← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 104

Sashe 44

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page 4 Al'ameen ne ya yanke jiki ya Fad'i,sosai mutumin ya rikice yahau salati cikin kidema Hayaniyar sa shiya matashe samarin dake kwana a d'akunan kofar gida,Suma dai sosai mutuwar Salim ta shigesu ruwa aka watsawa Al'ameen Amma Ina Koh farfadowa baiyi ba Dole tasa wasu daga cikin matasan d'aukar sa zuwa asibiti Usman makwancinsu shiya d'auki gawar Salim zuwa gidansa Washe gari agidan malam Usman aka shirya salim. Al'ameen dake asibiti kam Yana farfadowa da asuba ya tashi hankalin kowa sai ya dawo ankai Salim tare dashi Haka aka kamasa g'wanin tausayi zuwa gidan malam usman,Yana shiga gida aka Kaisa Kan gawar D'an uwansa a hankali ya zauna Kan cafet in hannu yasa Yana lalube ya bude gawan jikinsa na bare yasa hannu ya shafa fuskar Dan uwansa murya na rawa hawaye nabin kuncinsa yake ma D'an uwansa Addu'a Salim sosai ya samu jama'a kamar me don duk wanda yasansa, kuma yaji mutuwarsa yazo,tare da Al'ameen aka kai D'an uwansa kabari. Bayan mutuwar Salim sosai kewa da kad'aici ke damun Al'ameen Koh bacci baya iyya wa saboda kewan D'an uwansa shikenan yanzun baida abokin Hira baida Wanda zai fad'awa damuwar sa baida Wanda zai kwana tare dashi sai Yar kanwarsa khadija ita Kuma mace ce Mai gidan Salim shiya bawa Al'ameen kudi Ya sari mangoro Koh a bakin kofar gidane ya fara saidawa don Bai dace Yana tsallake titi kullum zuwa kasuwa zaman shago ba Ba musu Al'ameen ya karbi kudin yad'an fara business dashi,Kuma Allah yasama abin Albarka Yana samun na abinci da biyawa Khadija D'an hidindimun makaranta Zancen kamila Kam baiyi fushi ba duk da Bata Masa ta'aziyar D'an uwansa ba haka ya sake Kama Khadija don lokacin ta d'anye wayo sukaje gidansu kamila. Kamila ce tsaye da kawayen ta a waje tare da wasu samari uku A bakin mota Al'ameen suna Isa kofar gidansu kamila,yaji hayaniyar maganar mutane Kamar harda ta kamila hakan yasa cikin murna yau dai zasu gana, tunda ya jima Yana zuwa baya samun ganin ta Da saurinsa yace wa Khadija suye wajen da Yake jin muryan mutane Ba musu Khadija na rike da sandar sa suka nufi wajen, Assalamu alaikum Waalaikumu salam D'aya daga cikin samarin ya Amsa Masa Ina wunin ku, Al'ameen ya gaidasu Lafiya samarin suka amsa d'ayan ya zare kudi a Aljuhunsa Yana mikawa Khadija,ungo Yan mata Khadija Kam kin karba tayi don bata Saba bara ba koma yayanta ya hanata roko Koh karban abin hannun Wanda Bata sani ba Karba Mana yarinya D'aya daga cikin kawayen kamila ta fad'a don Bata San Al'ameen ba Yayana ya hanani karban kudin Wanda ban sani ba, Khadija ta fad'a musu tana noke kafad'a Da mamaki samarin ke kallon su Al'ameen mutum ya fitoh bara abasa yace bazai karba ba,toh lfy meya kawo ku gun mu inba bara ba Am don Allah Ina da tambaya ne? Al'ameen yace Allah yasa mun sani Yauwa Kamar muryan kamila nakeji d'azun a cikin ku? Eh ganinan lfy?kamila ta basa Amsa Lafiya kamila in ba damuwa inason magana dake ne Ina jinka,tace tana Masa kallon banza Don Allah mu koma gefe Kai MAKAHO akan me zaku kebe da matar da Zan aura Kai asuwa d'aya daga cikin samarin yace Wani abune ya cake zuciyar Al'ameen shikenan kamilar ma ya rasata shikam yaushe zai samu farin ciki ne duk mai kokarin faranta Masa wata Rana gudu yake ya barsa Kamila aure zakiyi?yace Yana kokarin faduwa tsaban shock Eh aure zanyi Koh kana da matsala da hakan ne Kamila Ina Alkawarin mu? Alkawari kana nufin na aure ka kana MAKAHO Kuma talaka da wanne zanji da ciyar dakai Koh da ciyar da yaranka Koh da maka jakora Koh d'awainiya?Zan dai iyya auren ka a Talaka Amma banda kana MAKAHO kam. Sosai zuciyar Al'ameen ta tsinke Dariya matasan da Y'an Matan suka sake na shekeyanci,Kai kamila bakida mutunci wallahi soyayya ce fa saikuje kusha love da lalube D'aya daga cin Yan matan ta fad'a tana dariya Budurwar da ke gefe sanye da hijab itace kad'ai Bata ma Al'ameen tozarci ba Kama hannun Khadija taye hade tacewa Al'ameen su tafe A hankali Al'ameen ke tafiya Kamar k'wai ya fashe Masa a ciki Bai d'auka Koh nakasa zaisa kamila gudunsa ba Koda kowa zai gujesa Suna sharan kwanan nayin, kawar kamila ta dube Al'ameen,kaga bawan Allah don Allah Ina Mai rokon alfarma a gareka shine ka rabu da kamila Koda itace autar Mata ka barta duniyace ai Koda zata rabu dakai bada tuzarci Koh kushen halitta ba Amma ita Bata dube hakan ba y Ta wulakanta ka kaima ka barta bari na har Abada,Kaye hakuri Allah Yana tare da musu hakure. Insha Allah baiwar Allah na rabu da kamila Nima na hakura da ita Allah ya had'a kowa da rabonsa, Ameen ta basa amsa tana Mai komawa layinsu tabarsa tsaye da Khadija Wannan shine Ranar da Al'ameen ya fita a Rayuwan kamila. Bayan wasu shekaru karatu ya fara zama sai da kudi, a hakan yake ta faman ganin Khadija tayi karatu Koh ba kome zata tallah fawa kanta, Amma Ina kudi ya gagara don yanzun mangoron ma sai a hankali Bai wuce a Rana yayi cinikin 200 Koh kasa da hakan. Gashi a ciki Kuma yake ciwa cikinsa hakan yasa karatun Khadija tsayawa iyya Junior. *An dawo labari* ........... Khadija Kam kuka take kaman me,haka ma Sumayya Allah sarki Ashe haka rayuwar wa'innan bayin Allah yake, tasu kaddarar kenan,a cikin Yan watanni nan da mahaifinta ya juya mata baya taji kamar tafi kowa matsala,ashe itakam ma in an had'a kaddarar ta dana Muhammad nata ba kome bane tunda har tayi karatu ta tashi cikin kudi da lfyr ta Amma shifa ga maraici ga kuncin rayuwa da Talauci. D'aga ido tayi tana kallon Al'ameen dake zaune a kujera fuska tayi ja"yayan khadija baka bani lbrn auren mu ba"?ta tambaye sa Khadija tashi ki tafi kinji kukan ya isa haka, Al'ameen yace batare da ya amsawa Sumayya tambayar taba Mikewa Khadija tayi zata fita a d'akin cikin kuka abin g'wanin tausaye"Khadija"Sumayya ta Kira sunan ta Na'am Aunty "Khadija kiyi hakuri kome na rayuwan duniya Mai karewane Sannan Yana da iyyaka kinji"? Toh Aunty tace tana share hawayenta "Ki d'auki doyan nan ki tafi dashi gobe da safe sauki kawo mini ducuments naki kinji Khadija" Toh Aunty kawai tace tana d'auki laidan doyan ta fita "Yayan khadija na tambaye ka shine kaci no face" Sumayya nagaji wallahih ki barni nad'an huta Mana waima me zakiye da ducuments in Khadija ne? "Oho ba'a sani ba Ina maka magana kana tambaya ta Nima naki fad'an" Shuru ya Mata tare da lumshe idanunsa Itakam ganin ya Mata shuru tasan dai akwai abinda bayason fad'a matane,tashi taye a hankali ta Isa garesa faduwa tayi a kansa da gangan Washhhh yace yana gyara Mata kwanciya "Don Allah ka fad'amin Mana" Kinga Sumayya nifa banason na fad'a Miki abinda zaizo Yana d'aga Miki hankali. "Allah bazan d'aga hankalina ba kawai ka fad'a mini" Ok toh shikenan Amma sai da dare Zan fad'a Miki "Gaskiya Nina gaji da abinda kake minin nan wani irin sai dare Kuma Wannan ai Jan Raine" Banace Zan fad'a ba ki barni Mana zuwa Daren in ban fad'a Miki ba saiki Tuhume ni "Uhmm toh yanzun me zakayi"? Bacci,ya Amsa mata "Bacci a hakan"? Eh..... Tashi Sumayya tayi taje ta d'aura abincin dare ta barsa a d'akin Bayan fitarta sosai yake tunani akan ya fad'a matane Koh karya fad'a Mata karshe dai ya yanke shawaran ya fad'a matan kawai Bayan isha'i Sumayya ce da Al'ameen kwance akan gado Sumayya taye matashe da cinyar Al'ameen sunfi minutes 20 a haka,tunda sukaci abincin dare sukayi sallah, suke a haka Amma Al'ameen baice mata kome akan labarin ba abin sosai ya dame ta Amma ta danne tunda yace zai fad'a zata barsa ya fad'an da kansa. Sumayya!!ya Kira sunanta Yana Mai shafa gashin kanta mai tsawo da kamshi "Na'am"ta amsa Masa Sumayya banso fad'a Miki dalilin auren mu ga ganin cewa kece kikafi kowa sanin hakikanin gaskiya don bana tunanin har yanzun ana cikin zamanin da za'a ma mace aure batare da tasan miji Koh miji ya santa ba. "Me kake nufi"? Sumayya ta tambaye sa fuskar ta a hade Jin abinda yake fad'a Mata Yanzun masifa Zaki mini Koh Jin lbr zakiyi? "Aiba labarin kake bani ba sukata kake"Sumayya tace,tana kokarin sauka a gadon Sorry toh, yace Yana kamota "Nikam ka sake ni " Kin saketan yayi yana rungume da abarsa, naki sakin kin in kajimin mata fa "Allah ni ka sakeni nace maka"tace tana kokarin xame kanta a jikinsa Fushi kikayi ne Gimbiya? " waye Gimbiyar"? Sumayya mana. "Gimbiyar wa"? Al'ameen... Uhmmm kawai tace bata kara magana ba Kinga na miki Alkawari, zan fad'a miki gaskiyan abinda na sani akan auren mu? "Nima nafasa ji yau sai gobe"ta fad'a tana mai sa hannu ta d'auko wayarta dake gefen filo, airp inda ke makale a jikin wayar ta manna a kanne Sai magana yake baiji ta amsa masa ba hannu yasa yana tattaba ta, Gimbiya ina magana kin mini shuru Duk da sumayya taji Al'ameen ya taba ta Amma taki koh sauraransa Shikam gane fushi take yasa sa dagota sama daga jikinsa ya jefata gefen gadon Ihu sumayya ta sake bawai zafi taji ba don laushin katifar dana blanket bazai bari taji zafi ba tsorata kawai tayi don bata tsammaci hakan ba" wayyo wuyana ya karye" Nashiga uku sumayya inga wuyan da gaske kinji zafi dan Allah kiyi hakuri ban dauka zakiji zafi ba, yace yana matsowa kusa da ita Sumayya kam langobewa tayi wai wuya ya bugu"wayyo wuyata shikenan ya kasheni jama'i Don Allah kiyi shuru muga wuyan wallahi bada niya nayi ba Sumayya kam kara lafewa tayi jin ya cicibeta ya daura a cinya kamar wata baby Sannu sumayya koh muje asibiti ne? "Nidai goyona nakeso kayi"ta karasa maganar da make murya Jikinsa na rawa yace, toh... toh... hau, yana dukawa a kan gadon "Nika d'agani bazan iyya tashi zaune ba" Cicibar sumayya yayi ya goya haka ya ringa lalube yana zaga d'aki zuwa baranda da ita sai kusan 10:00 sumayya taji gyangyadi kafun tace masa, " ka kwantar da ni bacci nake ji" Ai da sauri bawan Allah yayi d'aki da ita da lalube ya
Chapter 44 · 0% Book details