← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 104

Sashe 8

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kasa kafa ka fice ka barmu da ita, tun dazun nemanka ake likita nason ganinka, Kiye hakuri gida naje na dauko Mata kayane Me yasa she dayan bazai je ya dauka mata ba Kai ka zauna?, Taimakona yayi Kuma ya tafi, Jeka aje kayan kazo likita nason ganinka Da toh ya amsa Mata da lalube ya Isa inda gadon ta yake har lokacin Bata farka ba, Juyawa yayi ya fita a dakin sai da ya fita kafun, ya tuna baisan office in likitan bama tambayar wata nurse yayi da taimakon nurse innan ya gane office in doctor shiga yayi da sallama doctor ya amsa masa matashine kamarasa, Kaine ka kawo Sumayya Abdulsalam shugaba? Eh nine doctor ya basa amsa ..ok Sumayya na fama da apendes ya kunbura sosai don haka dole za'a Mata tiyata ga wannan sai kaje ka biya kudin, Atake zufa ta fara karyo Masa Innalilahih wainnailaihir rajuun,likita kudin zai Kai nawa,yafada Yana tambayan sa?, Bani bane Mai karban kudi in kaje wajen biya za'a fada maka................. My WhatsApp number *MATAR MAKAHO* ~ Na ~ *Rukayya Ibrahim* Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa Free book Page Cikin tashin hankali ya mike ya fita Dayake shi mutum ne Mai saurin fahimta yasa dakansa ya wuce wajen biyan kudi, Kudin 50k yaji ance Masa, Innalilahih wainnailaihir rajuun take yaji Kamar kansa xai rabe biyu haka ya karbi takardan ya wuce zuciyansa sai rawa take, shi Ina yasan zai samu kudi gabaki daya jarinsa ma baifi dubu daya da dari biyar ba Ina zai samu dubu hamsin, Koh bashi zai karba wazai tinkara in ma an basa Ina zai samu kudin biya? Har cikin ransa baya kaunan wani abin bukata ya Tashi ta bangarin Sumayya ya kasa Mata har sai Yan gidansu sun Mata duk da baisan dalilin da yasa duk cikin Jala Arasa mijinda zasu aura Mata sai shi suka zaba Mata Wanda har yau ya kasa samun Amsa dalilinsu,, Kuma bayason Koh da Wasa ta Saida abinda tazo dashi daga gidansu,saboda gazawarsa wajen Bata kulawa Bai santa ba Bai ta ba ganinta ba Bai taba Jin lbrn taba Bai San ya take ba muryarta kawai ya sani Amma a D'an zaman da sukayi Yana jinta har cikin ransa,, Ya Allah ka bani ikon kulawa da wannan Amanar da aka bani, A hankali yake tafiya harya fita a get in hospital in da taimakon wani Almajiri ya tsallake titi 100 da ke hannunsa ya Saya Mata Ayaban 100 guda biyar aka basa ya baiwa Almajirin ayaba daya ya sake tsallakar dashi, cikin hospital in ya shiga yanabi a hankali da sardarsa harya Isa kofar dakin da aka kwantar da ita da sallama ya shiga dakin, "Waalaikumu salam" na amsa Masa cikin dishashesshen muryata dagaji kasan na Mara lfyne maijin jiki Sannu Sumayya ya jikin ??. "Da sauki Alhamdulillah" Sannu ya sake cewa **Kai kawai na iyya daga masa Lalube ya fara Yana neman wajen zama, "Kujiran na Gefen ka na dama"nace Masa Laluben damansa yayi yaji kujiran plastic na roba ya matso dashi Kusa da gadon inda yaji muryarta ya laluba ya aje kujiran kusa da gadon saitin kanta a hankali ya zauna, Sannu Sumayya ga ayaba na sai miki yafada yana bude laidan hade da fitar da Ayaban masu k'yau guda biyar zai bare mini, "Ah ah ka ajiye,so nake sai nayi sallan asuba nayi brush da wanka Koh zanji dadin jikina kafun NASA Abu a bakina" Toh bara na taimaka Miki ki shiga bandakin sai kiye wanka da brush in duk na kawo Miki harda Kaya "Toh taimaka min na tashi " A hankali a mike Yana lalube na harya lalubo hannuna ya Kama na mike a hankali na sauka a gadon Ina "takalmina"? Na manta ban hada Miki ba komawa nayi na zauna a bakin gado "gaskiya ni bazan iyya taka tiles na asibiti ba takalmi gaskiya" toh ga nawa kisa Yana fada Yana cire mini ciny'ayyen silifas insa "ah ah innasa naka kaikuma fa"? ba damuwa Zan tafi haka "Bazanfa saka ba sai dai ka saimin sabon silifas abakin get" Wallahih ban fita da kudi ba sai dai in Khadija tazo taji da dauko Miki"toh" na basa amsa Ina k'wanciya a Kan gadon, Khadija bayan fitar yayanta dakin ta fara kimtsawa ta share ta cire zanin godon ta shimfida wani ta share baranda da kasa ta hada wanke wanke tayi kafun ta shiga kitchen,da yake akwai NEPA ruwa ta daura a hot-plate ta zuba ruwa ta rufe, ta dauko wani bojuwan daban ta daura shima ruwan ta saka ta rufe Daya ke hot-plate in Mai uku ne, Tattasai ta dauka da dogo dogo sai albasa ta hada ta juye a blander Dayake taga yanda Sumayya tayi ranan da suka shiga kitchen kunnawa tayi ta markada she Kara Kara baiyi laushi ba dai dai irin na miyan taliya, Sannu ishesheya munafukar yarinya uwar me kike a kofar har yanzun Naga fitar *makaho* tun dazun ya fita? Taji muryan inna asabe take fada tana shigowa kofar Inna Aunty Sumayya ce ba lfy shine Yaya yace na musu girki, Oh lallai ai sai ke in zai Kira don duk gidan nan ba bawan sa Kala Khadija batace Mata ba Dan ubanki bara na kawo kwanona ki zubamin inkin gama saura kisamin kadan, Kala Khadija batace ba tana cigaba da gyaran waken da ta iba cikin Kofi Daya da rabi Keee ishassheya bakiji me nace bane Naji innah ,ta Bata amsa Fita Inna asabe tayi sai gata ta dawo da katon kula ta ajema Khadija a gaba ta fita abinta Ruwa na tafasa ta sauke taliya daya ta juye a tukunyan ta barbada gishiri ta rufe, dayan bujuwan wake ta wanke ta zuba ta rufe shima ta saka Masa gishiri, Wani sabon bujuwa ta daura ta zuba Mai da albasa Yana soyuwa ta juye kayan miyarta ta soya ya soyu tukum ta saka ruwa ta bare Maggi tasa da onga classic Wanda ta gani duk a cikin kitchen in caton in kefe ta bude ta dau uku masu kyau ta aje a roba,ruwan zafi ta zuba a kettle Yana tafasa ta juye akan kefen ta barsa yadan d'auki seconds kafun ta tsame tasa a ruwan sanyi ta gyara ta juye a miyar ta rufe Daidai lokacin taliya ya nuna saukewa tayi ta juye a k'wando ta tsame, Fita tayi a kitchen in ta dau omo da sabulu ta hada wankin yayanta Dana Sumayya harda zanin godo ta fitar waje ta aje ta fara iban ruwa a rijiya tana wanke kayan dashi lokaci kankani ta Gama wanke wa ta shanya a igiyar kofar shashen, Kitchen ta shiga ta duba miyar ta nuna saukewa tayi,ta dauki wani kula a caton insa Mai azabar kyau har Yana daukar ido Mai guda hudune uku ta dauka ta wanke dayan ta zuba taliya daya Kuma Miya sauke waken tayi shima ta juye a dayan Kular, K'wando babba na kaba Mai kyau ta jera kulan a ciki sai lokacin ta Tuna kulan Inna asabe zuba mata, tayi, Ta shiga daki firij ta bude ta dauki drinks guda biyu sai ruwan gora biyu ta hada a k'wandon da plate biyu shukali biyu,.. Wanka ta shiga tana fita ta maida kayan da tazo dashi, Jin ana Kiran azahar tayi Alwala tayi sallah, Ta dauki sallaya ta ninke tana kokarin rufe kofar dakin sai ga Inna asabe tana zuwa kitchen ta nufa ta bude kulanta ganin abinci a ciki Kuma Mai yawa yasata dauka tayi gaba abinta, Rufe kofar tayi ta dauki k'wandon ta fita a shashen shima ta rufe kofar ta rike key in ta fita dashi lokacin karfe 1 na Rana hanyar FMC ta Kama da kafa, ***********Har lokacin muna zaune nida shi anzo an sake daura mini ruwa,Yana zaune cikin wani yanayi duk da na Saba ganinsa sanyi sanyi Amma nayau yafi na kullum Wanda bansan daliliba, Jin an fara kiraye kirayen sallah yasashi tashi Yana lulube yake cemin bara yaje sallah ya dawo,da "toh" na amsa masa, Fita yayi yaje masallaci yayi sallah ya zauna agun sai kusan 2 ya mike ya nufu Hall in emergency har yayi nisa yaji muryan Khadija daga nesa tana k'wala Masa Kira, Juyawa yayi saitin inda yake jiyo muryar Tata ya tsaya harta karaso Khadija kin isone? Eh Yaya na karaso tun dazun Amma ban gane dakin da kuke ba, Muje toh Khadija ya fada Yana tafiya,itama binsa tayi a baya,. Yaya ya cikin nata? ....Da sauki Khadija Yaya Yana ganka cikin damuwa haka meke faruwa ne Koh kudin magani ne baka dashi? Khadija Ina Zan samu kudin magani in badon Allah ya rufamin asiri ba ya hadani da wani bawan Allah ba ya biya mini kome na magani, A Ina ka Sansa Yaya? Bansan Saba yadaice sunansa Ammar Toh meke damunka? Wallahih khadija appendix ke damun Aunty ki Kuma kudin operation naira dubu hamsin shine yake dagamin hankali banda sisi Koh abinda Zan sayar na biya Amma yaya baka ganin gara a fadawa Aunty tunda bazata rasa kudi a hannunta ba, tabiya ?? Ah ah Khadija karki fada Mata yanzun Ina son in munje ki zauna agunta ni Zan fita Koh Allah zaisa na samu bashi, Habba Yaya wazai baka bashi tsakani da Allah fa Kaida Koh sisi baka dashi in ba mangoron da ya rage jiya ba wazai baka bashi' Khadija kedai ki tayani da Addu'a na Allah basa karewa Hakane kam Yaya Allah yasa ka samu Yauwa ameen Khadija ta Daidai lokacin suka iso dakin, shiga sukayi Ina kwance,sauke k'wandon Khadija tayi tana gaidani Aunty Ina kwana? "Lafiya Khadija" Ya jikin ki Aunty? "Da sauki Alhamdulillah" "Khadija kiramin nurse tazo ta cire mini ruwan nan na samu nayi Sallah" Toh Aunty tace, tana fita,sai gata da nurse sun dawo cire mini sukayi, "Khadija hau godon ki zauna ki ban takalmin ki bara na shiga toilet" toh Aunty, *Ta kalmin nata NASA shi Kuma ya bawa Khadija tasa ta saka ya lalube bakin gadon ya zauna **Da taimakon Khadija na shiga bandaki ta koma ta dauko mini brush da maclen,da kayan da Zan saka, ***Wanka nayi da brush nayi Alwala na fitoh a hankali nake takawa Ina bin bango harna bude kofar na fitoh Da sauri Khadija
Chapter 8 · 0% Book details