← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 104

Sashe 77

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aikin ki, ki Amince mu koma gida tare. Kara khadija ta sake da karfi, hade da kuka wayyo na shiga uku don Allah kuyi hakuri, wallahi yayana na sonta babu abinda baya mata, kuma ba mutumin banza bane, don Allah karku rabasu da Aunty, wallahi nima ina son zama da ita. "Kiyi shuru khadija koda Al'ameen bazai dawo ba, ni bazan taba barin gidan nan ba, koda na bari toh ba gidan shugaba zan koma ba, ku fita ku barmin gida banason ganin ku, nace ku fita"tayi maganar cikin karfi sai kuma ta sulale ta zube a kasa sumemmeya. After 6 hour's sumayya ce kwance a gado an d'aura mata ruwa a hannu, sai khadija dake gefen ta a zaune idanu jahur, sai Ammar dake gefe shima a zaune, cikin tashin hankali. A hankali sumayya takalli ammar " sun tafi"? Ah ah sumayya basu tafi ba tunda aka kawoki suke zaune a asibitin nan, yanzun ma sunso shiga likitane ya hana, kamar yanda kikace saboda yanayin bp ki, sumayya duk da bansan meke faruwa ba, nasan tabbas iyayen kine su, kuma iyaye darajane dasu baikama ta ki musu abinda kikayin nan ba, sannan abinda ya tsayamin a wuya, abin mamaki daman ba auren soyayya kukayi da Al'ameen ba? Don nasan sone kawai zaisa ke dashi ku kasance a karkashin inuwa d'aya, duba da duniyar mu ayau mai kudi sai mai kudi miskini sai miskini, talaka sai talaka Amma ke kullun sai na kwana da lamarin ku keda muhammad A raina, a yanda na ganku naga tsantsan kula da juna da soyayya, gaki kyakkyawa ruwan manya, kullun saina tambaye kaina taya kika aure muhammad?Amma Amsa d'aya nake samu soyayyace , don Allah yau ki fad'amin wani abu game dake koh muhammad, koh nima zansamu na kunce kullin dake damuna akanki. Hmm Ajiyar zuciya sumayya tayi, sannan a hankali ta bude baki"yau zan sanar dakai wacece sumayya Abdusalam Shugaba, ada kafun ta zamo MATAR MAKAHO........... *MATAR MAKAHO* ~ Na ~ *Rukayya Ibrahim* page7 Abdul'aziz wanda aka fi sani da shugaba, haifafen mambila plateau(Gembu) ne, Ainahin su fulanin gembu ne, acan aka haifi Abdul'aziz,duk da yana kauye hakan bai hana shugaba karatu ba, yayi karatun sa na secondary kafun yayi aure, matar sa ta farko fatima wance ake kira da fa'i, ita ma yar gembu ce, auren dangi aka musu, kafun daga baya ya aure sumayya (Dada), a kauyen su yake rayuwar sa da matan sa biyu,da yaransa maza biyar, yaran fa'i uku, Abdul'aziz mai sunan babansa(babuji)sai Abubakar da gaddafi,sumayya(dada)nada maza biyu itama, Usmanu sai Abdulsalam(Abie)shine autar gidan su, akwai kyakkyawar fahimta da zaman lafiya agidan, shugaba(Abdul'aziz)hakan ya samu asaline daga zaman lafiyar da matan keyi, zamane na kwatance a kauyen su, kaf kauyen babu gidan da zaka shiga kayi mamakin zaman kishiyoyi iri na gidan shugaba, sosai abin ke bawa wasu mazan sha'awa, don shugaba adaline a gidan sa, duk da auren soyayya sukayi da sumayya hakan baisa ya nunawa fa'i banbanci ba. bayan wasu shekaru an samu fad'an kabilanci a gembu sosai,tsakanin mambilawa da fulani wanda yazamo sanadin mutuwar fatima uwargidan shugaba, da mahaifiyar shugaba, daman mahaifinsa ya jima da rasuwa, wasu da dama a yan uwansa sun rasa ransu, a rikicin da ya afku. Bayan kome ya daidaita, shugaba ya saida duk wani kadara nasa na kauye wanda mahaifinsa ya mutu ya bar masa, don shikad'ai babansa ya haifa namiji sauran matane kuma duk sunyi aure, ya dandanka musu nasu gadon. Jalingo babban birnin jahar Taraba, ya tattara iyalansa suka dawo jalingo, gida madaidaici shugaba ya saya, yasa yaransa a makaranta, dada tana kula dasu kamar y'ay'anta na cikin ta, sam bata nuna musu banbanci da nata duk d'aya ta d'auke su, wannan abin shiya kara dasa soyayyar ta, a zuciyar mijinta. Bayan wasu shekaru kudi sosai ya fara zama a Aljuhun shugaba, don business yake na manya manyan shaguna zanunuwa a kasuwa yana order daga kano, aje aje yakoma na mototi, Arziki kullum gaba gaba yake ga yaransa na makaranta, duk wanda ya gama secondary, kwasar waje yake turasa karatu. Lokacin da yaransa suka fara nisa a boko , hakan yasa ya sakar musu wasu kud'ad'e su gwada tasu kasuwar, babuji da Abubakar sune suka fara kammala karatu, suka fad'a business abinka da yan boko, kuma kwararu a bangaren business, kankace kome kudine ya zauna company suka kafa mai zaman kansa, tare da haden gwuwar junan su, sosai arzikin su ya fantsama. Babuji da Abubakar a rana d'aya sukayi aure , wasu yaran jalingo suka aura wa'inda suka hadu a makaranta, bayan auren su, saida suka haifi yara bibbiyu, kafun gaddafi da Usman sukayi aure. Abdulsalam ya kammala karatunsa Amma sam yaki aure kaman yan uwansa, duk yanda iyayen sa sukaso yayi sai abin yaki, dada har magani take saka masa a abinci koh Aljanane ta aura mata yaro, Amma ina shuru abu yaki kowa aka nuna masa yace baya so, bata masa ba hardai su gaddafi suma suka hayayyafa sosai , a lokacin yaran babuji biyar, na Abubakar uku, yaran gaddafi biyu, na usman hudu. Bayan wasu yan shekaru shugaba ya kwanta ciwo, baiyi wani dogon jinya ba Allah ya karbi rayuwansa, gadon da aka raba musu shi suka had'a suka gina katafaren gida a unguwan specialist, gabaki d'ayan su suka tattaro kan iyalansu suka dawo cikin gidan da zama, don a lokacin Babuji da Abubakar suna da company kansu har biyu, yayinda gaddafi yake aikin goverment, usmanu d'an siyasa ne, Auta Abdulsalam shi ma'aikacin Bank ne(Accounter)kasance warsu rikankun yan boko ga naira ga kyau, kowa yasan yanda fulanin gembu keda tsananin kyau. Rayuwa ake a cikin shugaba family house mai kyau, daban sha'awa, mazan basu bawa matansu daman da zasu kawo musu tashin hankali ba sam, koh kara kika kaiwa mijinki matar wansa ta miki kaxa, had'a meeting ake a kira kowa, ku maida maganar hakan yasa matan sam suka daina fad'awa mazajen su, saidai ayi iyya mata da mata kasa kasa. Auren Abdulsalam ne yaxo musu da sabon salo, saboda yarinyar da ya kawo akan ita zai aura, yar maiduguri ne Amma tana karatu a TSU, tazo bank inda yake aiki cire kudi, Allah ya had'asu kanuri ce, hakan yasa dada tace ita sam bata yarda da auren nan ba, bazasu aure babarbariya ba, abinda ya xamo cecekuce a gidan kenan, duk yanda Abdulsalam yaso fahimtar da ita son da yake ma yarinyar, abu yaci tura sam taki Amince wa katafau tace bata yarda ba, shikuma Abdilsalam yace muddin ya rabu da Hafsa toh shikam bazaiyi aure ba. Aijin haka yad'agawa dada hankali don tasan sarai halin Abdulsalam, akwai kafiya kamar me, tayaya ma aka samu ya samo hafsar kullum yace yakusa aure shuru baiyi ba, bare yanzu yace bazaiyi ba ai magana ta lalace. Babu yanda ta iyya da banbakin su babuji ta Amince da auren hafsa, har maiduguri akaje da zancen auren. su karan kansu iyayen ta sunso gardama amma ganin sannanen family ne, yasasu karbansu da hannu bibbiyu, tare da kafa sharadin yarsu zata cigaba da karatu insun amince, zasu basu ita? Amincewa kam sunyi saboda kaf gidan shugaba yan boko ne, hatta matan gidan na zuwa aiki, rainon yara ma dada keyi da masu aiki. BAYAN AURE Hafsa fa ta fara fuskan tan banbancin launi a gidan su Abdulsalam, kasancewar ta baka kuma kanuri, sabanin yan gidan shugaba farare ne, daga matansu har maza da yara gasu fulani kyawawa, don Abdulsalam baza'ace kyaune ya rud'asa akan hafsa ba, ah ah sonta ne kawai Allah ya diga masa a zuciyar sa yaji baya ganin kyaun kowace mace sai nata, sosai ake nuna mata banbanci kuma ba wanda ya fara asasa hakan sai dada, haka zasu zauna suna hira daga sun ganta zasu koma yi da yare basa janta a jiki, inta matso garesu basa sonta rabesu sam, kansu a hade Amma ita sun ware ta. Hakan dasuke, yama hafsa zafi, yasata watsar da kowa na gidan, ta kama karatunta daga ta dawo makaranta ta shiga kitchen tayi girkinta, zata haura upstair's, ta shiga d'aki bata fita sai mijinta ya dawo. Abdulsalam yasha had'a meeting da korafi akan abinda akema matar sa, duk da bata fad'a masa ba, yaga alama yayunsa mazane kad'ai ke sonta. A haka fa abu yaki chanjawa abubuwa sai cigaba suke a haka, hafsa zaman hakuri take a gidan, babu zagi babu duka, Amma ana nuna mata mugun hali kam, a hakan cikin hukuncin Allah ta samu ciki, wanda kaf gidan babu mai farin ciki sai ita da mijin ta da yan uwan mijinta, amma babu ruwan matan dasu dada da ita, gashe cikin yazo mata da laulayi, bata iyya aikin kome, kuma babu mai taimakon ta, karshe dai Abdulsalam d'aukar hutu yayi a bank ya zauna a gida yana kula da matar sa, amma abu yaki karshe dai kiran iyayen ta yayi aka turo masa kanwar hafsa, tazo ta zauna da ita har cikin ya tsufa bata koma ba. Wata ranan Alhamis hafsa ta tashi da nakuda tsakar dare, Abdulsalam da kanwar hafsa ne, suka kaita asibiti don baiko sanar da yan gidan tana nakuda ba, hospital aka kaita kafun asuba Ta santalo yarta kyakkaywa fara tas, jinin gembu mai tsananin kama da zuriyar gidansu, koh kama da hafsa batayi kome na babanta ne. Sosai Abdul yayi farin cikin samun wannan baby, ga wani irin sonta daya ke sosai yaji son babyn sa, washe gari ne yan gidan suka tashi sukejin labarin haihuwar a bakin mazajen su, Dada da matan sunje asibiti bada son ransu ba, saidai ganin yanda Abdulsalam yahad'a wa kowa fuska, gaisuwa ma dada kawai ya gaishar, ya shiga yad'auko kayan baby ya fita, hakan yasan su zuwa duba baby. Ba karamin dadi sukaji ba ganin yarinya kamar su ta biyo, bama kamar dada a murna, zama tayi a asibitin taki tafiya ita kema yarinya wanka, duk da yar uwar hafsa tazo washe gari Amma dada ta karbi kome na baby, harsuka koma gida dada fa na leke da yarinya, ranan suna yarinya taci sunan dada sumayya ana kiranta da momcy, haihuwar sumayya shine musababin zaman lafiyar hafsa, sosai taga change agun dada haka ma matan gidan, sosai suka koma damawa da ita, itama bata rikesu a rai ba, a sannu sannu har itama ta fara
Chapter 77 · 0% Book details