← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 104

Sashe 97

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

tayi jikinta tana kuka yau kam ta rasa ina zata sa kanta, murnan samun babies koh murnan ganin mahaifiyarta koh mijinta dole tayi kuka, ummi karan kanta hawaye ne ya cika a idanunta tana shafa kan sumayya ya isa haka momcy yi shuru kinga ba lafiya bane dake koma ki kwanta, tana maganar tana rike da hannun sumayya har ta kaita bakin gadon ta aje ta. Waini yau hafsa nake gani ne koh gizau idanuna kemin koh mafarki nake ne? Itace dada Abie yace yana dafe kansa cikin takaici da bakin cikin abubuwan da suka faru a baya. Mijin hafsa ne yace, Hafsa kin sansu ne daman nina d'auka koh iyayen yarinyar nan ce? Baban kalamu ne da kakarsa wannan kuma Addansa ce ta nuna sumayya. Daga sumayya har kalamu da Abie a tare suka jefowa Hafsa tambaya lokaci guda, baban kalamu wani kalamun? Da sauri abie yace hafsa ban gane ba wanene kalamu. Nuna masa kalamu tayi dake tsaye cikin shock na abinda nanne tace, yanzun wai sumayya Addansa, ta yaya kamar ya?baigane ba? "Ummi kina nufin kalamu d'an uwa nane"? Hafsa kina nufin wannan yaro, yaro nane? Kallon sumayya da abie hafsa tayi jin tambayar da suka jefo mata, eh kawai tace tana kama hanyar kofa zata fita tare da kallon mijin ta, yauwa Alan guburo mutafi naga dangin ta sunzo zasu zauna a gunta. Ah ah hafsa zuwan mu bazaisa ki daina hidima da yarki ba. Ah ah dada zan tafi , Allah ya sauwaka momcy. "Ameeen ummi in zaki dawo a kawo mini sabulun wanka" Toh momcy muje kalamu koh zaka zauna ne? Ah ah nanne muje yace yana kallon abie da mamaki wai wannan ne babansa, shi abin ma yajisa wani banbara kwai. Kokarin fita a dakin suke a hankali abie ya kama hannun kalamu daya wucesa zai fita a d'akin, kalamu bazaka ma abie magana bane? Murmushi kalamu yayi sai kuma yaji hawaye ya taro masa, abie ashe kanason na maka magana, shine zaka kyamace ni ka kyautata rayuwar yar uwata, amma ka wofantar da nawa rayuwar ka barwa uwata ni, na zauna a matsayin agola a gidan da, bana ubana ba ya maye gurbinka ina Amfani da sunan sa koh a makaranta, bai taba nunawa duniya bashi ya haifeni ba koni bansan bashine mahaifina ba, sai yau akan me zan maka magana ni bansan wani uba ba sai ........ "bai karasa ba sumayya ta mike ta wanke sa da mari cikin bacin rai ta soma magana, karka kuskura ka fara abinda zai dame ka wallahi kayi kad'an ka zagar min uba na barka,ni a haka nake son abina koma me zaimin bazan taba kinsa ba" sai kuma ta kama kuka. Da sauri nurses dake falo suka shigo d'akin, akan surutun dake tashi, hakuri aka basu akan za'a kiyaye magana ne mai muhimmanci ake, ganin kalarsu yasa su barinsu a dakin. Daker aka samu suka sassanta nanne ta koma gida dasu goggo yayinda mazan kuma suka koma hotel sumayya ma ita da dada kadai aka bari a hospital. Washe gari aka sallame ta saboda kyaun da jikinta yayi, don haihuwar duk da yazo da gardama amma tana haihuwa shikenan. Gidan nanne aka maidata bata koma gidan hayansu ba,sosai ake kula da ita muhamamd a rana sai yazo sama da sau hudu, sai da sumayya ta kwana hudu da haihuwa kafun suka koma shirye shiryen dawowa jalingo don anan ake son yin taron suna gashi yan nijar ma sunce suna shirin zuwa, duk yanda sukayi ta rokon nanne ta biyosu taki tace bazataki bin umurnin mahaifinta ba na raba kanta da zuriyar shugaba, saida mijinta ya nuna bacin ransa da nuna mata yaranta nada hakki akan ta, sannan kalamu bazaiji dadin hakan ba tunda shima so yake yaje yaga dangin babansa, daker dai ta Amince washe gari da sumayya ta cika kwanan biyar sukabi jirgi saijalingo. Muhammad murza idanunsa yayi yace a gidan sa da babansa ya sai masa a Amazon sumayya zata sauka, ba musu duk da abie yaso ta koma gida Amma ganin hafsa da Al'ameen basason hakan. Gidan sumayya ta sauka dayake babban gidane ga d'akuna shiyasa gidan ya d'auke su, duka harda su hafsa falmata su babayo muhamamd goggo dasu mahmah, kalamu kam shugaba family house ya sauka kuma ba karamin farin cikin ganinsa sukayi ba. Babu inda haihuwar sumayya bai bazu ba jama'a sai tururuwan zuwa dubata suke harda yan Abuja laila ma daga adamawa ta gangaro, a ranan yan nijar suka diro nageria gabaki d'aya yan uwan yusuf ne harda shi karan kansa ma, wannan zuwa harda lawiza da nabila, sosai gidan ya dad'a cika da yan uwa kota ina yan gidan shugaba ma tun a washe gari suna matan suka diro, yusuf a gidan sarki ya sauka dayake suma ana gobe suna suka zo, kai sumayya taga jama'a iyya jama'a ga wani irin lalle da aka watsa mata mai masifar kyau da ketson suna duka. Yau take suna yara sunci suna NA'IMA da NA'IFA , tun Asuba yan gidan Adara suka diro su inna asabe inna lami Ana gindin murhu a sauke wanshan a d'aura wanshan, shanu uku aka yanka da rago biyu, duk suna ta kan gyaran nama, ga abinci kala kala, gashi koh ina ka leka zakaga group group na mata kowa da angon su mai zafi, wanda abie ya d'auki nauyi duka, yan nijar nasu da ban haka dangin adara, yan shugaba family house ga yan gembu, ashan gefe naga MATAR MAKAHO FAN'S ansha anko na Atamfa mai ratsen flower green ana zazzaune ana dirkan shinkafa a manyan tireruka hhhhh. Sumayya dake sanye da wani hadedden material gown wanda yasha dinki ga sarka na d'anyen gwal da sarki ya bada aka kawo mata, sarkane da dankunne sai warwaro ga agogo mai zafi na mata duka, tasha heavy make-up sai d'aukan hotuna suke da kannen Ammar dake sanye da Ankon su, khadija da kalamu dake zaune a gefe suna cin shinkafa. Muhammad da Ammar harda su ramadan zulkiflu gidado badaru duk yanzun sun chanja kamar basu ba, suna zazzaune a kofar gida a rumfar da aka kakkafa abinci suke ci mairai da lafiya. Tun daga nesa suke jin ihun yara da mutane suna rugawa a guje, da sauri suka mike gabaki d'ayansu suna kallon abinda ke faruwa. Mutum suka gani kamar mace ne koh na miji bazasu gane ba, kadangaru manne a jikin sa tana gudu suna binsa wasu na jikin ginin unguwan suna rugowa suna binta sosai kota ina kadangaru ga wasu runduna na binta a baya, sai wata mata dake gefenta rike da sharbebeyar bulala tana kad'a mai kadangarun suna tafiya a haka. Da sauri su muhammad suka ruga cikin gida da gudu har ana rige rige, ganin wajen da suke suka nufo. Suna shiga suka rufe kofar gidan da karfi suna ji sai bugawa matar take akan don Allah abude mata, kiri kiri su muhammad sukaki budewa har abin yaja hankalin matan dake compound sosai, dada dake rike da jinjira zata kaiwa kawayen ta dake falo a zaune ssga dayar, itace taji hayaniya aje jinjiran tayi ta fitoh compound, ganin su muahmamd da jama'ar tsakar gidan a tsaye yasata karasawa bakin get in tana tambayar dalili, kafun ma su muhammad suyi mata bayani tuni tasa hannu ta zare sakatar get in, ihu Ramadan ya sake tsabar rikita yare ma ya fara. Dada na budewa idanunta ya sauka akan matar dake rike da bulala kwalalo ido tayi cikin mamaki tace wanake gani anan kamar Nafi............. kafun ma ta karasa maganar ta idanunta ya sauka akan wance ke tsaye mammanne da kadangaru ga bataliya a kasa, ai ihu dada tasa ta ruga ciki da gudu, da sauri inna lami tazo zata rufe get aida sauri wannan matar ta banke kofar ta kora mai kadangaru ta shigo, itama shigowa tayi, ai ana ganinta, ihu ne yake tashi abinka da mata atake masu Aljanu Aljanunsu ya soma tashi, gidan suna gabaki d'aya ya rikice ya zama gidan tsere kowa gudu yake yana burmuwa falo wasu kitchen masu Aljanu kam sun zuzzube.............. Ruqeenjalal *MATAR MAKAHO*
Chapter 97 · 0% Book details