← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 104

Sashe 11

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

bane tashi yayi yaje ya tattara kayansu na dakin emergency ya dawo dashi dakin da take yanzun, zama yayi a Kan kujira, Har dare yayi sosai Bata farka ba, sai karfe 2 na dare ta farka tana fizge fizge bakin ta dauke da salati tana ambatan sunan abie yayi hakuri karya gujita itama,, Abirkice ya mike Yana kakamata ganin irin girgiza da take ya tsorata da sauri ya k'wala ma nurse inda ke dakin a zazzaune Kira ganin inyace zai tashi Sumayya zata iyya raunana kanta, Da gudu suka yi kanta suka kakamata surutai tayita Yi Akan Abie da salati sai Shan anjima kadan Sumayya ta koma bacci, Likita lafiya kam meke faruwa ne da Matata?ya fada hankalin sa a mugun tashe, Ka kwantar da hankalinka ana samun haka Daman in dai mutun zai farfado sai yayi ta sambatu,.. Toh doctor yace Yana komawa Kan kujiran ya zauna hannunta ya laluba ya rike yanajin wani irin tsoro a ransa, Har asuba Yana zaune sai da yaji ana Kiran sallah kafun. Ya Mike ya fita yaje yayi ya dawo ya cigaba da zama... Khadija Taki fadawa yayanta abinda ta gani a gidansu gudun kada hankalin sa ya tashi ta Sansa da saurin birkice wa gashi Yana fama da Sumayya tazo ta Kara Masa da wani Kuma, Keke napep tahau ta wuce a kofar gidan su Goggo Amina ta sauka ta biyasa kudinsa ta shiga gida da sallama. ...... Goggo Amina ta samu zaune sai rusan kuka take Kamar wance ake yanka namar jikinta, Da sauri ta karaso gareta cikin tashin hankali tana cewa Goggo Amina lfy menene ya farune wallahih tunda na tafi hankali na yaki k'wanciya? Wallahih Khadija kedai ki bare kawai mutanen gidan mu sun dawo kashe junansu, Kamarya Goggo ban gane ba? Toh dazun bayan la'asar iro ya dawo daga aiki yazo zaici abincin ranan sa ashe suwaiba( yar baba lami) ta dauka taci shine da yazo dauka yaga babu yake tambayan inno ya abincin sa babu a kula shine fati tace masa suwaiba ne taci, Tashin sa ba wani tunani ya zaro wayan wuta ainahin na bol ya zuba mata ita kuma da taji zafi tana ihu ta zari tabarya zata muka Masa, Inno Kuma ganin za'a bugawa iron ta tabarya tazo zata k'wace kawai tabarya ya sauka a kanta,shine fa Kika ga ta mike Koh motse batayi, Ni tsorona ma yanda naga Kan Bai fitar da jini ba kinsan akwai babban hatsari ka bugu irin wannan ace jini Bai fitoh ba, Shine iro ganin inno a yashe a kasa yaje ya ibo Yan sanda akazo aka tafi da suwaiba, gabaki daya gida ya hargitse su bappa nayinku duk sun bisu station wasu suna asibiti har hanzun ba'a San takamammen halinda inno ke ciki ba mutuwa Koh rayuwa wayyo ni Aminatu, ta fada tana sake rushewa da kuka ita dai Khadija Allah ya kiyaye na gaba tace ta Mike taje ta ajiye kulan Sumayya a kitchen sai gobe zataje kofarta da safe,wanka tayi, tayi isha'i ta kwanta don batajin yunwa taci a asibiti,haka tayita juyawa Amma bacci yaki daukan ta tashi tayi ta Kama lafilfilu tana nemawa Aunty Sumayyan ta lfy da nasaran aiki sai 1 ta kwanta Bangaren Al'ameen bayan sallan asuba har lokacin yana zaune Dayake dakin da suke yanzun babban falo ne Mai dauke da majinyata masu yawa wa'inda aka ma operation shiyasa Basu kadai bane a dakin, sosai Yan dakin ke mamakin MAKAHON nan shin baida Yan uwane da zasu kula da wannan Mara lfy sai MAKAHO chap lallai Kam kowa gulma na cinsa( Niko nace gulma zai karku bazakuji kome ba) Tun asuba Khadija ta farka Bata koma. Bacci ba wanke wanken Goggo Amina ta fara ta hada harda kulan aunty ta duka ta wanke tayi shara tana Gamawa ta daura dumame ganin yau Goggo Kamar Mara lfy haka da tashi ,tana Gamawa ta dauki key sai gidan yayan ta, Yauma sai da tayi shara ta daura ruwan zafi Yana tafasa ta juye a flasks ta dafa indomie da kwai lokacin karfe 7:30 wanka tayi tasa kayan ta data dauko a gidan Goggon ta tadau abincin tayi hanyar FMC ****Da misalin karfe bakwai na safe na bude idona Wanda nakejin Kamar an zuba mini barkono a cik i a hankali na sauke k'wayan idanuna a kansa a zaune yake ya tasani a gaba Kamar wani Mai kallo yayi tagumi kallo daya zaka Masa kasan a cikin zullumi yake sosai....... *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin Koh kinsan mace sai da kamshi da* *Turaren Suna d'ayane Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin* *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da gyara* *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* *Na tsunguno (habil)* *Na jiki (kwalaccam) (khumraBlack & while*) *Turaren turara jiki after birth* *Na d'aki (halud Al'oud)* *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* *Suna bada kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* *Contact them vie* 08028827241 or 09033791049 *MATAR MAKAHO*
Chapter 11 · 0% Book details