← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 104

Sashe 41

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aishan ADARA ne kwance Bata motse, cikin sauri Al'ameen ya Isa gareta yana kuka,don zuwa yanzun sun fara sanin ciwon kansu daga shi har Salim in,rungumar mahaifiyar sa yayi Yana kuka,don Allah Mami karki tafi ki barmu mami karki tafi ki barmu wayyo mamin mu yace Yana fashewa da kuka Salim Kam tsabar tashin hankali ciwon sa ne ya tashi,da sauri likitoti suka Kira baban Aisha dake waje a zaune yazo ya fitar da Al'ameen shi Kuma Salim Nurse suka d'aukesa zuwa wani gadon. Sumayya dake kwance a kirjin Al'ameen kukane ya k'wace Mata hannu tasa ta Kara rungumar sa tana kuka,shikam gabaki d'aya jijiyoyin kansa sun mike sosai, kallo D'aya mutum zai Masa yasan ran maza ya tsogalu. Kafun ya Kara bude baki, ji kawai sukaye kuka na tashi a bakin kofar d'akin su da sauri Sumayya ta mike hade da kamo hannun Al'ameen suka fitoh wajen tare Khadija ce duke tana kuka fuskarta harta kumbura Alamu dai ta Dade tanayinsa kasa kasa sune dai basuji ba. Yaya Daman gidan ADARA ba dangin mahaifin mu bane? Shiyasa suka nuna Mana launin fata,khadija ke tambayar yayan ta Ah ah khadija ba saboda haka bane suke wulakanta mu dama can haka kaddarar Rayuwar mu take, kishare hawayen ki maza ki tafi gida Ni wallahih Yaya inason Jin karashin labarin mu don Allah Yaya kaga ba Wanda ya taba ban Tarihin iyayen mu kullum na tambaye ka Koh Goggo sai kuce mu Marayu ne. Al'ameen nada niyar magana Sumayya ta regasa"gaskiya ne khadija tayi girman da zata San abubuwanda suka shafeta especially irin wa'innan Tarihin" Shikenan naji ana Kiran azahar bara nayi sallah Kuma kuyi Inna dawo saimu d'aura daga inda na tsaya,yace Yana Mai laluben buta Da sauri Sumayya ta nufi butar dake zaune a Gefen baranda ta Mika Masa. Alwala sukayi Sumayya kudi ta baiwa Al'ameen 1k in zai shigo gida yasai musu doya soyayye a bakin titi na 500 Ba musu ya karba ya fita Bayan an idar da sallah Al'ameen doya yasai musu suka ci su ukun, duka a plate d'aya bayan Sumayya ta matsa musu don har lokacin khadija kuka take Kamar yau Abubuwan da suka shige ya faru. Khadija inkin San kuka zakiyi toh Zaki bar gidan nan Banga amfanin kina kuka Kuma kice na cigaba da baki labarin ba kije ki samu wani damuwanne Koh me? Al'ameen ya fad'a ransa a bace,don shima dauriyane kawai "Don Allah yayan khadija kayi Hakuri mutuwar iyaye Koh shikara d'arine zafine da shi" Kayi hakuri Yaya,khadija tace tana share hawayen ta Dukansu Basuci wani abin kirki ba Al'ameen Kam doya yanka biyu kawai yace khadija Kam ma tanaci Amai tayi saboda yanda take ajiyar zuciya Bayan sun wanke hannunsu Al'ameen ya cigaba........ Bayan mutuwar Aisha Alhaji ubangari yaso d'aukar su Al'ameen ya rike, Amma baban Aisha ya murza ido yace ba dashi ba Koh kudi ubangari ya baiwa su Al'ameen sai an mayar Masa da kayansa sosai abubuwa suka ma ubangari yawa don yanzun Koh fita zainab Bata iyyawa,tana fita ana nunata . Khadija Kam, kanwar Aisha aka bawa wance ta h Bata jima da haihuwa ba ta shayar da khadija, Amma khadija Taki karban nono Sam sai madara,ganin Amina Bata taba haihuwa ba yasa baba karban khadija ya Baiwa Amina Amana. Al'ameen sunyi matukar kewar iyayensu Wanda Salim yafi saka abin a ransa shiyasa kullum cikin ciwo yake don yanzun dai Al'ameen wani abokin babane ya ajesa a shagonsa Yana sayar Masa da kayan marmari duk Rana Yana biyansa,da wannan yake Tarawa su had'a da baba akai Salim asibiti Duk da wannan d'awainiyar Salim Bai hanasu karatu ba a hakan Alameda yake zuwa makarantan gwannati Dayake lokacin duniya sanyi kalau ba kamar yanzun ba da ake kashiwa makarantan gwannati kudi. Relationship insu da kamila ba abinda ya ragu kullum saiya rakata gida kafun ya nufi unguwan su sosai Abu kamar Wasa shakuwarsu ta Kara karfin sosai saidai kamila Bata taba zuwa unguwan dasu Al'ameen suka koma ba shine dai Mai zuwa gunta, Ubangari Kam zaman jalingo ya gagaresa don lafiyarsa Dana zainab sai a hankali don yanzun saita kwana ta wuni Bata cewa kome makarantar ma yanzun Bata zuwa sosai rayuwa ta musu kunci,ganin Halinda suke ciki, yasa matar ubangari Kiran Yan uwansa ta sanar dasu abinda ke faruwa, Aiko a yanda suka tarar da ubangari da zainab don har an dakatar dashi agun aiki ganin Halinda yake ciki yasa Yan uwansa Saida gidan da suke ciki suka tatttarasu dashi da yaran NASA suka koma garinsu,Daman aikine ya kawo ubangari jalingo, Wannan kenan. Khadija taci gaba da samun kulawa Awajen Amina Alhamdulillah yarinya ta fara girma ga wayo sai daifa Sam Bata da jiki Yar firet da ita kyakkyawa sosai don Kamar ta da Yusuf ne sak shiyasa ita da Al'ameen Koh baka sansuba ka gansu kaga jini d'aya Daman Salim ne baki a cikin su don da Aisha yake Kama. Zaman su a gidan Adara Bai sauya musu hali ba, da yake abin a jininsu yake sanyi Hali da hakuri Amma fa Salim akwai zuciya mundin aka Bata Masa Rai in fa baisamu ya Rama ba saiya kwanta ciwo. Bayan wasu shekaru mahaifin Aisha dai ya kwanta ciwon kafa Wanda Koh kofar gida baya iyya fita Sai an Taimaka masa, don haka Abubuwa sun ma Al'ameen yawa ga kudin maganin Salim ga D'an abinda yake D'an kaima Yar kanwarsa khadija ga zaman shago ga zuwa makaranta ga soyayyar kamila wanda yake jinta har ransa. Haka baban Aisha yayita fama da ciwo har Allah ya d'auke ransa Wanda kafun ya mutu Saida ya jaddada wa yaransa Koh bayan ransa Bai yarda Yusuf da Salim Subar gidan nan Adalilinsu ba d'akinsa da yake ya bar musu halak malak, baya cikin gado, Wannan shine kalmarsa ta karshe Kuma itace sukecin Albarkacinta har yanzun suna cikin gidan ADARA. Bayan mutuwar baban Aisha rayuwa fa ta zamo ma su Al'ameen wani iri Sam a gidan Adara Babu Mai taimaka musu Koda ta abinda zasuci ne,Dole tasa Salim shima ya fad'a Tashar marmari Yana ma wasu jiran Kaya suna biyansa,saisu had'a da kudin Al'ameen su fidda na asibiti su fidda na abinci su fidda Wanda zasu baiwa Amina ta rage d'awainiyar khadija,hakan yasa Al'ameen aje karatunsa don ko yaje makarantan baya fahimtar kome tsabar damuwa, Ganin ya aje karatunsa Salim ma yaki zuwa makaranta ba yanda baiyi dashi ba Amma yake ganin Al'ameen ya matsa Masa yasa sa cewa Al'ameen,Yaya moha Koh naje makaranta asaran kudi zakayi tayi Kaine yafi cancanta Kayi karatu Koh don kanwarmu ta samu rayuwa Mai inganci Jin Amsar da Salim ya basa Saida Hankali Al'ameen ya tashe cikin damuwa yace Masa,salim ban gane ba kana nufin Kai Babu Amfanin karatun nakane, ka sani Koh Kaine Mai rabon Tallafawa Khadijan? Ah ah Yaya Kaine ya dace Kaye karatu don Allah badon niba Yaya ka koma makaranta nikam bazanje ba karatun ya isheni haka ya karasa maganar da kuka Rungumar sa Al'ameen yaye shima sai yaji hawaye nabin fuskarsa don yanzun sosai sukayi wayo girma ya fara zuwa musu Kuma labarin abinda ya faru ya riskesu,sosai suka kullace zainab a ransu Kuma har abada bazasu manta da fuskarta ba. Haka ba yanda Al'ameen ya iyya ya koma makaranta don lokacin ma ya Shiga SSS class yayinda khadija ta Kai shiga primary school da Taimakon Goggo Amina aka sakata Soyayya Kam tsakanin kamila da Al'ameen tayi girma don har abin yakai ga iyayensu sunsan kome,don kamila Kam Amfara zama Yan Mata kowa yazo da sunan soyayya haka zata koresa itakam fa sai Al'ameen,sosai mahaifyarta ta tsani wannan mu'amalar Al'ameen da kamila ganin ba'a San Asalin ubansa ba haka zuriyan maman sa Yan Ta'adane,gashi baida wani kakkauran sana'a Koh inda zaisaka kamila,Amma haka kamila ta nace sai shi, duk yanda zata zugata Koh fad'a Mata abinda ya dace kamila bataji Bata gani itafa sai Al'ameen. Hakan yasa baban kamila Kiran Al'ameen don ya yaba da Tarbiyan sa ga nutsuwa, yace Masa zai basa kamila Amma ya dage yayi karatu in waec nashi yayi kyau,ya d'auki d'awainiyar karasunsa harya kammala shi Kuma ya Masa Alkawarin xai basa kamila. Jin hakan sosai muhammad ya Kara dagewa da neman na kansa da Kuma karatunsa don sosai yanzun yake son kamila Shekaru sunja lokaci ya tafi rayuwa nata juyawa yau Dadi gobe Akatsen sa,hakan take a wajen su Al'ameen Ranar 3/8/2009 ranar da Al'ameen bazai taba mantawa dashi ba,yau ne suka kammala waec nasu gabaki d'aya makaranta kowa ka gani farin ciki ne d'auke a fuskarsa wasu Kam har kukan rabuwa da juna suke, don irin Wannan ranane Inka rabu da wani har abada bazaka Kara ganinsa ba Haka take a wajen Al'ameen ranar farin cikinsa ne ya kammala karatunsa na secondary sai Kuma jiran result,farin cikinsa harda hawaye ganin yau ya Gama jarabawa Amma bayada Wanda zai zauna ya nuna Masa farin ciki Kamar yanda sauran daliban iyayensu ke Basu kyaututuka da walima na murnar Ranar A hankali yake tafiya jikinsa sanye da uniform na makaranta Yana tafiya Yana tunane tunane rayuwa don a lokacin sun girma shi yanada shekara 18 Salim 15 Khadija 6 Ji kawai yayi wata mota Tasha gabansa kafun ya Ankara ma har sun Wasa Masa wani abu Bai Kara tuna Koh sanin inda yake ba sai bayan sati D'aya D'aya bude ido ya jisa a asibiti Amma baya ganin kome sai duhu,Wanda yake zaune dashi shine Wanda ya tsintosa a bayan gari wajen kauyensu ya fitoh gona kenan yaga wasu sunzo sun yarda Al'ameen a cikin ciyaye,shine ya daukosa ya kawosa hospital da vajin jikin uniform NASA aka gane makarantarsu har labari yaje gidan Adara Amma Amina ne kawai da Salim suka zo asibitin Kuma suke kokarin jinyansa da taimakon mutumin da ya tsintosa, Al'ameen sosai ya Shiga damuwa Daya waye gari baya gani gashi Doctor's sunyi iyya binciken su Amma basuga ciwo ba shi Karan kansa Al'ameen bayajin kome a cikin idon nasa Haka tun Yana kuka harya sadakar ya karbe kaddararsa,bayan makantarsa abin mamaki Koh da kamila ta samu labari batazo Koh duba Al'ameen ba sai abokansa na makaranta dana unguwan sune sukazozzo don ganewa idanunsu shin da gaske ne labarin da sukaji Al'ameen ya makance shine da kansa Yakama Salim ya Masa jagora zuwa gidansu kamila Amma
Chapter 41 · 0% Book details