← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 104

Sashe 89

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

tafiya bayan sunyi sallama da sumayya tsayawa yayi a waje get, kamar minutes 5 da fitar sa khadija ta mike zata fita a falon. "Ina zaki kuma khadija"? Aunty zan tattaro shanya nane naga garin da hadiri? "Ah ah kidai tattaro shanyar, Amma garin nan kam ba hadiri bayan yanzun damuna ta wuce" Jin Abinda sumayya tace yasa khadija sunkuyar da kai, ta fice a falon da sauri ta nufi igiya ta dauko hijab nata, tayi get, tana bude get in aiko kamar yanda ta zata inne Kalamu na tsaye, kai lafiya tun a falo sai ketket-ta mini ido kake? Wallahi khadija magana nake so nayi dake daman. Da mamaki da kallesa au yau kuma kunyar Aunty kake ji kome? Ah ah ba haka bane kinsan next week zamu fara exam? so bazan samu daman shigowa ba shiyasa na kawo miki wannan, yace yana mika mata bakin laidar dake hannunsa. Ba musu khadija ta karba hade da tambayar sa menene a ciki? Wayace harda sim, na miki register sai muna gaisawa daidai na samu zama, don zan kwana biyu gaskiya bazan leko ba? Kaga karbi abinka wallahi babu ruwana? Kamar yaya ba ruwanki khadija? Kamar yanda nace maka, so kake Aunty taga rashin kyauta wata gareta? tayi mini dukkan kyautatawa baika mata na nuna mata rashin godiyan Allah ba. Yanzun khadija karbar wayar ce rashin godiyan Allah? Kayi hakuri Amma bazan iyya karba ba sai dai in zaka kaiwa Aunty da kanka ka bata? Babu damuwa muje na batan. Ah ah wallahi ka fara zuwa dai kaikad'ai kar tace mun had'a baki, tana maganar ta koma cikin compound in tana tattara shanyar ta. Ba musu Kalamu ya koma kofar sumayya, da mamaki take tambayar sa lafiya kuwa ya dawo?bayani ya mata akan waya ya baiwa khadija taki karba shine ya kawo mata koh khadijan zata yarda ta karba? Da mamaki sumayya ta karbi wayar ta bude, wayane sumsung Galaxy S9+" Kalamu nima karan kaina nayi tunanin saya wa khadija waya, Amma nafi son saita kammala secondary ta mallaki hankalin kanta" Aunty yanzun ma khadija tayi hankali fa, shekara 19 take nema wasu a shekarun tan nan ma, suna jami'a don Allah aunty ki barta ta rike wannan in? "Au haka ta fad'a maka kenan bazan barta ta rike ba, kuka had'a baki kazo waje na koh"? Ah ah aunty kawai dai na fahimci khadija nada biyayya ne. "Shikenan Allah ya sanya Albarka, harda shekarunta ta fad'a maka kenan"? Ameen Aunty Amma nidai kiyastawa nayi bata fad'a mini ba, yace cikin murna ya fita ganin Aunty ta karbi wayar, yana fita a falo yakusa cin karo da khadija dake makale a kofar falo tana sauraron su, cikin murna tace Aunty ta yarda? Kai kawai ya d'aga mata ya wuce get ya fita, Khadija kam kasa komawa cikin falon tayi, taci gaba da tsayuwa a bakin kofa. Sumayya dake jiran Khadija ta shigo, shuru shuru bata shigo ba, yasata mikewa fuska a had'e ta nufi kofar falon....... ************* Jikin muhammad sai rawa yake yaje ya karbo wasu kayan, ya karbo sabon shayi, ya sake shigowa falon wannan karon tsohowar ce da yara biyun, wanda d'ayan bai manta sunan taba muhibbat sai karamar , gaida tsohowar yayi ya wuce falon sarki, Wannan karo sarkin baya falo yana ciki, aje masa shayin yayi a table ya tsaya a gefe, kusan 30 minutes kafun ya fitoh yauma kamar kullum fuska a rufe,, a take gaban Al'ameen ya soma bugawa da karfin gaske, zama sarkin yayi a hankali akan d'aya daga cikin kujerun falon, da sauri Al'ameen ya dukar da kansa a hankali ya matso da table in ya siyaye masa shayi hade da gaidashi, hannu kawai sarki ya d'aga masa ba tare da yayi magana ba. Yana gama had'a shayin, ya fita a falon, direct kitchen in shayi ya koma, yama abokan aikin sa sallama duk da lokacin tashi baiyi ba, ya kama hanyar gida, cikin hanzari yake tafiya har ya iso bakin titi tare abin hawa yayi. Yana isa gidan cikin hanzari ya bude kofa bakin sa d'auke da sallama, baikara saba sallamar ya makale masa a wuya, ganin baba tsaye akan kafafunsa........... Ruqeenjalal [10/24, 2:18 PM] +234 903 356 9641: *MATAR MAKAHO*
Chapter 89 · 0% Book details