Sashe 60
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
~ Na ~ *Rukayya* *Ibrahim* Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa free book Page5 Tunda muka fitoh Banganta ba. Wani irin baki gantaba kuma hauka kike ne khadija koh me? Wallahi yaya da gaske nake banga Aunty ba. Nashiga uku ni muhammad, yace yana kamo hannun khadija suka tsallaka titi zuwa cikin masallaci sosai suka dudu ba Amma basu ga koh mai kamada sumayya ba sosai abin ya gigitashi, ke khadija a daidai ina kuka rabune wai? A kofar fitane fa yaya cunkoso yasa muka rabu. Jingina kawai yayi da jikin ginin masallacin shikam dai ya shiga ukun sa ina sumayyar ta shiga ne wai? Yaya koh dai aunty gida ta koma ne? Wani irin gida kuma khadija bayan saida nace ku jirani a global xaki wanice ta koma gida nadai san sumayya bazata koma gida ba Daga khadija har muhammad hankalin su ya tashi har hankalin yan agaji ya dawo kansu d'aya daga cikin su ya tambaye sa malam lafiya naga kana ta zaga masallaci kaje ka dawo, tun dazun yanzun fa ana neman 4:00 bazaka tafi gida ba ga kanwarka ma naga kuna ta yawo tun d'azun lfy kam? Ina fa lfy wallahi ranka ya dade da matata mukazo masallaci amma ban ganta ba gabaki d'aya na gama iyya dubata amma bangan taba Wace irin magana ce wannan ita matar taka yar yayece koh jaririya da za'a nema a rasa koh hanyar gidane bata sani ba? Ranka shi dad'e ni nasan bazata koma gida ba tunda nace ta jirani toh tabbas zata jiranin Kaga malam karkazo ka d'aga mana hankali a wani unguwa kuke ne? Sintali ne.. Sintali A koh B? Sintali A ne ranka ya dade Amma dai kai d'an rainin wayo ne ina sintali A ina macilin da bazata iyya komawa da kanta ba kazo kana kokarin daga mana hankali? Kayi hakuri ranka ya dade Na hakura amma ka fita kakama kanwarka kubar masallaci nan ya zakazo da maganar da hankali bazai d'auka ba matar ka ta bata, ina macilin ina sintali?da bazata koma ba Kayi hakuri.. Kama gabanka malam? Haka Al'ameen ya fita kaman k'wai ya fashe masa a ciki Da sauri khadija tazo ta kama masa hannu haka suka fito a masallacin gwanin tausayi Tsallake titi sukayi suna tafiya Gabaki d'ayansu inka gansu kaga wa'inda basu da nutsuwa gabaki d'aya zuciyar Al'ameen bugawa take kamar ance masa sumayya zata barsa Sunzo daidai titin doruwa kamar daga sama khadija ta hango mace da hijabi tana tsallako titi Allah yasa akwai wutan sola shiya bata daman ganin wance ta tsallakon da karfi ta kwala ma sumayya kira Aunty!!! Ai da wani irin mugun sauri Al'amesn ke magana, kee kin ganta ne ina sumayyar take tana ina? Kafun khadija ta basa amsa da gudu sumayya ta karaso karesu"lafiya har yanzun baku koma gida ba"? Kee sumayya kina da hankali kuwa banace miki kafun mu shiga masallaci, kujirani a gidan man sintali ba koh ba haka nace ba, shine zakisa kafa ki koma gida don tsabar kin raina min wayo gani d'an iska koh? "Don girman Allah kayi hakuri, wallahi sace mini takalmi akayi shine na tsaya nema na jira mutane suka fifita duk ban gane ba dana fitoh wajen global, nan ma ban ganku ba shine nayi tunanin kun koma gida saina koma nima danaje kuma naga baku dawo ba, shine nabiyo ku" Don Allah yaya kayi hakuri tsabani aka samu! Na hakura khadija Amma sumayya karki sake mini haka Am warning you? "Insha Allah" tace tana kama hannunsa dake cikin na khadija don baizo da sanda ba suka tsallaka titi Bayan sun isa gida ganin sun kusa makara yasa sumayya hana khadija zuwa gida abincin sahur ta iba mata tuwo ne miyan kifi d'anye suka zauna a waje suna ci Al'ameen kam tuwo kawai yakeci da miya baya cin kifin Da mamaki sumayya tace "yayan khadija ya bakacin kifin gashi mun kusa makara fa"? Sumayya bazan iyya cin kifi d'anye ba kar kashi ya makale min a wuya " tarwad'a ne fa" Nikam ah ah Hannu sumayya tasa a kwanon miyan ta yago kifi tasa mai a baki"toh bude bakin nasa maka" Da sauri khadija ta kauda kai kamar bata gansu ba don wallahi sun bata kunya Al'ameen kam bude baki yayi sumayya sai da ta ciyar dashi kifi har yace ya isheshi kafun ta ci nata Bayan sunyi sallan asuba khadija ta koma gida Al'ameen kam bacci suka koma suna ramakon na jiya Yau koh tafsir basu samu zuwa ba saboda baccin dake idanun su har 12:00 suna bacci a d'aki Assalamu Alaikum!! wasu yan matane guda hudu ke sallama sunfi minutes 8 suna buga sallama shuru Al'ameen kamar a mafarki yake jin sallama akai akai mikewa yai hade da amsa musu Ina kwana? Lafiya, ya amsa Am wajen sumayya mukazo Ok lafiya kam? Eh munzo tambayar lallen sallah ne Ok bara na tada ta Ah ah ka barta in bata tashi ba inyaso gobe sai mu dawo Ok toh Allah ya kaimu Ameen, in ba damuwa inta tashi kace yaran gidan Malam yunusa ne sukazo tambayar Lalle kar wasu suzo su riga mu? Toh yace yana d'aukar boket bayan sun fita wanka yayi ya shiga dakin dayake yanzun yasan soket in kunna TV jin an kawo nepa ga fanka na hura d'akin danna soket in yayi daman jiya sunnah suke kallo aka d'auke, zama yayi yana sauraron wa'azi hannun sa d'auke da calbi yana ja Sumayya bata tashi ba sai azahar nan ma shiya tashe ta kafun ya tafi masallaci ******************* Haka rayuwa yayi ta tafiya axumi nata karewa a hankali hankali customers na sumayya suke zuwa tambayar lalle tun sallah saura kwana goma ita karan kanta batasan adadin wa'inda suka tambaye lalle ba ita dai ta amsa zatayi amma suzo da wuri, sannan tana musu tallan wanda zaiyi kitson sallah kanwar mijinta nayi ai kuwa khadija ma tatara customers sosai, kayan sallah ma bana muhammad ne ya d'auke sumayya da khadija har kasuwa sukayi sayayyan sallah duk da sumayya taki yarda ganin tana da wasu zanunuwan a akwatin ta amma ina yace na akwati daban na sallah daban, ba laifi yasai musu kaya itama ta dad'a wasu da kudin ta haka ma khadija ta kara mata har kala biyu bayan wanda ya musu she karan kansa gezena biyu yasaya sumayya ta kara masa biyu duk sunka kai dinki. Akwana A tashi yau dai saura kwana d'aya sallah kofar sumayya makil da jama'a daga masu kitso harda masu lalle, harda su suwaiban adara yau ana bin layi a kofar, sumayya na hango sanye da riga da wando baki tana ta fama da lalle sai khadija dake ma wata yarinya kitson brazil kulu da bit Har yamma mutane ne makil ba ita ta rabu da mutane ba sai kusan goma na dare nan ba hakuri ta basu akan gobe su dawo da asuba Al'ameen dake d'aki kwance yana lazimi shiya raka khadija gida Yau sumayya koh girkin asuba bata samu tayi ba na bud'a bakin ma watace ta mata girki tana ma yarta lalle Yauma bayan sunje tahajjud suna dawowa ne suka samu tuwo a bakin titi na asuba suka saya, dashi sukayi sahur Sumayya suna komawa gida suna sallah ta kwanta ai koh gama d'aukarta bacci baiyi ba tafara jin sallaman mutane ga idonta duk bacci kin tashi tayi Al'ameen ne ya fita ya basu hakuri akan sumayya na bacci Amma haka bayin Allah nan sukaki tafiya taburma suka shimfid'a suka zazzauna suna jiran sumy(masu lalle gaskiya kuna ganin abu a sallah har kwana ana muku a d'aki) Surutun su shiya hana sumayya komawa bacci haka tanaji tana gani ta kasa bacci dole yasa ta fitoh jin jama'a sai dad'uwa suke Ai tana fita saiga khadija da tawagar masu kitso sun tasata a gaba Haka suka dukufa suna neman halal nasu, Al'ameen fita yayi a d'akin sumayya! yakira sunan ta "Na'am"ta amsa tana mai mikewa ta bisa d'akin ganin ya koma Sumayya zan fita na karbo mana dinki, maganar zuwa kasuwan fa muna sa ran gobe sallah fa naga bamu shirya kome ba? "eh kam gaskiya nima naso naje kasuwan nan da kaina amma yanzun ba iyya fita zanyi ba sai dai ku tafi da khadija in yaso sai na rubuta mata list"? Ok nace na saya mana watanda ne?(naman shanu da ake yankawa a ranan jajeberi ana saidawa a unguwa) "Ah ah ka saya mana kaji gaskiya tunda sallah ne" Shinkafa koh tuwo zakiyi? "Habba tuwo ranan sallah, shinkafa zanyi da miya sai coslow da kaji sanan zanyi masa da miya" Ok daman so nake ranan sallan nan mu kaiwa gidan su Ammar abinci kuma muje mu gaida iyayen sa sai kuma nayi tunanin kar suce don kudin su yasa muke son rabansu fa? "Ah ah yayan khadija in zakayi abin Alkhari kayi kawai karma ka bari shaid'an ya saka maka wani tunani daban a ranka kaji"? Shikenan sumayya Allah ya kaimu goben kinyi lalle kuwa?yana maganar yana kama hannun ta "Ina naga lalle daga ni har khadija ba lalle ba kitso" Kai gaskiya nifa an takurani tun sallah saura kwana hudu ban sake cin abincin kiba ki taimaka ki mana girkin sallah da kanki "Insha Allah la'asar nayi zan sallami kowa wanda ya samu da wanda bai samu ba duk sai suyi hakuri nima na samu nayi aikin sallah" Ok kiramin khadijan inkin gama rubuta list in mu tafi Haka koh akayi sumayya list ta rubuta ta baiwa khadija duk yanda jama'a masu kitso suka ringa roko sai da sumayya ta d'aga khadija suka tafi kasuwa dinki suka fara karbowa sai cefenen da sukayi sosai sukayi cefene sai da ya cika bairo. Bayan khadija ta dawo sumayya tashi tayi ta gyara kajin duk da wasu sunso karba mata Amma taki yarda soya kajin tayi daman guda biyar ya saya ta rabawa mutane d'aya sosai tayi ta ayyukanta wasu kamma ganin aiki take kuma ba karewa zaiyi ba, zuciya kawai sukayi suka tafi abinsu wasu kam kama mata aikin sukayi duk da ta nuna su bari amma kin bari sukayi wasu sun gyara mata tattasai wasu sunkai nika cikin kankanin lokaci ta kammala had'a abubuwan sallan ta miya ma ta soya amma bata