Sashe 35
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
shiga d'akin tayi Kaya tasa,tana Gamawa ta jawo abincin "yayan khadija muci abinci" Sumayya kici nikam na koshi saiki dumamin da safe. "Ni wallahih ban yarda ba,toh bakace ka hakura ba Koh baka hakuran bane" tace tana hawaye Tabbas ko yaki Koh yaso Sumayya ce rufin asirin sa inba itaba bashida wajen da zaici abinci tunda ba kudi Koh sana'a bane dashi,sauka yayi ya matso Yana lalube ya zauna shukali Sumayya ta Mika masa,ya karba suka faracin abincin Koh minutes uku basuyi ba sukaji sallaman yaro a kofarsu, "Kai wallahih nifa na gaji habba matan nan bazata samu lallen nan ba" Wace Mata Sumayya kardai kice min matar Bashir baki je kin Mata lallen ba?da mamaki yake tambayar ta "Nikam banje ba" Saboda me? "Saboda baka dawo ba,Kuma ni yanzun dare yayi" Amma sumy gobe nefa sunan Kuma baki je kin Mata ba,sannan yanzun Kuma kice kin fasa,baxataji d'adi ba in Kama mutum Alkawari Yana da kyau ka cika Kinga na riga nace wa Bashir zakizo kima matar sa lalle bazaiji Dadi ba in Kika ke zuwa Kuma gobe suna. Hakane kam, Sumayya tace tana fitowa waje Ina wuni Aunty?yaron ke gaida Sumayya "Lafiya ya mamarka"? Lafiya aunty Wai inji mamana inzo in fada Miki Wai don Allah kiye hakuri kizo ki Mata lalle ta nemi me lalle Bata samu ba Toh shikenan bara na d'auko hijabina, Sumayya tace tana shiga d'akin "Yayan khadija zanje lallen saina dawo ga abincin ka karasa ci"tace tana d'aukar hijab nata da jakan lalle purse ta bude 50k ta d'auka,zata fita a d'akin Toh baki karasa cin abincin ba? "Ah Ah Alhamdulillah kaci kaikam nikam sai nadawo" Sumayya muje na rakaki kinji?yace Yana mikewa "Ah ah ga yaro zamu tafi tare,sai dai kazo ka d'auke ni anjima" Kamar karfe nawa? "Kana da agogone"? Oho,nikam ki fad'amin. "Yanzun 8:12 zuwa 10:00 sai kazo ka d'auke ni" Toh shikenan yace Yana zama,d'aukar abincin yayi ya cigaba da ci Sumayya Kam fita tayi da yaron,sai da sukazo kusa da titin first bank taga shagunan a bude kamar Rana ga wuta ako ina,"tsaya Kai mu Shiga shagon nan" tace ma yaron tana Kama hannunsa suka tsallaka titi,shagon ta shiga"excuse me"tace ganin Mai shagon inyamurine Yes ma barka da zuwa shigo ciki customer ki duba Kaya Da mamaki sumayya ke kallonsa Ashe ya iyya hausa,yauwa "sannunka,Kaya nake so" Ok wani iri? "Jallabiyoyi" Ok ki shigo gasunan kizo ki zaba Wanda ya miki,yace Yana zazzaro Mata jallabiyoyi sunfi kala goma Guda uku sumayyaa ta zaba masu masifan kyau fari da baki Mai maiko sosai da hula sai Kuma Mai aiki ruwan sararen samaniya,takalmi ta sai Masa Mai kyau na tambarin Adidas silifas ne,sai t-shirt da 3quiter sai Jean's,sosai Sumayya Tama Al'ameen sayayya harda Turare na maza ta sai Masa da abin haske Kai da gemu,sai kusan 9:26 suka je gidan Matan da zatama lalle Lalle Sumayya ta Mata baki da ja, Al'ameen tun 10 yazo Amma Basu Gama ba,ya zauna Yana jiranta a kofar gidan Suna Gama lallen Sumayya ta karbi kudinta laidan da ta aje a kulle a gefe na kayan da ta saima Al'ameen ta saba,waje ta nufa Tana fita taga yayan khadija a zaune "Yayan khadija mu tafi Koh"tace Masa Kun gama? "Eh mun Gama" Ok yace Yana mikewa tafiya suke shuru,can dai Al'ameen ya kasa hakuri Jin yanda yakejin motsen laida a hannun Sumayya Sumayya nikam laidan menene a hannunki Kato haka don nasan dai laida kananu basa Kara haka? "Abu na saya"ta basa amsa Kala baice ba suka cigaba da tafiya har suka Isa gida,Dayake sunyi wanka dazun yasa Kaya kawai suka chanja Yauma kwanciya sukayi tare bayan Al'ameen ya Gama kwsan rabonsa Washe gari da safe bayan Al'ameen ya tafi masallaci, Ghana must go nasa ta bude Daman jiya ta kirga kayan jallabiya ukune sai wando da riga D'aya sai 3quiter D'aya sai armless D'aya sai gajeren wando biyu vest D'aya, kwasosu tayi ta juye a basket na dattin kayanta,sabbin kayanda ta suyo jiya ta mayar cikin bakkon ta shirye Kamar yanda kayan suke a kirge sauran Kuma ta aje sai Randa ya wanke kayansa biyu masu dattin saita musanya Masa, Vaseline insa da ya kusa karewa ta juye a laida daukar manda ta siyo Masa tayi ta diga a cikin gongomin kamar yanda baseline insa yake, Haka ma tamasa da sabulu Sai 6:30 Al'ameen ya shigo gidan Sumayya Kam ganin ya shigo d'akin da sauri ta d'auki takalmin sa ciny'ayyen ta saka Masa sabo,ta dawo d'akin,kudi ta basa 2k yasai musu dankalin turawa boket D'aya sai k'wai guda biyar, Fita yayi a d'akin bayan ya karbi kudin yazo ya zura takalminsa,sai Kuma ya cire da sauri,ya ringa laluben bakin dakalin Amma wayam baiji takalminsa ba Sumayya!!ya k'wala Mata Kira "Na'am"Sumayya ta amsa tana fita a d'akin itama Sumayya Banga takalmina ba pls ki duba mini Mana? "Ba gashinan a gefenka ba" tace tana kallonsa Wannan ba nawa bane "Nawa kenan?kadaisan banda takalmi irin wannan soson"? Amma ni sai inaji Kamar ba nawa bane,nawa fa da laushi sosai ya kode "Toh wannan in fa",ta tambaye sa tana mamakin fahimta irin nasa Kamar sabo sabo, "Hhhh lalle zaka tafi da kafa kenan tunda dai ga takalminka kace Wai ba naka ba" Sumayya bafa Wasa nake ba Wannan ba takalmina bane "Nidai naka na gani atoh"tace tana komawa d'akin Al'ameen Kam ba yanda ya iya Haka ya saka takalmin Amma har ransa yanaji ba nasa bane. Bayan fitar Al'ameen Sumayya aikace aikacen ta na gida ta Gama ta d'aura ruwan zafi a kittle. Al'ameen Kam bakin kasuwa yaje ya musu sayaya ya kamo hanyar gida Bayan Al'ameen ya dawo Sumayya ta soya dankali da k'wai sai ta hada musu tie, rufewa tayi ganin Al'ameen ya Shiga wanka Al'ameen aban d'aki mamakine ya kamasa Jin sabulunsa na kamshi ,Amma baiyi magana ba bayan ya fitoh, d'aki ya Shiga a hankali ya bude bakkon sa jallabiya D'aya ya zare a ciki ya zaro gajeren wando da vest. Sumayya na zaune akan kujeran tana kallonsa saka wando yayi da vest sai Kuma taga ya tsaya Yana tattaba vest in,Amma baiyi magana ba ya d'auki jallabiyar yasa,sai Kuma ya juye kayan bakkon duka a cafet Yana tattabasu. Sumayya!ya kirata "Na'am"tace tana kallonsa Sumayya wa'innan ba Kayana bane? "Akan me zakace haka" Sumayya wa'innan Sabine kijifa kayan kamshin sabbin Kaya suke bama Turare ba kiji da karfi fa kayan ba masu laushi irin nawa bane? "Nidai naka na gani" Sumayya me Kika sayo jiya da naji laida na kayo kayo a hannunki? "Ina ruwanka"ta basa Amsa Indai baki fad'amin gaskiya ba toh bazan fad'a Miki wacece kamila, menene hadin mu da ita ba Tabe fuska Sumayya tayi "Gaskiya n................