← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 104

Sashe 96

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~ Na ~ *Rukayya* *Ibrahim* Page9 Bayan ta ya rike sosai ga wani irin ciwo da taji a maranta lokaci d'aya ta gigice tana salata tunda take bata taba jin ciwo irin na yau ba, Ambaton Allah kawai take a ranta gabaki d'aya ta had'a gumi, jin wani abu na zuba babu control ya sata tsorata ruwa ne yake dundula, salati ta sake hade da kwalawa khadija kira. Khadija dake bacci kamar a mafarki taji muryar sumayya mikewa tayi ta nufi ban d'akin da sauri ta bude wazata gani? sumayya ce duke jikinta sai rawa yake gabaki d'aya ta had'a gumi a tsorace take tambayar ta haihuwa ne? sumayya bata samu Amsan bata ba, nuni kawai ta mata ta kira mata mota su tafi asibiti, ba musu khadija tad'au hijab tasa akan kayan baccin jikinta, ta ruga da gudu ta fita a falon, sakatan get in ta zare ta fita bakin kwalta, abinka da dare koh tsuntsu bata samu ba koh ina shuru, kuka ta sa da gudu ta dawo cikin gidan, kofar d'aya makwanciyar su ta wuce tana buga wa, amma basu bude ba gashi kaf gidan babu mai mota koh mijin laila ma ba motar bane dashi. Haka da dawo sashen su, tana shiga zuwa lokacin jikin sumayya ya kara tsanani sosai koh zama ta kasa har lokacin tana tsungune. Da sauri ta d'auki wayar ta layin kalamu ta kira, sai da ta masa kusan 4 miss call kafun ya d'aga cikin muryar bacci yake tambayar ta lafiya? Ai tana sanar dashi da sauri ya mike ya zura jallabiyar sa ya fitoh a d'akin sa, harya tura kofar falon su zai fita saiga nannen sa ta fitoh daga dakin ta, tambayar sa tayi ina zaije a daren nan? Sanar da ita yayi Auntin khadija ba lafiya tana labour, tambayar sa tayi mijin tafa,Amsa ya bata shidai bai taba ganin mijinta ba, yama ga alamu bata da miji, jin haka yasa nanne d'aukar hijab nata ta sanar da mijinta zasukai sumayya asibiti, suka fitoh tare dashi mota kalamu ya fitar suka shiga sai get insu sumayya, fita nanne dashi sukayi zuwa ciki. Zuwa lokacin sumayya tayi laushi sosai koh gane wake kanta bazata iyya ba, dayake dare ne nanne da khadija ne suka ririketa yayinda kalamu ya diauki akwatin ta, data jima da shiryashi a zaune, rufe musu kofar yayi suka tafi asibitin da sumayya ke awo. Suna zuwa aka karbesu nanne na zaune a waje ita da khadija, kalamu keta hidima na sayyan abubuwan da aka bukata koh zama bai samu, har 4 na asuba sumayya haihuwa ya gagara, gabaki d'aya karfin ta ya gama karewa sai da aka kira Assalatu kafun haihuwa yazo gadan gadan, cikin hukunci Allah sumayya ta haifi yaran ta guda biyu wanda koh sanin wani iri ta haifa bata sani ba, tsabar wahalar da tasha, tadai san ta haihu sau biyu, Alluran hutu aka mata bayan an kimtsata a take bacci ya d'auke ta. ****************** Bugu d'aya Al'ameen ya d'auka a take Ammar ke sanar dashi anga wajen da khadija take, suna Abuja. Ai muhammad baisan lokacin da ya wantsalo daga kan kujeran falo, a take yayi sujjada akan tiles yana wa Allah kirari, goggo da mahmah dake zaune a kasan falo suna cin abinci da sauri suka mike suna tambayar sa lafiya?ai da sauri ya mike ya rungumi mahmah cikin farin ciki yake sanar da ita anga sumayya anga sumayya tana Abuja. Ai sosai suka nuna farin cikin su goggo harda kuka, a take Muhammad ya fitar da waya ya kira abie ya sanar dashi akan yanzun nan zai tafi gidan su Ammar zasu wuce abuja. Hanasa Abie yayi yace ya bari sai da safe sai subi fly zai sa a nema musu ticket sai su tafi tare da abie, ai a take goggo ma tace zata mahmah ma tace ita ma, dada dake kusa da abie tace itama baza'ayi ba ita ba, duk yanda abie da muhammad sukayi da tsofinnan su zauna a Taraba, su zasuje su dawo da sumayya amma kememen sukace kafar su kafar su abie, haka ba yanda abie ya iyya duka aka musu booking in fly tare da kiraye kirayen waya har nijar aka sanar dasu an samu wajen da suke, suma sun sanar dasu a cikin satin nan suna zuwa gabaki d'ayan su. Washe gari tun sassafe suka bar Taraba muhammad koh bacci jiya kasawa yayi, dada ma haka ta watsar da safina tace sai taje taga jikallen ta, Ammar ma tasa Abdul yayi a gaba tare zasu ya nuna musu gidan su kalamu. Karfe 9 su muhammad suka dira a Abuja, dayake yana da aboki, tun a taraba ya kirasa akan suna zuwa, tarba suka samu daga wajen abokin abie shiyazo ya d'aukesu a Airport, direct gidan su kalamu suka wuce, Amma abin haushi basu sami kowa ba wai Suna asibiti, haka mai ganin ya sanar dasu Alfarman ganin baban kalamu abie ya nema ba musu, mai gadi ya shiga ga sanar dashi, aiko sai gasa bayan sun gaisa ne sukace masa suna son sanin asibitin da kalamu sukaje in ba damuwa. Ganin girman su da kudin su, gashi kamar ba lafiya ba, hakan yasa baban kalamu yace musu bara ya bisu asibitin, shiga mototi sukayi ya kira nanne ya tambaye ta asibitin da number room nasu, da mamaki yake tambayar ta koh lafiya jin muryar ta ya dishe-dishe alamu dai ba lafiya ba, koh tayi kuka, ya tambaye ta lafiya tace masa ba kome, kashe wayar yayi ya sanar dasu abie ga asibitin da suke. Suna isa asibitin muhammad da gudu ya ruga bayan sanar dashi block inda suke koh kunyan su abie baiji ba da gudu yayi block in mutane sai kallonsa suke, da sauri sauri ya shiga d'akunan one by one yana dubasu, ana ukun ne ya shiga koh sallama babu ganin mace kwance akan gado ga yara sa'o'in juna zaune rike da jinjiraye a hannayen su, da sauri suma suka juyo jin mutun a d'akin babu sallama. Ai da sauri khadija ta mike ta kwala ihu yaya!!!!!!!! Da sauri kalamu dake kusa da ita rike da d'ayar babyn da sauri ya cafke wance ke hannun khadija, don saura kad'an ta buga jinjira, da gudu khadija tayi wajen muhammad batayi wata wata ba ta rungumi d'an uwanta tana fashewa da kuka yaya, kaine koh mafarki nake? Khadija nine nine khadija ina Aunty ki? Allahu akbar yaya kalli nan tace tana nuna masa kan gadon da sumayya ke kwance har yanzun tana bacci. Da sauri ya ware idanun sa yana kallon sumayya sai kuma ya juya ya kalli kalamu, ya sake kallon khadija? Gyada masa kai tayi tana murmushi, shima murmushin yayi sai kuma ga hawaye, tare da matsawa kusa da gadon da sumayya take kwance, dukawa yayi akan gwuwar sa hannu yasa a hankali yana shafa fuskar sumayya, dake kwance sanye da kayan asibiti, tayi kyau tayi fresh irin na masujego, wannan ce sumayyar tawa ashe haka take da kyau masha Allah? Itace yaya kaga wa'innan jarirai nakane. Da sauri ya juya yana kallon kalamu da sauri ya mike tsaye hannu yasa ya Amshi babies in yana kallon su, yarane mata masu tsananin kama da junan su tamkar An raba kunu a kofi, gasu masu tsananin kama dashi kome nashine a fuskar yaran, gasu farare tass, rungumarsu yayi ya fashe da kuka. Toh ragon maza baka da aiki sai kuka, mahmah da suka shigo cikin d'akin tun d'azun, amma basu ma san da su ba. Da sauri ya nufi mahmah yana ce mata, mahmah kalli yaran nan, wai yarana ne kallesu fa ga sumayya mahmah kyakkyawa fa sosai? Sunkuyar da kai abie yayi yana mamakin surkin nan nasa yau koh dai ya mantasa a wajen ne, shima da sauri ya nufi wajen da yarsa ke kwance, zama yayi a bakin gadon yana shafa gashin kanta daya hargitse koh ribon babu. Mahmah ce ta karbi baby d'aya dada ma ta karbi d'aya goggo kam baki kawai ta sake tana bin kowa da ido, kalamu kallon babansa yayi dake gefe, ya gaidashi, amsawa yayi yana tambayar sa mai jiki. Matsawa kusa da abie muhammad yayi ganin sumayya ta fara motse, a hankali ta bude idanunta dalilin kukan da yaranta suka sake dukan su biyu. Tana bude idanunta bata sauke sa akan kowa ba sai muhamamd dake kanta a tsaye, kamar a mafarki haka ta kalli abin da sauri ta mike zaune har tana kokarin zamowa kasa, da sauri ya tarota, bi a hankali sumayya jikin ki ba kirfi. Ai jin abinda yace da sauri ta riko hannunsa gam tana kwalama khadija kira, Amsawa khadija tayi da sauri ta karaso wajen"khadija yayanki ke mini gizau na kamasa " Aunty ba gizau bane yayane "Yaya kuma khadija mijina fa baya gani yau kuma naga wannan na gani"? Aunty ya warke ne. Ai sumayya najin haka ta sake dariya cikin farin ciki koh damuwa da jikinta batayi ba ta rungume mijinta, don ita sam hankalin ta vaikai wajen mutanen d'akin ba. Mikewa abie yayi dasu mahmah zasu fita a dakin su basu waje don sukam kunya ne zai kashe su. Nanne dake toilet tana wanke kayayyakin sumayya daya baci, tun d'azun take jin surutai a d'akin mikewa tayi tsaye da boket na kaya a hannunta ta bude kofar toilet ta fitoh, Wai khadija da kalamu anya kuna da hankali kuwa mara lafiya na bacci kuke surutai da wa......bata karasa ba tayi turus ganin jama'ar dake shirin fita a d'akin dasuka juyo suna kallonta. Dada ce ta kama salati tana tafa hanneye, wanake ganin nan? Abie ma da sauri yace Hafsa?? Nanne kam bata wani nuna reaction ba, dayake tun daren jiya data gane sumayya tasan tabbas zata ga su abie, duk da saurin da take tabar asibitin kafun suzo don ita batasan sumayya gudu tayi ba, haka ma batasan itace Aunty khadija ba sai daren jiya. Nanne bata wani Amsa ba bare ma ta nuna tasan abie, sai tsayuwar da tayi tana kallon sumayya data sake muhamamd tana kallonta sosai irin kallon nan na kewa da soyayya, cikin kuka tace" ummi"? Sai a wannan karo nanne tayi magana, Na'am momcy? Da sauri sumayya ta sauka akan gadon tana takawa a hankali cikin dauriya tayi wajen mahaifiyarta fad'awa
Chapter 96 · 0% Book details