Sashe 80
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
uku kome uku uku aka mata hada kayan kitchen, kawayen ta fa sun samu abin yi, sai dariya suke suna yad'a mata bakar magana, especially wa'inda sukayi aure, sumayya a ranan tayi kuka har saida tayi Addu'a Allah ya d'auki ranta,saida wata yar uwar su na gembu ta mata wa'azi kar bacin rai yasa tayi sabo. Ai bata tashi ganin bacin rai ba, saida motar su tayi fakin a kofar gidan Adara, wani gidane irin na talakawa mai jan kasa sai kofar gidan da babu kofa, lulubi aka mata suka shiga gidan, amma kamar ba gidan da za'a kawowa amarya ba, babu wanda ya tarbesu asalima kowa harkar gabansa yake kamar ba'aga zuwansu ba, tambayar kofar amarya sukayi aka nuna musu, wani samurmurin d'aki koh kewaye sa ba'ayi ba, d'akine d'aya kankani wani rubebe dashi, ihu sumayya tasa ta tsunguna agun tana sakin kuka itakam tata ta sameta. Ga auren MAKAHO ga talauci dame zataji, Allah ya isa ta farama su babuji, tana sun cuceta, a hakan dai aka wuce d'akin, yar uwar dada ce ta tura rubebben kofar da koh sakata bazai zauna ba tsaban rubewarsa, suna bude dakin ba laifi a wanke yake sai dai babu kome sai cinyayen taburma da ghana must go na kaya kad'ai a d'akin, su karan kansu masu jeren ma sun rasa ta ina zasu fara, wanda aka kawowa set uku shine aka samu d'aki d'aya karami. Da gudu sumayya ta b'anbara ta bar gidan, kawai su dada na zaune sukaga amarya ta faso da gudu ta dawo gida"wallahi bazan xauna agidan shan ba"wannan shine abinda sumayya tace, kuma ba wanda yayi maagana. Wannan hajiya yar uwar dada ita tayi waya aka kira mata kafinta, a take yaxo shida abokan aikinsa uku,suka buga musu kofar daki, a ka cire tsohon dayake yammane, wasu daga cikin yan uwan, kwana sukayi washe gari kafintoti suka gama aikinsu, sun kewaye kofar da falange an mata band''aki a kofarta, an saka silif da kitchen da baranda, Amma fa kaya bai d'auka ba koh set d'aya basu samu shigaba, haka aka juya da sauran kayan. Abie da kansa a ranan da , dadare ya dawo da sumayya bisa umurnin dada,haka aka watse aka bar sumayya da halinta, wasu sun mata wa'azi wasu kam magana suka gaggaya mata. Sumayya tunda suka watse aka barta kuka take, gashi dare ne tana zaune akan gadon tana kuka cikin bakin cikin wannan al'amari, sai a ranan wani irin kewar mahaifiyarta ya kamata da ace mamarta na tare da ita da abubuwa zasu mata sauki. Duke take tana kuka baji ba gani wai itace da aure a irin wannan gida................. Tas sumayya ta sanar da Ammar duk irin wahalar da tasha, da burinda taci na ganin tayi wa muhammad wulakanci, harsai yaji a jikinsa kafun tanemi sakin ta, amma saboda kyawawan halinsa da hakurinsa don babu abinda sumayya bata masa ba, amma bai taba nunawa koh a fuska ba, bai taba riketa , da wani manufa a ransa ba, kullum kokarin faranta mata yake, wannan sune makamin da yayi tasiri wajen mallakar zuciyar sumayya, taji zata rayu dashi a haka, sannan ta d'auki auren su da Al'ameeen isharane Allah ya nuna mata, akan halinta, kuma ta karbe kaddarar ta, tazauna da mijinta.... cigaban labari......... "Sannan yau suce wai na rabu dashi akan me"? D'aga ido Ammar yayi ya kalli sumayya da khadija dake kuka, lokaci guda, sumayya!!ya kira sunan ta. "Na'am" Kukan ya isa haka abinda nakeso dake shine ki d'auki duk abinda ya faru a matsayin jarabawa, kamar yanda kikace, naji duk abinda iyayen ki suka miki, Amma ke me kika fahimta akan auren ku da muhammad, da gaske bashi yace yana sonki ba? Gyara xama sumayya tayi ta zayyana masa labarin muhammad, da irin wahalhalun da yasha. Tabbas Ammar ya tausayawa rayuwar su muhammad, kuma a cikin labarin sa da sumayya ya auna wasu abubuwa da dama akai, sai kuma abu na biyu, sumayya kina nufin mamar ki sunan ta hafsa sannan yar maiduguri ce? "Eh Amma bansan a ina take a maidugurin ba" Amma naji mahaifin ki yace zai kaiki wannan karon. "Ni yanzun bata maiduguri nake ba, ta mijina nake" Sumayya kiyi hakuri ki koma gidan naku, tunda naga iyayenki zama a gidan Adara ne basaso kiyi, in Allah yasa Al'ameen ya dawo, kinga shikenan sai ki dawo d'akinki, in ma basason zaman gidan ne, nizan nema muku wani gidan saiku koma, amma a halinda kike cikin nan ya kamata ki kula da kanki, juna biyu ne dake ga dp ki na hawa, koh kinaso ki rasa babyn nakune? "Ah ah yaya Ammar"sumayya ta amsa masa. Yauwa koh kefa kiyi hakuri ki koma gidan kinji?insha Allah auren ki da muhammad bazai mutu ba. Kuka sukaji da karfi a gefen su, khadija ce ke kuka. Kee lafiya menene haka? Kallonsa khadija tayi da haushi jin tambayar da ya mata, toh ba kai bane kake cewa Aunty ta tafi, toh ni kuma in zauna dawa? Da goggo mana zaki zauna, ba za'a bude makaranta gobe monday ba?saiki cigaba da zuwa kafun yayan ki ya dawo. Kuka khadija ta sake, shikenan aunty yanzun tafiya zakiyi ki barni. Toh koh zaki bita ne gidan nasu?koh taki bin umurnin iyayen ta akanki?khadija iyaye fa ba wasa bane?ammar yace cikin haushi Shuru ta masa, sai ga likita yazo ya basu sallama, don sumayyar ba wani jin jiki tayi ba, ruwan da aka saka mata ya kare. Suna Fitowa taga Ahlin gidansu tim a cike a haraban asibitin, kala batace musu ba Tana bin Ammar a baya, ga khadija a gefe. Tashi sukayi suka bisu a baya har packing space, sumayya motar Ammar tayi niyar shiga Amma dada tayi tsalle ta dire akan ba inda sumayya zata shiga, sai motar gidansu. "Kinsan Allah dada in kika matsamin saina fasa bin naku naga ta tsiya" sumayya tace. Yi hakuri kawalli jeki shiga na Abokin mijin naki. Shiga motar sumayya tayi ta kalli khadija dake tafiya a hankali kamar kwai ya fashe mata a ciki, daga ka ganta kasan tana cikin matsanan cin damuwa, "ya Ammar ka fad'a musu bazan koma yau ba sai gobe, sutura driver yazo ya d'auke ni inna shirya kayana" ba musu Ammar ya fita a motar daidai lokacin khadija ke kokarin shiga, yaje ya sanar dasu basu wani d'aga hankalisu ba sukace goben insha Allah abie da kansa zaizo d'aukar ta, in kayan sawane ma?ta bari kawai za'a saya mata sabbi. Amma sumayya tace ita sai ta kwana washe gari zata koma gidan su. Bayan isar su sumayya gida, Ammar tafiya yayi, khadija ta kalli Auntin ta, yanzun Aunty da gaske zaki tafi ki barni?shikenan ni babu yaya babu ke banida kowa yanzun sai goggo? "Khadija baxan barki ba koh babu yayan ki Zan kula dake, guduwa zamuyi daga jalingo, gobe goben nan da asuba zamu bar gari.............. Ruqeenjalal *MATAR MAKAHO*