← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 104

Sashe 17

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

layin su Goggo Amina, Nikam Ina shiga cikin gidan da yake ana ruwa ba kowa a tsakar gida shashen mu na nufa,aje jakana da takalmi nayi a baranda na kwabe lufayar jikina da yajika jakaf da ruwa na makala a igiya, dakin na shiga nadau towel na daura na zame dogon wando da NASA da under wear na makala a igiyar kofa , Kitchen na shiga na kunna gas na daura bojuwa (tukunya) na zuba ruwa a ciki,boket na dauko na ibi ruwa a Randa na tsaya a cikin kitchen in ruwan na tafasa na juye a boket in daidai yanda zanyi wanka na dauki boket in nayi bandaki,wanka nayi na fitoh,har lokacin ruwa ake Alwala nayi,jakana na dauka a baranda na shiga dakin, Jin dis dis Kamar panfo yazo daukewa yasa na lalube wayata a jaka na haska dakin idona ya sauka akan kujiran da yayan khadija ke k'wanciya ya jika jakaf da ruwa saitin wajen na yoyo fita waje nayi da sauri na d'auko baf nazo na tare ruwan,kaya na dauka na bacci na saka da hula harda socks don wani irin sanyi nakeji har cikin k'ashina sallaya na shinfida na Tada sallah mangariba da Isha nayi shafa'i da wutire , blanket na dauko nahau gadon na lullubu abina na kwanta da wani irin ciwon Kai da zazzabi nakeji gashi kafafuna sai zuge suke mini nama rasa meke mini Dadi Al'ameen suna tafiya da Khadija Chan dai Khadija ta kasa hakuri tace ,Yaya nikam na tambaye ka Mana? Allah yasa na sani dija, Kai Yaya ni banason dijan nan ai sunan tsofine, Toh hadixa Ina jinki, Habba yaya ta fada tana hada fuska, Sorry toh kanwata Ina jinki Yauwa Yaya nikam Aina ka hadu da Aunty Sumayyan ne harkace kana Sonta? ....Dam dam haka gabansa ke bugawa , Khadija meyasa Kika mini wannan tambayar,? Ba kome Yaya kawai na tambaye Kane , Ah ah Khadija fad'amin gaskiya nasan baki tambayar Abu banza, Am Yaya Naga baka taba bani lbrn kana da budurwa ba kawai sai naji Wai kayi aure za'a kawo Amarya, Toh Khadija ke abokina ne da saina fada Miki Ina da budurwa, auren Kuma yazone a bazata ban dauka iyayen ta zasu bani ita lokaci d'aya ba, Amma yaya kaga gidansu aunty kuwa Mai azaban kyau ga Yan gayu k'yawawa a gidan Kuma Aunty ma kyakkyawa fa Yaya toh ma Ina kake zuwa daga Tashar kayan marmari sai wajen sana'ar ka Ina kaga aunty har kuka fara soyayya? Ikon Allah Khadija Wai tambayar nan Kam na lfy kin sani a gaba da tambaya sai kace wani sa'anki , Kayi hakuri Yaya dai dai lokacin suna iso kofar gidan Goggo Amina, Muje Khadija na rakaki cikin gidan nama Goggo bayanin dalilin yin darenki , Toh Yaya , shiga sukayi cikin gidan tare, Goggo Amina ce ta amsa sallaman tasu tana fama da icce a runfar girkin ta Isa sukayi ya gaishe da ta Yamata bayanin dalilin yin Daren Khadija,.. Wallahih Muhammad Nima sai da na tura yaro yajimin lfy Khadija har dare Bata dawo ba ga aikin dare da tace zata dawo ta Kama mini, ya dawo yace min ba kowa a shashen ku, Kiyi hakuri Goggo, Basu dawo ba sai yanzun Al'ameen yace Yana mike wa, Ba kome muhammad shine ka tasata a gaba a ruwan nan Maimakon ku bare Sai ya tsakaita, Goggo Nima haka nace Mata Amma tace Zaki Mata Holo itakam sai gidan Goggo shine na rakota Gggo ruwan da yawansa bansan karfe nawa zai dauke ba shiyasa nace gwara na dawo Hakane Kam da gaskiyar ki Khadija Toh sai da safe, Goggo Allah bamu alkhari Ameen suka amsa ita da Khadija shikam fita yayi ya Kama hanyar gida, Ina kwance Amma ba bacci nake ba tunani kawai na fada nayi zugum gabaki daya gari yamin zafi, daidai lokacin ya shigo kofar duk ya jike Daman jallabiya ne a jikinsa ,, hauro wa dakalin Yayi ya zare jallabiyar sa ya aje a cikin boket in wanka dakin ya shigo daga shi Sai gajirin wando, da sallama a bakinsa Ina kwance cikin duhu don na kashe hasken wayana naji buruntu ana kokarin shigowa dakin don ni Sam banji sallamar ba, hasken wayata na kunna me Zan gani yayan Khadija ba Kaya, murd'adden damtsen hannunsa naci Karo a waje ga fafad'an kirjinsa mai cike da yalwan gashi,baki sitik kwance akan farar fatarsa kafarsa farare tas sai gashi ke kwance a lallausar fatar kafar tasa ai bansan lokacin da na k'wala ihu ba na dirko a saman gadon,na Kama hanyar waje don ni sai ma gani nake kamar ba wando a jikinsa don ajike wandon yake tsabar birkita hanyar kofa na nufa zanfita na bar Masa dakin, Jin ihunta sai ya birkitasa ya dauka Koh wani abune ya sameta Jin ihun take akai akai hakan yasa ya gigice shima ya fara neman hanyar kofa cikin lalube,da D'an saurin sa Jin itama kofar ta nufo tana ihu har lokacin, Ji kake gauuuu! sun garu da juna a kofa daga shi har ita ihu suka saka a tare, sai kawai suka kuma zubuwa ji kake timmmmmmm............ *Gobe Monday Ina da jarabawa bazakuga update ba fan's* *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara* *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* *Na tsunguno(habil)* *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* ) *Turaren turara jiki after birth* , *Na d'aki(halud Al'oud)* *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* Contact them vie 08028827241 or 09033791049 *MATAR MAKAHO*
Chapter 17 · 0% Book details