← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 104

Sashe 42

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Koh ganinta basu samuyi ba duk abokansa yanzun basa son Koh zama waje d'aya tare dashi kowa gudunsa yake Bayan waec ya fitoh Salim ne ya karbo Masa result,ya samu 9credit sosai Al'ameen ya rungume result nasa a kirji Yana hawaye,yaci buri akan result nan yayi karatu har bacci bayayi,Ashe ba rabon zaiga abinda ya samu ma da idanunsa sai an duba an fad'a Masa. Rayuwa fa Tama su Al'ameen zafi don abinda zasuci ma ya zamo musu aiki sai salim ya fita ya nema kafun su samu gashi yanzun an sallame Al'ameen a shagon da yake zama don ganin baida ido duk yanda yaso su taimake sa zai iyya ciniki koda ba idone abin ya gagara Bayan wata D'aya da makantar Al'ameen yaje gidansu kamila yafi kafa goma Amma kullum sai ace Masa Batanan,Wasa Wasa jikin Salim ya Tashi don ba'a je ganin likita ba har wata ya wuce,ganin ciwo yaci karfin Salim ga bamai taimakonsu, yasa Al'ameen neman taimakon yaran unguwa suka kaisa asibiti Likita yace Masa wannan karon aiki za'a ma Salim gashe kudi masu yawane,sosai hankalinsa ya Tashi ga rashin ido gashi basuda abinda zasu Kama su sayar sai sarkanda mahaifinsa ya bar Masa Wanda shi kad'aine abinda yake gani a matsayen Abu Mai girma da muhimmaci a Rayuwansa Wanda zai buga kirji yace Awajen iyayensa ya gada,Amma baikai Dan uwansa ba muhimmaci ba. Haka ya d'auki sarkan yakai kasuwa don a Saya Amma masu sarka sukace bazasu Saya ba gudun karsu sayi abin sata bare sarka Mai shaki Kamar Wannan Basu taba ganin sarka Mai zubinsa ba Duk inda Al'ameen yasan zai samu a taimaka Masa yaje Amma babu Wanda yayi yunkurin taimakon sa har gidansu kamila yaje Amma Koh sauraron sa mahaifinta baiyi ba Karshe dai Koran su akayi a asibiti ganin Basu da Koh sisi kullum Kuma kudin gado karuwa yake,dawowar Salim gida ciwo ya Kara Tashi gadan gadan,haka Al'ameen yanaji Yana gani jikin Salim na tsanani Amma Babu yanda zaiyi haka yake fama ga rashin ido Yauma Kamar kullum suna kwance a d'akinsu Wanda kakansu ya mutu ya barmusu tun 1:00 na dare jikin Salim ya tashi ko rimtsawa Basu samu sunyi ba dukansu biyu Al'ameen na zaune Salim ya kwantar da kansa akan cinyar D'an uwansa sosai yake Aman jini Al'ameen Kam sai kuka yake Yana Kara tallafar Kan D'an uwansa Jin Aman da Salim keyi Yana karnin jini yasaka yatsansa ya lakuto Aman tsuntsunawa yayi tabbas jinine ba Wai ba, ai da gudu ya fita tsakar gidan Yana kuka Yana bubuga musu kofa Amma ba Wanda ya taimaka Masa Asalima zaginsa suke,insun bude kofar,da gudu yayi waje. gidan makwancinsu ya shiga Yana kuka ya ringa buga masu kofa,mutumin na budewa yaga Al'ameen ne,hakika yau yaji tausayin yaran da gudu ya Kama Al'ameen sukaye cikin gidan Jin Al'ameen nace Masa Salim na Aman jini Suna isowa zuwa lokacin salim kam jiki yayi tsamare sosai haka mutumin ya cicibesa Al'ameen na binsa a baya sai tuntube yake Yana buga kafarsa saboda rashin sandar jagora Koh D'an jagora A haka suka fitoh kofar gidan, aje Salim mutumin yayi yace bara ya d'auko machine su kaisa hospital Mutumin na shiga gidansa Salim ya ringa Kiran sunan Al'ameen Yana tari jini nabin Gefen bakinsa,Yaya Muhammad !!Yaya muhammad zuciya na, zuciya na na ciwo Yaya kamin fifita zafi nakeji a jikina Yaya bana ganinka Yaya zansha ruwa kishi nakeji gabaki d'aya Al'ameen ya rude iyya rudewa da gudu ya ruga yayi randar masallaci saboda rashin jagora, ya hadu da pol ji kake Gauu ya buga goshinsa jini ya balle Masa duk irin azabar da yaji hakan baisa ya kasa tashi ba haka ya mike a daddafe yayi randar masallaci dumbulo ruwa yayi Yana kuka Yana sauri ya karaso kusa da Salim tsungunawa yayi ya d'ago kansa jikinsa na rawa Jin Salim ya daina kakarin Amai gashi kansa yayi nauyi daker ya d'agasa ya d'aura akan cinyarsa lalubar bakin salim yayi ya kafa Masa mod'an Amma Ina ruwa baya tafiya sai bin Gefen bakin yake Yana zuba,dagajin haka Al'ameen ya k'wala Kara Yayi daidai da lokacin mutumin ya fitoh da machine da sauri ya karaso gunsu Jin ihun Al'ameen Yana zuwa cikin hanzari ya haska su idonsa ya sauka akan Salim kwance ido ya kafe a sama jiki a sake Wanda Koh ba'a fad'a ba yasan lokacin Salim ne yayi Innalilahih wainnailaihir rajuun kalmarda ta fitoh a bakinsa kenan Aiko Wannan kalmar ita ta Kara tabbatar wa Al'ameen lallai ya rasa kaninsa, a karo na uku Yana rasa mutanen da sukafi soyowa a ransa, farin cikinsa,duka a gabansa suka Amsa Kiran mahalincin su(Allah Kasa mu cika da imani,muyi kyakkyawan karshe) Ji kawai mutumin yayi Al'ameen ya Fad'i timmmmmm............. *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara* *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* *Na tsunguno(habil)* *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* ) *Turaren turara jiki after birth* , *Na d'aki(halud Al'oud)* *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* Contact them vie 08028827241 or 09033791049 IG @umsadincense *MATAR MAKAHO*
Chapter 42 · 0% Book details