← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 104

Sashe 22

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Jin tausayin baiwar Allah nan D'aki na shiga na barta tana kuka akwatina na bude Kaya na d'auka Atamfa da les masu azaban kyau a dinke sai Turare na d'auka guda D'aya na fitoh a d'akin dasu a hannuna "Khadija rike kayan nan Naga kamar akwai tailoli a tsallaken titi ki Kai musu wa'innan kayan su rage Miki yayi daidan ki yanzun in Kika fita, wannan Turare Kuma kasuwa nakeso ki Kai shagunan masu Turare Koh zasu Saya kudin sa 20k ne Amma Koh 10k Kika samu Koh kasa dashe ki karba kawai" Aunty ba Yaya yace ki daina Saida kayanki ba? "Khadija Zan zauna da yunwa ne Ina da abinda Zan tsayar naci a cikina sai na zauna" Gaskiya ne Aunty Amma fa Yan kasuwa bazasu Saya ba don yanzun Suma tsoron sayan kayan hannu suke karsu Saya na sata,sai dai akwai wata Mata dillaliya ta bayan kasuwa sai na Kai Mata don ance itakam Koh kayan satane Saya take don Yar rikici ce sosai "Yauwa khadija Allah yasa ta Saya wannan kayan in kin fita ki fara kaisu shagunan dinki" Aunty wazaki bawa kayan Kuma ai Naga daidan kine naji kince a maidashe daidai na? "Ina ruwan Ki,nidai tashi kije mini aika na, sannan in ta Saya Turaren ki shiga kasuwa ki sai Gam bak'i Mai kyau ki hada da Turaren lalle,sajan,tsamiyan kanti, ki sai bakin lalle guda biyu shima" Aunty lalle zakije ne? "Kai Khadi ja banson tambaya ki sai mini kayan Miya duka,in kin dawo ki biya tailan kudinsa ki karbi kayan Saiki saimin doya soyayye a bakin titi na karya" Toh Aunty tace ta karbi kayan tasa a laida ta fita D'aki na shiga Ina ta tunanin halin rayuwa da khadija ke ciki Sai karfe 10 khadija ta dawo kayan na bubbude na Bata ta gwada Aiko yayi Mata daidai jikinta sosai kayan ya karbe ta,doyan na bude Mana mukaci tare Kam in na manna a tire na kwaba Jan lalle, "khadija zoki zauna na Miki lalle"nace Mata Ina zama akan dakali Aunty Daman ni Zaki ma lallen ne har Kika Saida Turaren ki Mai tsada a naira 5k? "Khadija bazan d'auki wulakanci ba Sam insha Allah yau saikin fi Amaryar kyau bama kawayen ba" Daman kin iyya lalle ne Aunty?ta fada tana zama "Sosai ma khadija ai lokacin da nake primary school innaje makaranta sai nayita zana flower lalle a takanda na Inna dawo gida sai ummie na tace zata buge ni sai abie ya k'waceni yace bazata bugeni ba ai batasan Koh baiwar da Allah ya mini ba kenan, sai ya sai mini takkadar lalle daban duk lokacin da zanyi Zane saina dawo makaranta sai ya bani takardar na zana, lokacin da na Gama primary sai ya sai k'wallon dayes ya baiwa Mai aikin mu ta dafa mini da lalle,sai nayi mole na zuba a ciki,abie ke saimin hydrogen Ina ma yaran gidan mu lalle harda yaran makwanta, harna girma Ina lalle duk yaran gidan mu da aka aurar Mata Ninake musu lallen aure da make-up haka kawaye na da Yan unguwan mu sosai nake Alfahari da lalle khadija"nace Ina manna Mata Gam a gafa Kenan Aunty kina sana'an lalle da kwalliya? "Ban taba yin lalle kudi ba Koh make-up khadija don ba abinda na nema na rasa a rayuwa a lokacin" Allah sarki, tace Lalle na tsarawa khadija sosai bak'i da ja sai bayan azahar Muka Gama, tunda nake da khadija ban taba ganin farin cikin Dana gani a lokacin da na Gama Mata lalle ba bini bini saita duba lallen tayi murmushi "Wai nikam khadija baki taba lalle bane" Aunty Kenan Koh a sallah bana lallle in Kinga nayi lalle toh gaggo ne ta mini yabe "Toh yaukam kinyi design na flower"nace Ina mikewa sallah Mukayi kafun Muka girka abincin Rana har lokacin yayan Khadija Bai dawo ba, Sai biyu da rabi na Gama abinci zuba Mana nayi mukaci har lokacin fuskar khadija na d'auke da murmushi ***Nima sai naji Ina cikin farin ciki ganinta tana walwala "Khadija ga abincin yayanki kikai Masa" Toh Aunty ta d'auki kulan tana kukarin fita,"yauwa khadija in kinje ki dawo da wure samun mu fara make-up in da wure" Toh Aunty nagode,tace tana fita,cikin farin ciki duk Wanda ya ganta yau yasan Bata da wata damuwa Tun daga nesa ta hango yayanta a zaune g'wanin tausayi sai zufa yake................ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara* *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* *Na tsunguno(habil)* *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* ) *Turaren turara jiki after birth* , *Na d'aki(halud Al'oud)* *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* Contact them vie 08028827241 or 09033791049 *MATAR MAKAHO*
Chapter 22 · 0% Book details