Sashe 9
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta tashi tazo ta taimaka mini ta shimfida mini Sallayan da tazo dashi ta shimfida mini ta Mika min hijab na saka na Tada sallah harda na asuba na biya,ina idar wa na cire hijab in, Khadija ta mikamin hula nasa, na tashi na koma Kan gadon dukansu sukaimin sannu har suna hada baki, Khadija takalminta ta saka Wanda na cire ta bawa Al'ameen nasa, Abinci ta iba min a plate ta Miko mini, "Khadija bawa yayanki abincin nan bazan iyya ci ba bakina ba Dadi Sam" Ah ah Sumayya ki karbi abinci kici ai ba'a jinya sai da abinci" Al'ameen yace Gaskiya ne Aunty rabonki da abinci tun jiya fa,ta fada tana aje mini, "Wallahih Khadija bazan iyya ci ba kidai Mika mini ayabar nan naci" Toh Aunty, Ayaban ta bani na samu naci uku ta Mika mini fresh milk in da tazo dashi daga gida nasha rabi Plate na abincin da ta bani ta Mika Masa karba yayi Bismillah ya fara ci, "Khadija ya Naga kin zauna ki ibi abinci kici Mana" na Bata umurni Iba tayi ta faraci, Yana Gama cin abinci ruwan gora daya Khadija ta bashi yasha, Khadija ki zauna da Aunty ki bara na fita sai na dawo,ya fada Yana tashi yayi hanyar waje, Toh yaya Allah ya bada sa'a ...... Ameen Khadija Nidai da ido na bisa harya fita na juya Ina kallon Khadija" Khadija waya biya kudin magangunan nan Naga harda ruwa duka"? Nima ban sani ba Aunty yanzun nazo sai dai ki tambayi Yaya, **Shuru kawai nayi na koma na kwanta Al'ameen Bai Dade da fita ba, sai ga wani matashin saurayi baki k'yakk'yawa Mai matsakaicin tsayi da jiki ya shigo dakin mu da sallama a bakinsa Amsawa Khadija tayi nikam hannu nasa na dauki hijabina da na cire a jikin karfen gado nasa, Shigowa yayi ,barka kudai ya jiki Sumayya? Mamakine ya kamani Ina kuma wannan bawan Allah ya sanni, "Da sauki Alhamdulillah" Allah ya kara sauwa kewa "Ameen" nace Al'ameen ya fitane? Eh wallahih yanzun ya fita baku hadu ba? Khadija ta basa amsa Ah ah bamu hadu ba, Koh Kaine Ammar? Nine Hala lbrna ya baki haka kikayi saurin gane ni? Eh yadai fadamin abin alkhari da ka Mana Allah ya kara bude, ...Ameen Nidai shuru nayi na barsa da Khadija suna Hira Kamar Wanda suka San juna, Khadija nikam Inaga Zan gudu fa har yanzun Al'ameen Bai dawo ba gashi Ina son muyi sallama tafiya ne ta kamani wallahih gobe Zan wuce shiyasa naso mu hadu kafun na wuce, Yace Yana zaro kudi a Aljuhunsa Yana mikawa Khadija ga wannan ba yawa a saiwa mara lfy lemo in yayan naki ya dawo kice Ina gaishe she , Mungode Allah ya saka Kuma zaiji sakon ka, Allah yasa yace Yana kokarin nufar kofa "Nagode" nace masa ba tare da na dago ba ganin irin kallona da yake tayi kamar ya samu TV tun dazun da suke hira da Khadija idonsa na kaina, Ba kome yace yasa Kai ya fita......... My WhatsApp number *MATAR MAKAHO* ~ Na ~ *Rukayya Ibrahim* Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa Free book Page 1 Bayan fitar Ammar Khadija ta kirga kudin dubu goma ne,Mika min tayi, Aunty ga kudin "Ajjye Khadija in yayanki yazo ki basa tunda shike fama da zirga zirgan asibiti" toh Aunty ta bani Amsa tana aje kudin a cikin ak'watin Kayana, Al'ameen na fita daga asibiti da kafa ya koma har gida Dayake akwai sanda in Kuma yazo titi sai ya Kama yara su tsallakar dashi Yana Isa unguwan su(sintali) wajen shagunan bakin titi ta inda yake sai da mangoro a bakin su, Shagon malam shu'aibu ya fara zuwa don shine yafi masu shagunan abin arziki sosai alayin da sallama a bakinsa ya shiga shagon, Assalamu alaikum malam shu'aibu Waalaikumu salam Mai mangoro ne? Eh nine malam shu'aibu barka da jama'a Barka dai lafiya Kam Naga yau tun safe danazo bude shago Naga hulbairon ka a rufe dazun na aiki yaron gidana ya karbo mini yako yake fadamin baka nan? Eh wallahih malam shu'aibu iyalina ne ba lfy jiya na kaita asibiti, Allah sarki ya jikin nata? Da sauki Daman nace bara nazo ka taimaka mini da kudi dubu hamsin za'a Mata aikine appendix ya kumbura a cikin ta don Allah ka taima kamin, Kutt lallai ma a karnin nan da kowa ke takai takai Ina Zan iyya daukan kudi har 50k na baka da sunan bashi, bayan anyi operation in Ina zaka samu kudina ka biyani, gaskiya bazan boye maka ba ni nan Koh biyar bazan iyya baka ba banaji ance Yar masu kudi aka aura maka ba me yasa danginta bazasu Mata jinya ba tunda sunsan baka dashi Daman suka baka ita Shikinan malam shu'aibu na gode, ya fada Yana fita ba tare da ya basa amsar tambayar Saba, D'ayan shagon Al'ameen ya shiga shagon gwanja bayan sun gaisa shima ya rokesa Koh zai samu bashin kudi Amma Kai dai wallahih D'an rainin wayo ne ya Ina Saida kayan Miya zakace na baka dubu hamsin duk kayan shagon nan aka sayar Ina zaiyi dubu hamsin, Haka yayita bin shagunan makwantansa Amma ba Wanda ya basa Koh sisi wasu kamma da bakar magana suke binsa dashi, A haka ya iso shagon Haladu shima yace baidashi,. Wajen bairon mangoron sa yaje ya bude ya tataba mangoron rabi duk sun lalace saboda yini da sukayi a rana Kuma a rufe, zabe masu kyau yayi Yana, D'auka yana sawa a k'wando ya shiga shagon Haladu dashi, Yana cewa, don Allah Haladu Koh zaka sayar mini da mangoro na zanje na zauna a asibiti na kwana biyu daidai Matata taji sauki Gaskiya bazan iyya sayar maka ba sai dai na saya kawai na sayar Nima na samu D'an riba, Ba damuwa Al'ameen yace Masa .....Nawane mangoron? D'ari takwas da hansim .....Zan baka dari biyar don Naga wasu sunyi laushi? Ba damuwa Allah ya saka musu albarka ......Ameen Kudin Haladu ya basa ya karba gida ya shiga ya bude kofar, da yake ya karbi key a hannun Khadija wanka yayi ya saka kayansa Jin ana Kiran la'asar yayi Alwala ya lalube takalmin Sumayya ya fita dashi a hannunsa, masallaci ya tafi yayi sallah ya wuce asibiti duk zuciyansa ba Dadi ya rasa wajen wa zai tinkara da zancen kudi,, yasan Koh mutuwa zaiyi Yan gidansu bazasu taimaka Masa ba bare Sumayya matar sa, ***Muna nan da Khadija har la'asar sallah mukayi dukan mu nurse tazo ta mayar mini da laidar ruwan a hannu na, Na kwanta baccine ya dauken nabar Khadija na zaune, Ya iso asibitin da sallama ya shigo dakin Khadija ta amsa masa. Sannu yaya ka dawo? Eh Khadija Toh yaya ka samu kudin? Wallahih Khadija sai addu'a naira 500 ne kadai na samu Amma yaya ya kamata ka sanar da Aunty gaskiya don wallahih Yaya Ina Jin tsoro kaga ance appendix in ya kumbura fa tunda Allah Bai baka ikon samu ba, ka fada Mata ita sai ta biya? Toh Khadija wallahih inajin kunya a matsayina na mijinta na kasa biya Mata kudin operation don samun lfyr ta, Habba Yaya karfa ka manta Allah yaga zuciyar ka baka dashine Kuma ba abin kunya bane tunda itama tasan baka dashi, Suna cikin Hira na farka a gigice Jin wani irin mahaukacin ciwon ciki ya tasarmin " Innalilahih wainnailaihir rajuun wayyo Allah na cikina" Subhanallah Sumayya cikin ne Al'ameen Daya Mike cikin tsananin tashin hankali yake lalubarta , Khadija ma da saurin ta ta iso ni,sannu Aunty take fada idon ta ya jika da hawaye *****Nikam.na kasa Bata amsa kuka kawai nake hankali tashe Khadija tashi kije ki Kira doctor eiiii sauri Toh yaya tace tana mikewa da saurin ta Al'ameen Kam hannun Sumayya ya Kama sai sannu yake Mata a hakan likita yazo ya sameta a halinnan Da sauri shida nurse suka rufu a kanta tare da K'ura Khadija da Al'ameen waje,allurai sukai Mata harda na bacci lokaci daya bacci ya dauke ta, Khadija da Al'ameen na tsaye a bakin kofa likita ya fitoh ya kira su zuwa office, Malam Al'ameen majinyaciyar ka tana cikin condition Mai muni ya kamata ka samo kudin aiki nan da awa uku ba wallahih kome zai iyya faruwa, Innalilahih wainnailaihir rajuun kawai suke fada, Suka mike zuka fita a office in Khadija Kam kuka ta fara abin Yama Al'ameen yawa ta Ina zai fara anya zai yafewa kansa kuwa in yar mutane ta mutu ata dalilin rashin kudin aikin da Bai samo ba, Yaya ya kamata Aunty tasan abinda ke faruwa muje ka fada mata ta Kama hannunsa sukayi dakin Suna shiga suka samu Sumayya na bacci .......... Yaya Ammar innan yazo baka nan ya bawa Aunty kudi Amma Taki karba tace na baka Allah sarki Ammar yazo ne? Eh yaya kana fita Yana shiga, yace ma Wai Daman Yaso kuyi sallama tafiya ne ya kamasa, na gaggawa, Allah sarki, Allah ya saka Masa da alkhari Yan kiyaye sa aduk inda yake, Ameen yaya Khadija Miko min kudin na hada da dari biyar in hannu na naje na Basu Koh zasu mata daidai a Nemo sauran su bimu bashi, Uhmm lallai yaya kadai San asibiti bata ma matum aiki ba tare da kudi bak'oh? Khadija bara dai naje na gwada Koh Allah zaisa a dace tunda kinga hour uku aka bamu kuma yanzun bacci take, bara naje na dawo ya fada Yana karban kudin da khadijar ke mika Masa, Yana fita yaje wajen biyan kudi, don Allah Dan uwa kayi hakuri ga dubu goma da dari bayar a fara mata aikin in yaso za'a cikita muku daga baya Dan Allah ku taimaka min matatace ba lfy kuma hour 3 aka bani ake son mata operation? Amma Kai *makahon* nan Ina ga baka zuwa asibiti ne taima? Ina zuwa ranka shi Dade sai dai ban taba kawo majinyaci irin wannan ba Toh gaskiya ka gannin nan Koh biyar naci a cikin kudin da nake karba wallahih Sai an daure ni Kuma anan in baka biya kudiba wallahih baza'a Mata aiki ba Koh mutuwa zatayi gwara kaje ka Nemo duk in da kudi ya shiga ya fita shawara nake baka,Amma zance a taimaka maka toh hadai asibiti