← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 104

Sashe 24

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

~ Na ~
*Rukayya* *Ibrahim*
Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa
free book
Page 2
Ba karamin Dadi naji ba,da saurina Amsa musu sallamar muryata na rawa"waalaikumu salam"nace Ina kallonsa ganin baiyi niyar sakeni ba,"toh ka tashi Mana naje naji suwa ke sallama"
Wayace kiyi magana?
"Au amsa sallaman ne,laifi"
Toh ai badon Allah kika.amsa ba ya fada Yana sauka a hankali ya kwanta a Gefen ta
Jin ya sauka akaina ai da sauri na mike zanina da ya yasar a kasa na tsunguna na d'auka,fita nayi a d'akin duk jikina sai rawa yake, na barsa a kwance akan
Gadon.
Yan matane zasu Kai su biyar gabaki D'aya bazasu wuce sa'o'in Khadija ba,"sunnunku da zuwa"
Sukam mamakine ya cikasu,wannan ne MATAR MAKAHO Mata Kamar balarabiya Aiko Mai kudi lafiyayye ba kowa bani yake sa'ar samun mace Mai kyaun Sumayya, yauwa,Ina wuni Aunty sumy? Suna had'a baki
"Lafiya Alhamdulillah bara na d'auko muku abin zama"
La ki barshi kawai Aunty,sauri muke ma dare yayi.
"Gaskiya Kam Kuna Mata yanzun ana neman 10 na dare fa,kuna waje"
Eh wallahih Aunty nasan bazaki ganemu ba,Daman mu kawayen Khadija ne,wata acikinsu tace
"Kawayen Khadija Kuma aini Khadija batace mini tanada kawaye ba bayan Asma'u"nace musu haka don na gane kawayen Amaryar ne,ganinsu da Anko
Eh Aunty dukan mu kawayen Khadijan ne harda Asma'u,
"Toh Allah dai yasa lfy ba wani abin bane ya faru"nace Ina zullumi kar wani abinne ya samu khadija
Eh Aunty yanzun ma gidan su khadija Muka fitoh akan ta rakamu wajen ki,shine tace Wai yayanta ya hanata fitan dare
"Gaskiya ne Bata fita bayan mangariba, Allah dai yasa lfy kuke son ganina"?
Eh lfy Daman mun tambaye tane akan inda tayi lalle da make-up jiya,
Shine tace Mana Wai agun matar yayanta,.
Shine mukazo mu tambaya Koh zamu samu lalle gobe,da kwalliya in Allah ya kaimu?
"Bazaku samuba" nace Ina zuyawa na shiga d'aki Koh bin ta kansu banyi ba, saboda sanin da na musu sune suka ma khadija rashin mutunci jiya agun Fulani Dance.
Ina shiga d'aki akan kujira na zauna, gaskiya Ina son yin lalle Koh don na samu na biyan bukata Amma bazan ma Yan iskan nan ba.
Sumayya meyasa bazaki musu lallen ba? Al'ameen ya tambaye ta
"Ina ruwanka watoh ka fara sa ido Koh"
Ina Naga idon bare na saka ni duhu nake gani,ya Bata Amsa
"Watoh kaima ka iyya bakar magana Koh"
Ai agunki na koya
"Badai aguna ba malam ehen"
Amma Sumayya dakin musu lallen ai.
"Bafa Zan musu ba Yan iskan yara bakasan me suka mini bane,"
Yaushe sukazo gidan nan har suka Miki Abu?
"Kai jama'a yaushe ka koma D'an jaridane ban sani ba"
Baimin magana ba mikewa Naga yayi Yana kokarin sauka a gadon ai ihu na saka na mike zanyi waje.
Wallahih Kika fita a d'akin nan saina Miki abinda bakiso
"Me kenan"?
Kin fini sani,yace Yana nufar kofa, waje ya fita yaje ya rufe shashen mu ya dawo ya rufe kofan d'aki
Ina dai zaune sai raba ido nake,ganin ya nufu kujiran,da nake yasa na mike a hankali na lallaba na chanja waje, zuwa gaban mirror na tsaya,
Jin motsen takunta yasa ya gane lallai tabar Kan kujiran..
Fara lalube yayi nidai sai chanja waje nake in ya nufi inda nake saina chanja waje,duk magiyar da yake min, kin tsayawa nayi.
Muna cikin zagaya d'akin kawai aka d'auke NEPA gashe ban San takamemmen inda na aje wayata ba.
Jin tsayawar fanka,yasa ya gane an d'auke NEPA ne, shiyasa ya fara tafiya a hankali Yana laluben ta sanin da yayi yanzun itama ba ganinsa zatanayi ba.
Raraba ido nake ta faman Yi banajin motsensa Sam sannan Banga wayata ba.matsawa nayi sosai jikin kujira na sunguna Zan duba wayata,ji kawai nayi ya rungumeni ta baya
"Wayyo Allah nikam ka sakeni wallahih banaso"
yanzun dai kema baki ganin kome kamarni.
"Allah ba kamar Kai bakam"
Koma yayane dai baki gani
"Nikam sakeni hai"
Naki yace Yana dagata
"Wayyo nashiga uku,ka saukeni"nace Ina ta faman mutsu mutsu
Kiye shuru Mana mu k'wanta
"Niki shurun nikam ka sakeni"
Kin saketa yayi duk yanda tayi ya saketa ki yayi
Ina ji Ina gani ya kwanta akan kujira d'aurani yayi akansa,tun Ina masifa harnayi shuru Jin ana iska da yayafi ,sanan aka kece da ruwan sama,
Baccine ya d'auke mu dukan mu biyu akan kujiran muka kwana
Da safe,shayi mukasha da bread,wanke wanke na fitar Ina wanke wa
Sanin da yayi Koh ya fita ba lallai bane yayi ciniki sai wani ikon Allah da safen nan, gashe mangoron duk sunyi labo labo.
Kayansa ya fitar Wanda Bai wuce kala hudu ba a igiyar bayan gida inda take Tara kayansa masu datti,d'aukar basket in kayan Sumayya yayi ya fitar dashe waje ya zuye a dakali,ibo ruwa yayi ya fara wanke musu kayan.
Ina wanke wanke,Yana wanki,dukan mu shuru Babu Mai magana
Assalamu alaikum, khadija ce tayi sallama hannunta d'auke da laida
"Waalaikumu salam khadija"
Ina kwana Yaya?
Lafiya khadin Goggo
Ina kwana Aunty,tace tana murmushi
"Lafiya khadija ya Goggo"
Tana gaisheki,tace tana zama a Gefen yayanta dake zaune abakin dakali da boket in ruwan kumfa
"Aiko Ina amsa wa"
Aunty kinsan me? Kai jiya Naga abin mamaki,tace d'auraye kayanda yayanta ke wankewa
"Me Kika gani haka"? Na tambaye ta
Aunty kinsan Allah Ina fita a gidan nan,na wuce gidansu Asma'u duk inda na wuce sai ayita kallona ,
Ina Isa na samu an kawo mototi sunkai ashirin,kinsan Aunty mijin Asma'u shima Mai kudine?
"Ina Zan sani khadija ai sai kin fad'amin"?
Ina isowa wajen mototi sun cika har ana kokarin tafiya,kawai saina nemi gefe na tsaya, kawai wani abokin Ango yazo kusa Dani,Wai hajiya baki samu mota bane?
Nace eh ban samu ba ku tafi kawai Zan hau machine,
Wai harda cewa Wai babban Dani ba girma na bane Hawa machine bara a sama mini wajen zama,
Kawai yaje ya fidda kawar amarya ya sani a motar
"Hhhhhh Kai habba dai khadija"nace Ina dariya
Yanzun abin dariyane agunki Sumayya an fidda wani Ansa wata,Koh ke zakiji d'adi a Miki haka, Al'ameen ya fada Yana Bata Rai
Khadija Kam tsoro ne ya kamata Sam ta manta da yayanta agun ta sake baki tana zuba
"Kasan me suka matane"?
Koma me suka Mata hakan Bai kamata ba cin fuska ne,
Fad'a Masa kome nayi akan abinda suka ma khadija
Koma me suka Mata banji Dadi ba
"Khadija tashi mu shiga ciki muye sirri"nace Mata Ina Kama hannunta Muka shiga d'aki
"Khadija karasa mini sai akayi yaya"na tambaye ta
Ai Aunty in gaya Miki kawai na Shiga abina kawayen fa Basu gagane niba sai da Muka Isa Taraba motel in da Muka fifita a motar,duk Saida suka Raina wankan su Aunty kaf insu harda Amarya Babu Wanda kwalliyar ta yayi kyau irin nawa,
Sai da nama Amarya magana kafun suka gane nice, wallahih Aunty baki ga yanda aka maida ni abin kallo ba masu vedion aure sai d'aukana suke harda hotuna,Kinga agun kawaye uku nayi yaran masu kudi,samari Kuma sai turawa suke Wai suna son magana Dani a waje.
Kin zuwa nayi kawayen ma naki kulasu,ai Aunty badon Allah ba kenan suke Sona, tunda Basu Soni a khadija ta ba Saida suka ga nayi kyau,ta karasa maganar tana washe baki
"Gaskiya ne khadija bare ma insha Allah karatu zakiye insha Allah"nace Ina murmushi don tabbas khadija akwai kaifin tunani
Aunty jiya fa goshin mangariba na fitoh a Hall in Zan dawo gida Kinga yanda abokan Ango ke ribibin zasu kawoni gida,.
Amma naki,
"Gwara da Kika ki khadija yanzun mutum ake kiwo. Ba dabba kad'ai ba"
Wallahih kuwa Aunty kawai da dare saiga wani yazo gidan mu bansan ma waya nuna Masa ba Wai ana sallama dani,
"Lallai kanwata tayi goshi"
Allah Aunty kin fita nayi Goggo tayita fad'a
"Don me khadija wulakanci ba kyau fa dakin fitan ai"
Gaskiya ni Aunty banason Abu da masu kudi,
don mudi yace mini da babban mota yazo,Kinga masu kudin nan in Kika aure su wallahih Kina Yar talaka,basa ganin daraja. Yan uwanki
Ah ah khadija ba duka aka zama D'aya ba indai da kyakkyawan Niya akayi aure badon kyau Koh kwad'ayi ba,insha Allah ba abinda zai faru
Hakane Kam aunty,au Ashe fa na had'a da Aunty a magana ta am sorry (don tace auren masu kudi basa ganin darajan Yan uwan matan su,in talaka wa ne)
"Uhmm khadija kenan,ai Nima na zama talaka yanzun"
Amma ai gidan ku akwai kudi?
"Gidan mijina babu"
Aunty jiya wasu sunzo wajenki karfe kusan 10?
"Eh Khadija"
Nima jiya suka zo gidan mu Wai na fad'a musu Wanda tamin lalle,da Wanda tamin make-up
"Kawayen Amarya Koh"?
Eh Aunty sune,suka mini wulakanci agun Fulani Dance
"Aiko shiyasa nayi maganin su nace bazan musu lalle ba"
Meyasa Aunty
"Saboda kee kad'ai Zan ma kwalliya har Agama programs na auren Asma'u"
Kiye hakuri ki musu Aunty Zaki samu kudi sosai fa yau HENNA DAY, Kuma da yamma za'ayi Algaita
"Gaskiya khadija bazan musu ba "
Shikinan Aunty ga kayanki nan na dawo Miki dasu
"Habba khadija ki rike na bar miki"Daman kyauta na baki ba aro ba"
Aunty' ai yayi yawa
"Ki rike duka"
Allah ya..........
Bata karasaba mukaji sallama na muryar mace babba
Al'ameen dake zaune a waje ne, ya amsa
Sannu Ina kwana hajiya,yace Yana tsame hannunsa a wankin
Lafiya Alhamdulillah don Allah nan ne kofar MATAR MAKAHO?don ita Bata zata Al'ameen baya kallo ba
Kafun Al'ameen ya Bata Amsa Muka fitoh a d'akin dagani har khadija kallon matar muke hajiyace Kuma hamshakiya daga ganinta naira ya zauna
"Hajiya lfy" nace Ina kallon ta dajin haushin sunan da ta kirani Wai MATAR MAKAHO mtwss
yauwa wajenki nazo
"Ok Bismillah khadija d'auko Mata darduma" nace saboda d'akin mu D'ayane bazan iyya saka baki a ciki ba
"Bismillah hajiya ga wajen zama"
Zama tayi Muka gaisa
Ni sunana hajiya sa'a findon Asma'u kawar Khadija kanwar mijinki nasan khadija Kam ta ganeni Koh? tace tana kallon khadija
Eh Aunty sa'a, khadija tace
Yauwa Daman nazone akan in ba damuwa,Koh Asma'u zata samu lalle inda halima harda mu,don jiya na turo kawayen ta sunce Wai bazakiyi ba shiyasa nazo da kaina,
"Gaskiya hajiya ni Ina da aure bazan iyya zuwa in ma amarya lalle ba,tunda Henna day ne yau"
Habba wallahih ba kome zamu zo har gida ki Mana itama Amaryar zatazo saiki mata,tunda ba'a d'aura aure ba kuma gida baki da hanci
"Shikinan hajiya"
Yauwa nace zata iyya zuwa yanzun don anjima akwai Algaita da yamma,saiki Mata kwalliya ma duka
"Toh hajiya gaskiya bazaku samu lalle yauba don indai lallen Amarya ne Dole za'a jima ga kwalliya duka"
Saiki Mana gobe da safe,tunda Walima ne kwalliya kawai zaki Mana da yamma saiki Mana lalle da safe,
"Ku nawa ne"?
Mu bakwai Zaki ma lalle da Amarya 8 Amma bansan kawayen ta mutun nawa ba
"Ok za'a ma Amarya lalle da kwalliya yau"In yaso ku sai amuku gobe hannu bibiyu sai kwalliyar walima,saboda time"Amma banda kawayen don bazasu samu ba
Ba damuwa Daman booking mukayi har Agama bikin zakina Mana kwalliya in ba damuwa
"Ok shikinan"
Nawane kudin ki?
"Hajiya kwalliyar Amarya kashi biyu ne ana heavy make-up a dinner, bud'an Kai, kamu sai light make-up anayi a Walima, Algaita, Arab night
Kinga kenan light make-up Zan mata yau"
"Kudin kwalliyar yau 5k ne, lalle 10k na Amarya"
"Kwalliyar ku 3k ne Koh wani mutum D'aya"
Ok na gobe fa ?
"Lallen ku na gobe hannu bibiyu ne Kuma ja da baki za'a muku a hannun dubu D'aya da d'ari biyar ne, in da lalle na Kuma 2k Koh wani mutum D'aya"
Ok tace ta hada lissafi ta bani kudin a hannun,gashe kudin kwalliyar Amarya da lallen ta nayau da kwalliyar mu sai na lallen mu na gobe,in mukazo kwalliyar walima sai muyi lissafi harda na dinner,tace tana mamakin wayewar Sumayya,
da akace mata MATAR MAKAHO ne ta d'auka Koh zatazo taga bagidajiya sai taga hatta MAKAHO ma bazaka zata baya gani ba
Ok hajiya" nace Ina karban kudin kirgawa nayi Naga ya cika,hajiya watoh harda kudin lalle Kika bayar kenan"?
Eh zuwa kawai zamuyi goben,Amma Amarya na zuwa da lallen ta,kinsan ana kawo kayan rufi da lallen Amarya ?
"Gaskiya ne shikenan saina ganku anjiman"
Allah yasa tace tana Mike wa ta tafi
Khadija Kam da Al'ameen mutuwar tsaye sukayi,Wai kwalliyar da ake gogiwa shine za'a biya dubu biyar ayi ai gwara ma lalle zaiyi sati..
Aunty yanzun duk wannan kudin na lalle ne kawai da kitso? khadija ta tambaye Sumayya
"Kai Khadija ba abin yayi bane,Kuma kayan kwalliyar ma tsadane dashi"
Ikon Allah,tace
"Kinga khadija tashi maza kije kasuwa ki mini sayayyan lalle sai ki sai Mana semolina yau tuwo zanyi na gaji da shinkafan nan na fada Ina Mika Mata 10k ki sai Mana harda kaji biyu a gyara Miki a kasuwan,ki hada mana da kayan Miya harda su vegetable"
Toh Aunty tace tana karban kudin
Al'ameen Kam baice kome ba ,Yana shanya kayanda yawanke
Khadija na fita Koh minutes uku batayi ba mukaji Karan faduwa timmm sai muryar Khadija data k'wala Kara,irin na azabar nan,dagani harshi da gudu Muka nufi kofar fita a shashen mu, ganin tsabar rudewa Bai gane hanyar kofa ba yasa na Kama Masa hannu na Masa jagora Muka fitoh,
me Zan gani khadija ce a..........
Chapter 24 · 0% Book details