← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 104

Sashe 52

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*HAPPY INDEPENDENT DAY* Page5 Lafiya daman nazo akan maganar make-up inne, naji shuru baki kirani ba inna kira ba'a picking call in. "Ok toh ai na zaci koh kina da fahimta ne, ki gane me nake nufi" Kamar ya sumayya ban gane ba? "Ok toh kamila bara na miki gwari gwari, bazan koyar ba" Akan me? bayan kince sai mijinki ya yarda kuma a gabanki yace ya Amince. "Eh ya amince nima haka yace mini sai dai ni ban Amince dake ba har kizo gidana kina kare mini tanadi" Kamar ya bangane ba me kike nufi?zanzo gidan ki in kare miki tanadi?ina ma gidan yake bare "Hhhhh hayyeeee nanayeeee ashe gidan ba yanda yake akazo cin moriyan masu shi" Ke sumayya nafiki rashin mutunci don naga baki dashi ya daga abin Arziki sai tsiya ya biyo baya matsalanka da matsiyaci kenan bai gaji arziki ba "Ehhhhhh yariya tsiyama waje ya samu ki kalleni da kyau daga ni har mijina kinga Alamun yunwa a tare damu, kuma ki kallen sama da kasa koh uwar ubanki bataci arzikin da naci ba harta mutu ke uwarki data aure ubanki har yanzun bataci arzikin danake ciba. A'uzu sumayya wani rin , zagine haka kar in sake jin kin tanka mata shige ki wuce d'aki, don Allah kamila kiyi hakuri Kutt ni kike xagi? ai kamila super tayi da jakarta tayo kan sumayya da mugun sauri "Sumayya da gudu tayi kitchen tabarya ta rarumo ta rike"don uwarki kizo yau saina rusa miki kai shegeya harni zakima bariki kizo mini da yaudara da sunan koyan kwalliya" Ai da sauri kamila taja birki, in ba tsoro ba ki aje abinda ke hannunki yau saina nuna miki true colour na. "Shegeya akan me zan aje nasan dame kikazo kizo kima mijina asara a banza " Shammatar sumayya kamila tayi tana magana, da sauri tayi kanta gadan gadan da kwalba a hannu Ai ji kawai tayi Al'ameeen ya hankad'ata gefe, don duk abinda suke hankalinsa na kansu, keee kamila kin isa kizo har gida kice zaki bugarmin mata kimin asara akan me? Ke kin kini na samu mai zama dani shine zaki bugeta Wayyyo nashiga uku na lalace wayyo hannu na innalilahih kun kasheni, kamila ke ihun nan tana rike da hannunta wanda Acid ya zube mata akai "Subahanallah daman abinda kike da niyar watsa mini kenan Algunguma shegeya, aikokin watsa min bashine yake nufin karewar auren mu ba tunda ba idone dashi ba bare yaga yanda na koma" Sumayya meke faruwa ne haka meya sami hannun nata naji kina cewa zata zuba miki Kamila kam ihu take kamar ranta zai fita Ihun kamila shiya jawo da hankalin jama'ar gidan kofar su Al'ameen, da sauri daga maza har mata yara da manya suka nufi kofar donjin ba'asi "Ruwan Acid tayi niyar watsa mini Allah yasa ka shureta shine ya zube a hannunta hannun sai d'ayewa yake" Subahanallah Al'ameen yace yana nufar inda kamila take, kee kamila tashi muje asibiti tashi tashi yau an bonu Kaiii karka kuskura ka taba ta kaji na fad'a maka, keee Kinsan su waye a gidan nan har kika iyya d'aukar Acid zaki zo ki zubawa mutum a cikin gidan Adara? kutumar uba iro yace yana nufar kamila Salame ce ta Lailayo Ashar ta maka, Ci ubanta dan uwarta(wa'iyyazu billah) koh dabban gidan Adara bama bari aci zalinsa bare mutum Ai kafun Al'ameen yace wani abu tuni iro ya fara wanke fuskar kamila da ruwan maruka ji kawai kake kauuu kauuuu kauuuu Ihun kamila ke tashi yanda kasan ranta zai fita bugunta suke tana kokarin gudu wasu su kamo ta, Al'ameen karan kansa hankalin sa ya tashi da kukan ta kamila keyi duk yanda yaso kwatarta abin yaci tura karshe ma salman turesa yayi saura kad'an ya fad'i sumayya ta taro sa Jama'ar kofar gida su suka shigo gidan jin kukar mace kamar me, shigowa sukayi ganin abinda ke faruwa yasa su rugawa a guje suka kwace kamila Ai kamila na ganin ta tsira da wani irin matsifeffen gudu ta falla waje kamar walkiya ga hannu duk ya d'aye fatar Bayan gudun kamila suwaiba ce ta d'auki jakar kamilar, Kai Allah ya mini ga jaka mai azaban kyau maybe ma harda cash a ciki, takara sa maganar da fita a kofar Bayan fitar jama'a a kofar Al'ameen rai a bace ya fara magana sumayya yanzun kin kyauta fisabilillahi daga abin arziki saiki kama zagin yarinya "Ok watoh laifina kake gani kenan na zagi budurwan ka koh"? Waike sumayya meye haka duk wacece ummulkaba'isin wannan matsifar tun farko me yasa zaki zageta akan wani dalili yanzun mutuncin kine ashar koh zamanki a gidan nan ne kika koya, ni fad'a nake miki a matsayina na mijinki ba saurayin kamila ba, yana karasa maganar yayi d'aki ya barta tsayi kamar an dasa ta Sai yanzun sumayya tayi data sanin biyewa kamila koh yaushe kamila tazo gidan saita had'ata fad'a da mijin ta ina bazai yuba, kitchen in ta shiga taci gaba da ayyukan ta, don batason basa hakuri yanzun ganin ransa ya baci sosai Da misalin karfe 11:20 saiga yan koyan make-up inta sunzo a waje suka zauna ta shinfid'a musu taburma suka fara training don yau kwanan su biyu da fara koyo Jin d'uriyar jiniyar motar yan sanda sukaji ya tsaya a kofar gida, ba'a wani jima ba saiga matan yan sanda sun shigo gidan har kofar su sumayya Sallama dai... "Yauwa sannunku da zuwa lfy"? Lafiya ba lau ba don duk wanda yagan mu baiga lfy ba, wacece sumayya? "Ikon Allah nice wani abinne ya faru"? In munje station zakiji dalili, shige muje d'ayar yar sandan tace tana kokarin kama hannun sumayya Da sauri sumayya ta fizge hannunta tare dama police in kallon banza, babu inda zani wallahi akan me banyi kome ba Awani ce za'a tafi dani Babu wanda zai tafimin da mata ba tare da sanin laifinta ba, Al'ameen da yafitoh d'aki da sauri yake fad'a musu haka Kai ka iyye bakinka fa kasan a gabansu wa kake babu ruwan mu da makantar ka wallahi koya maka hankali zamuyi. Sannu uwar sa koya masa hankali na rantse kika tabamin miji ubanki za'a taba, station ne dai baza...... Bata karasa ba taji saukar mare tasss a fuska police in ta tsinketa dashi ai kafun ta sauke hannunta Al'ameen ya watsa mata rabonta itama duk da ba'a fuska ya saita ba amma ta maru kam Kutturu hukuma ka mara yau daga kai har matar taka sai munga gatan ku a jala yau innan, waya tayi wasu mazan yan sanda biyu suka shigo aka rufuwa Al'ameen da sumayya da karfin cin tuwo za'ayi waje dasu Al'ameen kam anfa kasa tafiya dashi sai kokuwa suke, yau sunga ikon Allah kama MAKAHO ya gagare su sumayya kam an fita da ita waje bayan ta sanya hijab Ammar ne yayi packing mota da sauri ganin yanda jama'a suka cika kofar gidan ga sumayya an tisata a gaba cikin sassarfa ya karaso wajen yana tambayar ba'asi ganinsa da daula yasa police in saura ransa suka masa bayanin sunzo kama sumayya ne Al'ameen ya mari police Cikin gidan Ammar ya shiga da mamaki yake kallon Al'ameen dake ta fama da police da sauri ya karaso wajen hannun Al'ameen ya kama ya rike hade da kiran sunan sa Tsayawa da kokuwar yayi, Ammar kaine? Eh wai meke faruwa ne, meka musu? Wallahi ba musan me muka musu ba daga zuwa wai zasu tafi da sumayya na tambayi dalili wai sai munje office insu kajifa. Gaskiya ne Al'ameen ba'a fad'awa mutum laifinsa sai a station kazo muje ba abinda zai faru mundin kaine da gaskiya Binsa Al'ameeen yayi police kam sai hararan Al'ameen suke da kitsima irin dukan da zaisha a hannunsu in ya shiga cell Alfarma Ammar ya nema a barsu sumayya su shiga motar sa inyaso sai police shigo ciki Bayan an isa station kenan officer ya had'asu da iyayen kamila a office insa sannan ya kalli sumayya, an kawo mana karanki kinyi kokarin zubawa wata Acid a fuska Allah ya kiyaye ta, ya zube a hannu bayan haka baki barta ba kika mata duka yanzun haka tana kwance a police clinic don haka zamu rikeki anan don iyyayenta zasu kai kara kotu Amma dai yallaboi kafun a kamata ai sai an tambaye ita sumayyar ba'asi itama aji tata jawabin sannan kamila ta kawo shaida ku kuma saiku kamata ku rufe, Amma daga fad'a muku magana kuma sai ku rufe mutun ba bincike haka ake Hukunci?Ammar ne ke maganar yana nuna officer in Toh kai kuma malam asuwa har zaka nuna mini abinda ya dace nayi koh kafini sanin doka ne? Ban fika sani ba haka zalika bazan barka ka rufe baiwar Allah ba dalili ba akan me? Kai malam dakata kasan a gaban wa kake kuwa? d'aya daga cikin police in yake Tambaya Ammar Koma waye ne shi, nadai gama magana sumayya fad'a musu menene Ainahin abinda ya faru Sumayya ba tsoro ta bayyana gaskiyar hakika nin abinda ya wanzu tsakaninsu da kamila Kuna daiji koh asalima kamilar ce bata da gaskiya koh a hukunce wanda yazo ya sameka har cikin gidan ka kuma yajaka da fad'a kome akai masa shiya kai kansa, sannan a maganar nan ba ruwan sumayya haka zalika Al'ameen bada niya ya zubar da acid in a jikinta ba haka zalika itace take kokarin cutar masa da mata kunga kenan duka wannan abinda ya faru ba ruwan sumayya da Al'ameen duka, kuma jama'ar gidan ne suka mata basu ba ya karasa jawabin yana bin officer in da kallo Kaima ai yanzun gashi ka yanke hukunci ba tare da bincike ba menene hujjar ka? nace wa kamila ce taje da acid in, baban kamila ya tambayi Ammar Ku tura d'aya daga cikin yaran ku officer aje a d'auko goran acid in Allah dai yasa sumayya baki taba bako? "Eh yana nan ata gefen kitchen a kasa" Ok aje a d'auko saiku saka a gwada yatsun hannun wanda aka gani a kai wannnan ma ai hujjane koh? Wai kai a matsayinka nawaye har zakana bamu order kai waye? Hannu Ammar yasa a Aljuhu ya zaro ID card nasa ya nuna Ai da sauri duka police inda ke wajen suka kame tare da sara masa A gaskiya station nan yana
Chapter 52 · 0% Book details