← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 104

Sashe 32

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

zai Bata itama d'ayar hannun nasa yasa ya lalubo fuskarta,Jin fuskar Tata yasa ya fara lalubar bakinta da hannunsa "Kasan Allah Inka samin hannun hagunka a bakina ba"tace ganin Yana ta tattaba Mata baki da hannun nasa Kayya abinci Zan baki,yafada Yana Mika Mata gutsuren bread inda ke hannun damansa a baki, Rufe bakin tayi Taki budewa. Shikam sai goga Mata bread in yake a lebe gashi duk butter ya Bata Mata fuska "Kanata Bata mini fuska da butter"tace bayan ta rike hannunsa Toh ba kinki bude bakin ba sai kokari nake, Kaga kaci abincin kan, ka barni naci nawa,tace Masa tana goge fuskar ta Toh ki bare na baki wanann kawai kinji Ganin yanda ya nace Mata yasa ta bude bakin Yana saka Mata bread in da sauri ta datse hakorin ta,Wai don ta cije yatsarsa shima abin mamaki da sauri taga ya cire hannunsa kafun ma hakorinta ya Sauka akan yatsar,Yana dariya Ai Daman nasan saikince Zaki Rama shiyasa Nima nayi taka tsamtsam da yatsana. Shuru ta Masa Bata tanka masa ba. Haushi ya shigane bakutuwa? Kara ta sake tayi kansa "nice bakutuwa" Jin ta hafto, yasashi Kare kansa, hannu yasa ya tare fuskarsa. Ganin haka sai abin yayi mugun Bata dariya waishi harga Allah tunani yake wani abin zata Masa haryana tare fuska. Jin shuru baiji tayi Masa kome ba yasashi fara laluben ta Aiko ya jita a kusa dashi,da sauri ya rikota, sorry kinji "Ni......shuru tayi Bata karasa ba Jin sallama a kofarsu amsawa tayi ta mike kaci abincin kafun na dawo" Toh yace Yana saka hannunsa ya d'auki cup inda ta aje masa... Sumayya tana fita taga wata budurwa irin classic innan zata Kai kusan sa'ar ta kyakkyawace Amma baka Tasha kwalliya tana rataye da school back "sannuki da zuwa"tace Mata tana shimfid'a musu darduma"Bismillah ki zauna" Yauwa Ina kwana?bakuwar tace tana zama akan sallayar "Lafiya ykk ya gida"? Lafiya Alhamdulillah,ya aiki? Lafiya klau,Ina zuwa Sumayya tace tana mikewa d'akin ta shiga ta hada cornflakes da ruwa Daya a fijrij ta hada a tire ta kawowa bakuwarBismillalahih ka abin Kari ba nauye Kam"tace tana ajemata a gaba La d'awainiyane haka Allah dakin barsa yanzun na fitoh gida zanje school ne ma nace bara na biyu dai ta gidanki "Allah sarki Amma dai ki saka Koh albarkane yafi dai kikici bazanji Dadi ba" Shikenan bara dai NASA albarkan tunda kin Masa tace tana iban cornflakes in da shukali uku tayi tace Alhamdulillah "Badai harkin koshi ba"? Alhamdulillah wallahih ya isheni,suna na kamila Ina zaune a unguwan gadi,Daman nazone wajen ki in Babu damuwa inason zan fara Training in make-up,Naga wanda kika ma kanwata a auren Asma'u shine nace tamin kwatancen gidanki inyaso sai nazo inji. "Toh gaskiya ni bana koyarda make-up saboda bani da shago sai gidana Kinga Kuma Ina da ayyuka yau da gobe"tace Mata tana tunanin ta yarda ne Koh karna yarda Ba damuwa sister Nima Ina zuwa school Kinga saiki bani time inda zanna zuwa Koh ki ban number ki duk lokacin da kike free sai ki kirani Koh Kika samu Yan make-up. "Shikenan yanzun dai ki bare Inna ma mijina magaa in ya Amince xakiji daga gareni" Ok ba damuwa saiki bani contact naki Koh in ba damuwa sannan nawane kudin da Zan biyaki Kinga Inna koma Koh yaushe Kika kirani saina tawo dasu Toh, make-up dai kashi kashine sanann yanayin kwakwalwar mutum wata a wata D'aya zata koye make-up wata biyu wata fiye da uku ma Bata iyya ba so ni bansan ya yanayin d'aukar kwalliyarki ba Amma dai inso samune wata uku kina koya" Ok yanzun wata ukun nawa ne kudina "50k Koh wani wata kudinki na wata uku 150k kenan" Wai habba sister kudin nan yayi yawa Mana dubu dari da hamsin, Gaskiya kenan Kinga a cikin kudin Zan Saya make-up kit sabo duka,saboda bazaiyu Ina baki na aikina kina koya dashi ba, sanan infa kika iyya a kwana uku Zaki iyya samun sama da kudinda Kika biya na koyo" Hakane Kam Amma dai ki duba ki rage mini kinsan baban mu yace in zaiyu nida kanwata zai biyawa. "Shikenan Zan rage dubu goma" ok shikenan an gode saina jiki Shikenan bara na baki number,daidai lokacin Al'ameen ya fito d'akin hannunsa rike da cup inda yasha shaye What?? wa nake ganin nan Kamar Muhammad Al'ameen Yusuf bakuwar tace tana zare ido A matukar razane har bakin sa na rawa yace kamilaaaaa........... *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara* *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* *Na tsunguno(habil)* *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* ) *Turaren turara jiki after birth* , *Na d'aki(halud Al'oud)* *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* Contact them vie 08028827241 or 09033791049 IG @umsadincenseIG @umsadincense *IG *MATAR MAKAHO*
Chapter 32 · 0% Book details