← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 104

Sashe 72

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sallah, gida suka koma suna shiga muhammad yaga yarinyar d'azun da safe zaune a gefe tana cin tuwo, kai koh d'an kwali babu. d'aga ido tayi ta kalli A l'ameen da sauri kuma ta mike, cikin fullaci tace, laa bako kaine ka tashi, ya jikin naka yau sai sauri nake nono na ya kare na dawo gida, Amma bai kare da wuri ba. Shuru Al'ameen yayi baiyi magana ba, yana nazarin yarinyar kenan khadijar sa zatafi yarinyar nan a yanzun, Allah sarki yaci burin ganin su duk da bai taba tunanin ganin sa zai dawo ba, Amma yaso ganin sa na farko yafara dasu, ganin yanda ta bata fuska alamu dai bataji dadin shurun da ya mata ba, gashi gidado na kusa dashi, yasa a hankali yace eh na tashi. Washe baki tayi sai kuma da sauri tace, nakai maka abincin ka d'aki bappa yace na kai. Kai ya fahimce yarinyar nan yar damuwace, fadi ba'a tambaye taba, kamar ya sata, rijiyar dake tsakar gidan ya nufa jan ruwa yayi a kwalla ya wuce bandaki, bayan ya d'auko kayan da zaisa, bai wani jimaba ya fitoh Alwalan isha yayi jin ana kiran sallah ya wuce masallaci. Bayan an idar da sallan gida ya nufa a hankali ya shige dakin da aka ware masa, zama yayi akan gadon kaba da aka saka A dakin, ya buga tagumi abin duniya ya dame sa, tunanin matarsa kawai yake, adaidai wannan lokacin ne suke cin abinci, shin itama abincin take cine koh me take yanzun? Gidado ne ya shigo dakin da sallama. Amsa masa muhammad yayi, tare da gyara zaman sa. Har yanxun bakaci abincin ba tsoho? Da mamaki muhammad ke kallon sa, tsoho kuma? Eh man tunda ka haifi bappa aikai tsohone, yace yana aje agushin hannunsa. Murmushi muhammad yayi sai yanzun ya tuna, ashe fa bappa yace sunan baban sa garesa. Abinci na kawo mu had'a muci, yace yana bubude agushi. Hannu kawai muhammad yasa a kwanon bawai don yana kwadayin cin abinda ke ciki ba, loma uku yayi ya tsame hannun sa, da mamaki gidado ke kallon sa, wai harka koshine koh me? Wallahi gidado bazan iyya ciba, gabaki daya na saba ci da mata na, muna ci muna hira gabaki d'aya yau dai ina jina wani iri. Hhh dayake kabar hannun wa'inda suka kamaka ba har kana zancen kewa . Dariya shima muhamad yayi yana kallon gidado, wai ni ya akai nazo gidan kune? Nine na tsintoka a ruwa, na kawo ka gida. D'agani kayi koh shanunka ne ya kawo ni? Nina d'agaka, mana. Da mamaki Al'ameen yace, kaika d'agani fa kace, yana mamakin yaron nan ne ya dagasa. Hh ka raina karfina kenan koh? Shuru yayi sai kuma ya girgiza kai Toh kaci abincin mana, in bazaka ciba sai nasa indo ta kawo maka nono. Kai na koshi, nagode gidado Haka gidado yaci sauran abincin, bayan sun fita waje muhammad ya wanke hannunsa yana kokarin koma wa daki don sam zaman gidan baimai ba, bayason zama a gidan da akwai mata, haka shi kuma yana tsakiyarsu gashi ba'a kewaye dakin sa akayi ba, babana!!!!yaji bappa ya kirasa. Na'am ya amsa yana nufo bappa, bayan ya zauna ne bappa ya mika masa maganguna, wannan na hayaki ne wannan na wanka, yanxun zaka d'auki kwalla ka jika zuwa safiya, zaka fara amfani sai wannan gadaline zaka, shiga daki da kanka zaka nika da duste zansa gidado ya kawo maka, ga mai saika zuba gadalin a ciki, kana shafawa safe da rana, sosai bappa ya had'awa muhammad magani karba yayi, yayi godiya. Kamar yanda bappa yace haka yayi, ya jika maganin ya had'a nasha, yana gamawa ya shiga ya kwanta abinsa, sai kuma kewar sumayya duk yabi ya cikasa ji yake kamar yayi tsuntsu ya gamsa a nigeria, koh hankalin sa zai kwanta sosai yake kewan gadon su, kewan jikin ta, abincin ta, fadar su,kamshin ta kome nata kewan sa yake, a haka daker bacci ya d'auke sa. ********************* sumayya fa jiki ya fara sauki kad'an duk da ba kwari yayi ba, Amma da sauki, sosai take samun kulawa a wajen mutanen nan guda uku, goggo Ammar da khadija duk da ba kula Ammar take ba, amma kullum sai yazo kuma inzai zo haka zai kawo mata abubuwa, su tsire koh kaza, sai dai su khadija suci, itakam bata iyya ci sam. Makwanta dayan unguwa, harda yan gidan Adara, sunzo dubata sosai ta cika da mamaki, haka customers nata ma sunzozzo kuma sosai suke rike wani abu in zasuzo, lallai sana'ar mutun nasa aga kimarsa,tunda lokacin da bata sana'a babu wanda ya lekota a asibiti, Amma yanzun kowa zuwa yake yana mata ya jiki, da jajen batar mijin ta, gashi yau satin ta biyu a gado, amma haryau zuwa ake, iyayen Ammar ma sunzo da kannen sa, baban sa ne kawai baizo ba. Kamar kullum yauma hakan take, da sallama ya shigo d'akin, hannunsa d'auke da laida jikin laidan duk raba da alamu dai wani abin mai sanyi ne. Khadija dake gefe ne ta Amsa masa tana tashi daga kan kujeran da take, ta koma gefen gadon ta zauna. Sumayya dake kwance, koh d'ago kai batayi ta dubesa ba, don tun akan wayanta ta daina bi takan sa. Sannu hajiya ya jikin? Shuru ta masa taki magana, sai khadija dake gefen tane takece masa jikin da sauki. Bude laidan da yazo dashi yayi, goran kunun ayane mai sanyi harda raba a jiki, gashi fari tass, ya mikawa khadija, gashi ki bata koh zata sha? Kaidai yaya Ammar baka gajiya wallahi, kullum ka kawo abu baci take ba, amma koh yaushe sai ka saya. Mom ina cefa tayi kunu, shine nece ta zubamin a gora guda biyar, zan kawowa sumayya tun jiya na aje a firij. Karba khadija tayi tana kallon sumayya dake kwance tana jinsu, Amma har lokacin bata d'ago ba, Aunty ga kunun aya mai sanyi. Shuru tayi sai kuma taji tana jin kwad'ayin sha, mikewa tayi a hankali ta karbi goran. Tsaya ta tsiyaye miki a kofi, Ammar yace ganin tana kokarin bude marfin. Koh magana sumayya batayi masa ba, tana bude goron a hankali tasa hancin ta mai tsayi a bakin goron tana tsuntsuna kunun, tare da lumshe ido, kunun sosai yake mata wani irin masifeffen kamshi, dake fita a ciki na aya da dabino. Habba sumayya menene haka?abinci kike tsuntsunawa hakan bai dace ba, babu kyau fa, yace yana mamakin abinda tayi kamar wata tababbiya. Kafa goran tayi da bismillah, ta fara sha shatake kamar yar kokowa da sauri sauri, tunda ta kafa goran sai da yayi rabi ta cire a bakinta tana hutawa,kafun ta sake kafa bakin ta akai sai gora ya rage babu kunu. Ammar da khadija tsakake sukayi suna kallon sumayya, ita da tafi sati biyu ana binta taci abinci, taki sai d'aura mata ruwa ake, duk an bubula mata jiki, Amma yau ba lallama ba banbaki, da kanta tasha kunu har goran faro medium. Sumayya kam ta kammala da gora d'aya, rike take da gora empty a hannu, tayi shuru amma fa har ranta kari take so, saidai tanajin kunyar tambayar wani,ganin Ammar in baibar d'akin ba. Bude laidan Ammar yayi ya fitar da wani goran kunu, tashi yayi da kansa ya mika mata, hade da karban empty na goran, ba tare da yayi magana ba ya koma ya zauna. Ba kunya sumayya ta bude goron ta kama sha, wannan karon kam a hankali take sha tana kurba kad'an kad'an har tayi rabin goran, kafun ta aje sauran a hankali ta koma ta kwanta. Ammar mikewa yayi ya kalli khadija, ke tashi muje waje zanyi magana dake, yana maganar yana fita waje. Tashi khadija tayi tabi bayansa, samunsa tayi tsaye a baranda yana jiran ta, karasowa tayi ta tsaya a gefen sa fuska ba walwala, kamar yanda taga yayi. Shin yayan ki nada abokan hammaya ne? Babu yayana baida wani abokin fad'a, asali ma yanda na tashi ban taba ganin yayana yayi koda cacan baki bane da wani. Ok toh akwai wanda yake nuna masa kii koh kyama haka? Gaskiya babu. Ok shikenan kawai, yace yana barin wajen ya nufi packing space, khadija ma cikin d'akin ta koma . Sumayya kam da tafiyan Ammar koh minutes 30 batayi ba, ta sake mikewa da sauri ta d'auki sauran kunun ayan ta shanye wanda ta rege a gora, kafun dare sumayya ta gama da gora biyar innan tas sai fitsari da take akai akai. Goggo data dawo karan kanta tasha mamakin kunun da yau sumayya tasha, amma batace kome ba. Da misalin karfe 2 sumayya ta farka da sauri ta mike zaune, jin wani irin azabebben yunwan kunun aya daya farkar da ita, sauka tayi a gadon ta nufi wajen empty in gorunan, bubudesu tayi tana kale a marfi tana sha, tsaban yanda take ji kamar bazata iyya bacci ba in bata sha ba. Da yake asibitin ba'a barin mutane fiye da d'aya da mara lafiya, yasa goggo barin khadija da sumayya a dakin ita ta koma wajen block in ta shimfida taburma ta kwanta, kamar yanda sauran yan uwan majinyata keyi, shiyasa buruntun sumayya, khadija ya tayar mikewa tayi a hankali tana kallon sumayya, Aunty lafiya? "Khadija kunun ayannan nake so, kuma ya kare" toh kiyi hakuri Aunty, zuwa da safe sai inje in sai miki, kinga yanzun dare yayi. Sumayya kam ji take yanzun in bata sha kunun nan ba zata mutu, mikewa tayi ta d'au hijab tanufi kofa. Aunty ina zaki kuma? "Neman kunu, ta bata amsa" A daren nan ina zamu samu wani kunu , don allah ki dawo bara nafita ni naje na saya miki. Dawowa sumayya tayi ta zauna a bakin gadon, ta d'auki goran kunu tana shinshinawa. Fita khadija tayi tun sumayya na tsammanin ganin ta har ta fara gajiya, ta jira kusan awa d'aya bata dawo ba, mikewa kawai tayi ta fita a dakin,ba tare da ta damu ba don yanzun damuwar ta kunu ne, ba dare ba,bakin get ta nufa daga ida sai hijab, data d'aura akan zanin ta sai takalmi koh kudin kunu ma bata d'auka ba a hakan ta nufi get. Security ne suka tare ta da mamaki, ganin zata fita da uwar daren nan, duk yanda taso su barta, ki sukayi itama taki koma
Chapter 72 · 0% Book details