← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 104

Sashe 83

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

~ Na ~
*Rukayya* *Ibrahim*
Page 8
Maciji ne babba duk da darene amma macijin fatarsa na sheki, Girgiza kai gidado yayi Alamu dai ba sarinsa yayi ba, da gudu Muhammad ya jawo wani katon reshen itace babba, ya bugawa macijin da karfi akai, ya sake buga masa take kan macijin ya wargaje, mikewa muhammad yayi ya taimaka wa gidado suka mike, ganin maciji a wajen yasa su cigaba da tafiya duk da dare ne, saida suka isa wani wajen yashi kafun suka yad'a zango, agun suka kwanta.
Basu suka farka ba sai washe gari, harma gari ya waye kafun suka farka, taimama sukayi, sukayi sallah zuwa lokacin hannun Muhammad yayi mugun kumbura sosai, badaru ne ya tsinko wani ganye ya mursuke yasaka masa a ciwon, mangoro suka tsinko mai yawa suka sha ga ruwan korama suka iba, sukaci gaba da tafiya.
A haka su Al'ameen sukayi ta tafiya kusan sati biyu, suna fasa hanya saidai su shiga wannan dajin su fita suyi wannan, gabaki d'aya wahala ya canja su, hannun Muhammad yayi dan sauki, kafafunsu tun yana musu rad'adi har suka saba, ga giransa daya tsage, da ace a garine dinki za'a masa, Amma haka sukaci gaba da tafi giran na warke wa, amma fa fatar bai hade ba sai yayi kamar tsagun wuka wajen yayi, sai yayi matikar karawa fuskar tasa kyau.
Saida su Al'ameen sukayi kusan wata biyu, suna tafiya a kafa bayan zama da sukad'anyi a wasu kauyuka, yaukam tsintar kansu sukayi a sahara mai zafin gaske, Allah yasa ma sunyi guzuri saboda kauyen da suka baro sun sanar dasu gabansu sahara ne, suna tsallake sa nijar zasu shiga.
*********
Ta bangaren sumayya basu farka ba sai
mangariba, Bathroom suka shiga sukayi Alwala, bayan sunyi sallah sumayya ta kalli khadija"ki shiga kitchen a cikin cefenen da kukayin nan ki d'auka ki dafa mana koh abu mara nauyi ne"
Toh Aunty khadija tace ta wuce wa kitchen in, dayake duk a falo yake basai ta fita waje ba flat ne babba, khadija na shiga kitchen saiga yar laila mai shekara biyar ta shigo d'akin da sallama
Amsa mata sumayya tayi ta karbi kulan da ke hannunta, ina kwana aunty, ta gaida sumayya.
Murmushi sumayya tayi tace"Ina wuni dai baby"
Ina wuni?
"Lafiya munira, Dady ya dawa koh?
Eh ya dawo gashi momy ta bani na kawo miki, tace tana mikawa sumayya kulan
" wai gaskiya mungode wa momy kinji kice nama dady sannu da zuwa.
Toh yarinyar tace tana fita a falon, kwalama khadija kira sumayya tayi, bayan ta fitoh ne sumayya kece mata, Laila ta kawo musu abinci tabar girkin, ta d'auko musu pure water biyu dake kitchen in, A plate d'aya sumayya ta zuba musu abincin, tuwo ne miyar shuwaka da kifi busheshe, sosai sukaci tuwon suka sha ruwa tashi khadija tayi tarufe musu kofar falon, tabar kee a jikin kofar wanka sukayi dayake Abuja akwai nepa yasa ta kunna AC dake makale a falo, don sunyi sa'a akwai Ac a falo, shiyasa sumayya tace susa katifa a falon in, kwanciya sukayi akatifarsu.
Washe gari tie da kwai suka karya dashi khadija ta wanke musu d'an plate insu da kwanon laila,khadija ce ta maida mata kwanukan da safe, sumayya had'a laila tayi da khadija da zata fita aiki akan suje ta kai khadija makarantar da yaranta ke zuwa, tunda transfer ne ba sabon register zatayi ba.
Khadija ta samu gurbin karatu a school in, sai dai fa kudin makaranta 50k ne duk team nan ma wai makaranta daidai gwargwado kenan,sai kudin school bus, a ranan suka bawa khadija uniform nata Daman tazo da kome na makarantan ta harda note book, shiyasa washe gari da safe tana karyawa ta sanya uniform nata, siket ne da riga sai necktie da baby hijab, bayan khadija ta tafi makaranta dayake school bus na jiranta a bakin titi, Karyawa sumayya tayi ta koma ta kwanta tama rasa me zata kama, ta gaji da zama waje d'aya tashi tayi ta shirya ta fita, da kwatance taje clinic don yanzun cikin na neman 4 months shiyasa takeson fara zuwa awo abinka da yar boko dakanta, ta gane asibitin, ta bude file a wajen sannan zatana zuwa clinic harta haihu, daga asibiti kasuwa ta wuce tad'an saisai musu kayan masarufi.
Bayan ta dawo wanka tayi ta dafa musu abinci sai yamma khadija ta dawo, uniform nata ta wanke ta had'a da kayanda Auntin ta ta saka jiya, tayi moping tayi musu girkin dare, yayin da sumayya ke kwance akan katifa tana kallo a system nata.
Bayan mangari ba saiga laila ta shigo lokacin sumayya da khadija nacin abinci a kasan tiles, sumayya na zaune akan filo saboda yanayin ta da ba'aso ta dabasu a kasa.
Ah ah hajiya sumy haka ake makwantakan koh nokin babu.
"Kai laila kin cika iyayi maigida ya dawo basai mu baku waje ku sarara ba, tukunna"
Karasowa falon laila tayi, lallai ma sumayya wani irin bamu waje, kaman sabbin aure
Ina kwana Maman munira?
Lafiya khadija ya school in?
Lafiya klau, tace tana iban abinci a wani plate ta wuce daki.
"Kai laila ga abinci bismillah"
Zama tayi a bakin katifar, sumayya nayi magana da baban munira yace min za'a samu shago, amma nidai gaskiya sumayya hankalina bai kama ki bude shago yanzun ba, duba da halinda kike ciki ba
[10/24, 2:18 PM] +234 903 356 9641:
*MATAR MAKAHO*
Chapter 83 · 0% Book details