyamin bukata ne bayayi, don bana gamsuwa shiyasa na kashe aure na don ni yanzun duniya kaf in dai zan samu namiji gwarzo ba ruwa na da talauci koh kyau kin gannin nan don nabisu banga da kyau ba Amma ke dai kamila akwai shirme kece miki akai shi Al'ameen in jarabebbe ne kamar ki? Hhh habba Harira ido fa ba mudu bane amma yasan kema Hhhh shegiya ta faso gari, ta karasa maganar da bawa kamila hannu suka tafa, toh yanzun me kike so ayi ne Yauwa MAKAHO fa aure yayi kuma wata yar iska ya aura family shugaba shugaba fa kikace? Eh nima nayi mamaki auren nan yar iska in kika ganta sai gaban ki ya fad'i tsabar kyau Kema dai kamila aikin san zuriyan gidan daman kyawawane sai dai na wani yafi na wani Gaskiya ne in gaya miki wai dana gama bibiyar muhammad na tataro kome nasa na samu cikeken bayani akansu shinefa naje da sunan koyan kwalliya wajen ta yar iska kinga duka da suka mini karshe ma acid inda zani makaranta dashi zamu shiga lab zuciya ya ebeni na d'auko zan watsa ma yar banza kawai in gaya miki abin mamaki muhammad ya zabi matar sa akaina da kansa ya hankad'a ni har acid ya zube a hannuna, ta karasa maganar da nunawa Harira hannun Cap wani mataki Dad ya d'auka akansa? Ai ban fad'a masa gaskiya ba cewa nayi ita ta zuba mini Aiko kinyi wauta Ai ma abin ba inda yaje don bata kamu ba Kema ai kinsan bazata kamun ba, yanzun dai me kike so ayi Yauwa Harira wajen malaman nan naki nake so ki kaini akan maganar nan Hhhh yar iska ba kullum fad'a kike mini akan malamai ba angaya miki ana zama hakane ai kikace zaki zauna haka toh bone ya sameki Gaskiya kam don akansa babu abinda bazan aikata ba ke so nake inga koh kaunar ganin sumayya baya so yaji kaf duniya ba wanda yaki jini irin ta, ba wanda yake so irina Shegiya ba kome tashima kiga bara na d'auko mayafi muyi gaba kinsan har kauyen mutum biyu ne in bamu tafi yanzun ba sai kuma gobe saboda hanya ba kyau ga dare Amma harira haka zaki tafi naga mai gidan baya nan gashi yara daga su sai yar aiki Kee waya gaya miki sai na jira sa ai wallahi sai abinda nace Uhmm kai nima fa za'ayi tafiyar nan naku dani Amma dai kin taho da kudi kam koh ? Karkiji kome akwai kudi akwai mota sai ki tukamu tunda ke kika san hanya Ok muje haka kamila da Harira suka d'auki hanyar mutum biyu wajen boka a watan azumi koh tsoron Allah babu Sai la'asar suka isa cikin mutum biyu dole tasa suka faka motar su a bakin titi suka hau machine mai kafa biyu zuwa ciki cikin kauyen bayan sun iso ma sai da suka tsallake ruwa Wani dutse ne baki kiren hayaki na fita akai tunda suka nufo wajen wani irin wari ne yake bugan hancin su da sauri kamila ta tushe hancin ta Cikin gaggawa Harira ta buge hannun, kamila ke kamila ki rufa mana asiri kar muje ciki a haka kin tushe hanci wani irin iskanci ne wannan? Amma Harira baki jin wari da doyi na tashi