Sashe 69
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
matata bata da lafiya na barta koh karyawa batayi ba. Kai muahmmad banace kaci abincin gaban kaba, koh bakaji bane? Ai da sauri ya fara cin abincin, jikinsa na bari. Kasan me mukeso dakai muhammad? Ah ah sai kun fad'a ya basu amsa abinci cike a bakin sa, don ya tsorata ainun, tura abinci kawai yake. An bamu kwangilar kashe ka, Amma mu bazamu iyya kashe ka ba, don shekarun baya mune tsilar makantar ka, wanan karon bazamu iyya d'aukar ranka ba, bakaji ba, baka gani ba, ana buwayan rayuwar ka. Innalilahi kune daman wa'inda kuka zubamin abu a fuska, na makance? Ba zuba maka abin bane ya makantar dakai muhammad, tafiya mukai dakai a wancan karon ma. Toh me nai muku kuma, waya saku?yana maganar yana kuka. Kai mana shuru,abinda muke so dakai yanzun shine xamu fitar dakai daga NIGERIA, Bama son ka kara taka kafar ka a wannan kasar, kaje can kayi rayuwar ka, yafi maka Alkhari sama da zaman ka a kasar nan. Toh don Allah ku bari na d'auki matata da kanwa ta, saimu tafi tare wallahi na muku Alkawari bazamu sake taka nigeria ba. Kaiiii kana wasa da ranka koh? ana maka gata kana kokarin sa kanka a matsala, an gaya maka koma warka gida yanzun baka bata mana aiki bane, don haka barin kasar nan dakai ya zama dole mundin kana son rayuwa mai tsawo Don Allah ranka ya d.... Bai bari ya karasa ba yace, rufemin baki wawan banza kawai, kome mata mata ai akwai mata da yawa a duniya, in sake jin ka am bace Hakuri anan saina sumar dakai nosense. Shuru muhammad yayi, agun suka kwana washe gari suka kama hanya, wanda shi ba gani yake ba bai san ma ina ake jansa ba. Lokacin da aka zo tsallaka border da muhammad ana tsallaka nigeria wani irin ihu ya sake yana birgima a cikin motar, ji yake kamar ruwan zafi aka watsa masa, sosai yake salati yana kuka jin jikinsa na tafarfasa. Abin mamaki mutanen basu wani damu ba, kuma abin bai basu mamaki ba, d'aya daga cikin sune ya masa Allauran bacci a take jikin sa ya sake. Ta bangaren sumayya sai da ta kwana biyu kafun ta dawo hayyacin ta, tunda ta farka sunan muhammad kawai take kira sai kuka, zaune take akan gadon asibiti An d'aura mata sabon ruwa a hannu, inka ga sumayya saika tausaya mata tsabar rama da tayi, Likita ce ta shigo d'akin, sumayya ta kalla ta sake kallon goggo dake zaune a gefe, ga khadija ma zaune tayi tagumi gabaki d'ayan su wujiga wujiga suka koma, abin tausayi. Sannun ku yamai jikin? Da sauki likita, goggo ta Amsa mata. Masha Allah, sumayya kam tana da mijine? Eh likita tana da miji. Ok koh zan iyya ganinsa? Kuka sumayya ta sake mai tsanani, tana dafa kirjinta jin zafin da yake mata. Subhanallah sumayya ki kula da lafiyar kifa, kina kokarin d'aurawa kanki wani ciwon kuma akan wanda kike dashi. Dole nayi kuka Dr mijina aka sace shikaran jiya da safe. Amma kun kai report wajen yan sanda kuwa? Ah ah waye muke dashi, da zai kai mana report, yan sandan ma in kaje sai sun nemi wani abu agun ka, mu ina muka ga abinda zamu basu. Duk da haka gwara kukai report yafi, sannan ina son kuban waje zanyi magana da sumayya? Ba kome likita, goggo tace tana fita, khadija ma tashi tayi tabi goggo har lokacin bata daina kuka ba inta tuna yayan ta. Sumayya hawan jini kika samu ya kamata, ki nutsu kisa tawakkali a ranki kiyi hakuri insha Allah mijin ki zai dawo. Dole nayi kuka Dr mijina shine kad'ai farin cikina daya saura mini, sannan a waye gari ban gansa ba dole na shiga damuwa. Kiyi hakuri, sannan ya kamata kima mahaifiyar ki magana ta ringa xuwa miki da ruwan zafi, kina zama a ciki saboda yanayin jikin ki kinji Allah ya sauwaka. Ameeen nagode likita, sumayya tace tana kallon likitar bazata wuce sa'arta ba koh ta bata yan tsiraran shekaru. Ta bangaren muhammad Sai da sukayi sati suna tafiya a motar, kafun suka iso kasar da suka shirya kaisa. Suna shiga kasar da suka yanke zasu aje sa, d'aya daga cikinsu ne ya kalli ogansa, oga anya wannan yaron, bazaice zai dawo kasa ba kuwa, ka sansa akwai fahimta ni inso samune mai zai hana a masa yanda zai manta da kome, na d'an wani lokaci. Bazai yuba hakkin yaron nan ya mana yawa, mu barsa haka wannan karon bazan sake cutar da yaron nan ba. Shikenan oga amma naga hakan ma, taimakon sa muke son yi, don mun masa hakan ba kome bane. Gaskiya ne oga, d'aya daga cikin su yace Kai ban Amince ba ku aje yaron nan mubar kasar nan, kar a kamamu jirgi ma zamu bi, bada mota zamu koma kamar zuwa ba. Haka suka aje muhammad suka kara gaba. Kamar Awa d'aya da tafiyar su muhammad ya farka, A hankali ya motsa hannunsa sai kuma ya fara kokarin bude idanusa a hankali, ya bude su yana kallon sararin samaniya, ai da sauri ya mike zaune, mafarki yake koh gaske jikin sa har rawa yake yasa hannu ya murza idon sa da kyau don kara tabbatar wa kansa abinda yake gani, gaskiya ne koh A mafarki yake............... *MATAR MAKAHO* ~ Na ~ *Rukayya Ibrahim* Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa Free book Page6 Mafarki yake koh gaske, da idanun sa yake kallon duniya, wanda rabon sa daya gani yanzun ana neman shekara 13, Allahu Akbar Tsarki ya tabbata ga Allah, Alhamdulilah Alhamdulilah, shine abinda yake maimaitawa Mikewa yayi da sauri yana bin koh ida da kallo, kamar wani dolo, shi ganin abin yake kamar mafarki ne, an jima zaici gaba da ganin duhu,sai bin wajen yake kamar daji, haka ya ringa takawa a hankali yana tafiya cike da Al'ajabin abinda ke faruwa yau dashi, shine da kallo? Hango gonaki yayi a shimfide, gwanin sha'awa na kayan labbu, ga kogi babba yana gudana da gudu yayi saitin kogin da saurinsa ya shiga ruwan, don wallahi azababben kishi yake ji, ai yana shiga kogin ya tsoma hannun sa cikin ruwan ya iba yasha, ya sake tsoma wa ya iba yasha, kamar wasa yaji ruwa yana jansa daga bakin gaba, har tsakiya sai kokari yake ya fitoh amma ina abin yaci tura, salati ya fara yana innalilahi, wasa wasa ruwa ya fara nitsar dashi sai kokowa yake da ruwan, duk kokarin sa na fita, abu ya gagara, daman shi ba ruwa ya iyya ba, ina makaho ina rafi, koh lokacin tasowar sa baiyi yayin bin yara kogi ba. Sosai ruwa ya hadiye sa har wuya, sai kokari yake Amma ruwan yafi karfinsa, zuwa wani lokaci, shuuuuuuuu yaji ya burme cikin ruwa, da sauri yayi tsalle yafitar da kansa, sai kuma yaji ya sake komawa, kamar wasa Al'ameen ya fara shan ruwa, sannu sannu har yaji ruwan yaci karfinsa, tun yana gani dishi dishi har yaji bayanan , Gid'ado ne tsaye da shanun sa, daya koro bakin gaba susha ruwa, kamar wasa yaga shanukan sa, na kuka a bakin gaba, Alamu dai wani abin suka gani. Da sauri ya karaso wajen don yayi tunanin kada ne, koh wani mugun abu, tsayawa yayi turus yana bin abinda yake gani shida dabbobin sa, mutum ne, kwance baya motse kamar gawa, da sauri ya kad'a shanunsa har ya juya zai tafi don gudu rigima, daman ba shiri suke da manoma ba kar ace shiya kashesa, ya shiga uku. Sai kuma ya sake dawowa, haka kawai yaji hankalin sa bai kwanta da tafiya yabar gawan ba, nade kafar fantalelen wandon sa, na kiwo yayi ya shiga ruwan, jawo Al'ameen yayi, kiiiiiiiiii ya fitar dashi a ruwan, ajesa yayi a kan tabon bakin kogi. Kurawa fuskar Al'ameen ido gid'ado yayi tabbas wannan ba kabila bane, duk da fuskar tayi irin na fulani,Amma ba fulani husul bane, kyaun sanan akwai mix,ganin Hakan yasaka sa ciccibar Al'ameen, ya d'aura a bayan wuyansa yayi Rugan su dashi. Tun daga mahadin rugan su ake binsa da kallo, ganinsa d'auke da gawa a wuya, kowa ya tare sa, cemai yake shima a ruwa ya gansa, sosai wasu ke zagin sa meye na kawo musu gawa salon ya jaza musu bala'i, Amma shi sam bai damu ba tafiyar sa kawai yake. Isarsa gida ya tarar da mahaifinsa zaune a gindin bishiyar tsada a tsakar gidan su, sai innar sa dake gindin murhu tana girki. Assalamu Alaikum Waalaikum.......sai kuma ta dakata, bata ma karasa amsa sallamar ba, hadde yan boni, gid'ado dun dume, miyiyata do ha bahoma?(me nake ganin nan a bayan ka) Shuru yayi yana kallon ta, ganin yanda gabaki d'aya tabi ta gigice, bappan sa dake zaune a gindin bishiya ne, yayi saurin tasowa jin abinda inna kece wa. Gid'ado d'obo?bappan sa ya tambaya, yana nuna Al'ameen dake kafadar gidado. Bappa, kuyi hakuri bara na sauke sa sai in muku bayani, duk cikin fulanci suke maganar. Wani irin mu kwantar da hankali?kawai ka ciccibo mutum baya motse a kafad'ar ka, ka shigo mana ruga akan me? Don Allah inna a wad'a muyal, nima ganin sa nayi a bakin gaba, alamu dai ruwane ya jasa, koh aka yardashi, gidado yace yana kallon matarsa data fitoh daga d'aki, d'auke da tsohon ciki tana nufosu. Kwantar dashi gid'ado, in yaso koh sallah Amasa tunda naga kamar musulmi ne, bappa yace. Sauke sa gidado yayi, sosai bappa ya kurawa fuskar muhammad ido, yana nazari sai kuma ya d'aga ido yakalli gidado, Ai ohmayai(ai bai mutu ba)suma yayi. Da sauri gidado ya kara maimaitawa suma bappa? eh, yi sauri ka d'auko mini kwaryar magani a bukka, yana maganar yana dukawa kusa da muhammad, danne masa ciki ya farayi, take ruwa ya fara fita, ta bakin sa duk da baiyi motse ba, amma dai ruwan na fita sosai, bappa ya mammatse masa ciki. Matar gidado kam kujera ta samu ta zauna a hankali daker, sai ga gid'ado ya fitoh bukan bappa, da sauri ya ajewa bappa magani a gefe, bappa da lenki mai. Maganin bappa ya d'auka a kwarya, yana shashafa ma Al'ameen a fuska, da wuya yana masa Tofi,yana gamawa ya d'aga ido ya