← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 104

Sashe 85

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da lokacin su, wuce falon sukayi suka nufi wani kofa daban, nan ma falone Amma baikai wanda suka wuce girma ba Da kayatuwa, kara nausawa sukayi cikin wani kofar, saigasu a wajen shakatawa mai d'auke da shuke shuke na flowers mai ban sha'awa da kamshi, jefa kafa kawai muhammad yake don yayi matukar gajiya da tafiyar nan, da yake daman bai gama sauke gudun hijiran da sukayi ba, ga matsanan cin bugun zuciyrsa kiyi da karfi, lokacin da idanunsa suka sauka akan mutanen dake zaune su biyu cikin shiga na Alfarma wanda koh ba'a fad'a ba kasan sarkine tare da matarsa dake sanye da Alkimba mai masifar kyau da d'aukar ido, farace tas kyakkyawa da ita, yayinda sarkin ke sanye da rawanin buzaye a kansa ya rufe fuskar sa luf banda idanunsa babu abinda mutun zai hanga don koh kafar sa da hannunsa boye yake a cikin suturansa, shuru sarauniyar tayi ganin su Al'ameen da Alamu dai magana take da mijinta Da sallama a bakin su Al'ameen suka karaso inda suke, da sauri sarkin ya dafe daidai saitin zuciyarsa yana Ambatun sunan Allah a zuciyar sa, yayin da muhamamd suka tsunguna a kan gwuwuwinsu A hankali ya d'aura tiren akan table inda ke gabansu, hannunsa sai rawa yake wanda baisan dalilin hakan ba, tsiyaye shayin ya fara a kofi yana had'awa da zuma. Sarauniya ita ta kula da halin da mijin ta ke ciki da sauri ta matso garesa Ranka ya dade lafiya meke faruwa zuciyar ce? Shuru ya mata, itama bata damu ba don tasan halin mijin ta zata masa magana sau dubu ba Samun Amsa zatayi ba, yasha yarfata a gaban bayinta Amma tun yana damunta yanzun koh a jikinta, kara tambayar sa tayi zuciyar sa na ciwo ne? Girgiza mata kai kawai yayi baiyi magana ba, jingina yayi da jikin kujeran da yake zaune akai ya lumshe ido yana maimaita innalilahi..... Al'ameen na gama had'a shayin ya mike abinsa ya fita a lambun, sai a lokacin sarkin ya zare hannunsa daga kan kirjinsa yayinda idanunsa sunyi matukar kaduwa zuwa ja, sosai jikinsa ke rawa, ganin hakan yasa sarauniya mikewa da sauri ta fita a lambun ba'a jima ba saiga ta, ta dawo da wata tsohowar mata cikin shiga ta Alfarma kyakkyawa da ita fara, ta karaso garesa hannunta d'auke da magani, da saurin ta balla hade da karban kofin ruwan dake hannun sarauniya ta kafa masa a baki, ba musu ya karba yasha maganin, ka tashi ka koma ciki kaji?tsohowar tace Girgiza mata kai kawai yayi vaiyi magana ba, Alamu dai yafison zaman nan in, ba musu daga matar tasa, har tsohowar suka basa waje don haka yake indai ta shine yafi kaunar a basa waje ya zauna shi kad'ai sau dubu akan ya zauna da mutane. Al'ameen kam yana komawa kitchen in abinci aka kawo musu na rana, mai rai da lafiya harda kaji sukaci, zama sukayi a falon da kitchen in ke cikinsa suka kwanta a kan kujerun dake wajen alamu dai daman falon donsu akama,(ma'aikatan shayi) sai la'asar suka sake dafa sabon shaye wannan karon Al'ameen ne ya d'auka shi kad'an sa, ba tare da rakiyar jakadiya ba ya shigo falon, yarane zaune a tsakar falo su uku, biyu suna zaune a kasan cafet dake shimfid'e a tsakiyar falon, suna rubutu a takarda dukansu mata ne d'ayan zata kai shekara goma sha biyar, d'ayan kuma zata kai shekara Goma, Lokacin da yaran suka d'ago suka kallesa baisan lokacin da tiren shayin dake hannun sa ya tsubuce a hannunsa ba, a take kome ya tarwatse a wajen, suma yaran zare ido sukayi ganin barnan da muhammad ya musu a falo, d'aya yarinya ta ukun dake zaune akan kujera tana danna waya bazata wuce shekara 20 ba, ta mike cikin masifa da izza, kai wani irin wawane koh ince dolo kana da hankali kuwa zaka shigo mana falo kazo ka zubar da abu, sannan ka tsaya kana kallon mu, jira kake mu kwashe maka koh me? Habba Nabila baikamata kima mutum babba kamar wannan irin zagin nan va, baikama taba gaskiya ki gyara halinki, d'aya daga cikin yaran da ke zaune a kasan cafet in tace ma nabilar. Kinga muhibbat babu ruwan ki dani ki daina mini irin wannan abin da kike mini, niba sa'arki bace Amma na fahimci kina mini shishigi a lamurana be careful, takarasa maganar da barin falon tana hararan sa. Muhibbat ce ta kallesa kaga malam tattara abinda ka fasan nan ka tafi store a baka wasu kayi sauri ka kawowa Abba shayi?duk da Turanci suke magana. Muhammad kam mutuwar tsaye yayi yana kallon yarinyar, koh dai mafarki yake ne yarinyar kamar khadijar sa haka yake jin muryar ta, yanda khadija ke magana ba R haka ita ke magana, kaman ninta kome nata yana masa irin na yar uwarsa,duk da khadija na yarinya ya makance amma hakan bazai hanasa gane taba, a gaskiya abinnan ya basa mamaki matuka da kuma tsoro gasu su biyu masu tsananin kama da juna, koh yace masu kama dasu, jin ta sake masa magana cikin yanayin mamaki ya tsunguna ya kwashe fashashun kofunan ya fita a falon da sauri. ***************** Sumayya fa yanzun ci yafi nada ga bacci babu aikin da take yanzun kome khadija kiyi in taga aikin yama khadija yawa saita, sata ta musu take Away kawai, don khadija na kokari ga zuwa school har yamma take dawowa ga aikin gida ga masu kitso, amma Alhmdulilah baza'ace aikin mai yawa ba tunda sharane kawai sai girkin abinda zasuci don yanzun cin sumayya yafi nada gashi cikin yayi girma sosai ya kara hurata, jiki tayi bana wasa ba kafafunta haka suka cika tim,An hanata cin gishiri ma A hospital yanzun ganin irin huruwar da tayi. Yau weekend babu school khadija ce zaune a baranda tana ma mutane kitso, yayinda wasu ke zazzaune suna jiran layi yazo kansu, sumayya ce ta fito cikin shiga ta Alfarma zanine less da hijab nata mai hannu medium size, sai jakan sakalawa a kafad'a da waya a hannunta sosai tayi kyau, hannu tasa ta maida kofar falon ta rufe, "khadija lailar ta fitoh ne"? Ah ah Aunty bata fitoh ba koh na dubo miki itane? "Ah ah khadija ki bari kawai bara naje flat natan sai mu wuce" Toh Aunty saikun dawo Tana sauka a kan barandan tace"Yauwa khadija" au na manta me zan dafa ne na rana? "Kibari kawai khadija naga yau akwai layin kitso sosai in muka shiga kasuwa zanbi restaurant nai mana take Away" Ok toh Aunty adawo lafiya "Allah yasa khadija"wucewa compound in gidan tayi ta nufi sashen laila, harta haura dakalin d'akin ta saigata ta fitoh cikin shirin fita, ah ah sumayya harkin shiryane? "Bazan shirya ba laila so fa nake mu dawo kafun Azahar don wannan zafin ranan ba lafiya bane" Gaskiya kam bare ku masu ciki. "Kinga laila don Allah ki shige muje bana son yawan tsayuwar nan habba" Yi hakuri hajiya muje, kawai laila tace suka kama hanya da sumayya. Kasuwa laila da sumayya sukaje da taimakon laila sukayi sayayyan kayan baby, dana haihuwa kama daga baf gadon yara kayan sawa feda kome daya dangance baby da sumayya wanda zatayi Amfani dashi lokacin haihuwa da bayan haihuwa ita da babyn ta duk sumayya ta saya, kaya niki niki haka suka zuba a Texi, har sun shiga mota sumayya ta hangi mai mangoro, take tunanin mijin ta daya zamo mata jiki ya fado mata, sai kuma taji tanason sha, hakuri ta baiwa mai motar ta sauka, da sauri ta nufi wajen mai mongoron bata saurare maganar da laila kece mata ba,tana kokarin bude jakar hannunta, gabaki d'aya hankalin ta na kan jakan, bata koh ganin gabanta. Ji kawai tayi an bangajeta da karfi tayi baya tagal tagal zata fadi............ Ruqeenjalal *MATAR MAKAHO*
Chapter 85 · 0% Book details