Sashe 4
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gera daki na na jona kask'wan lantarki na zuba Turarukan wuta a dakin fita nayi Naga har yanzun Yana Kan wanke wanke Kwanukan akwai Dan yawa na abincin jiya da yara sukaci ban samu na wanke ba Harda na dare, *Wanka na shiga Ina fitowa na tarar ya kammala Yana zaune a kujiran tsugunne, " Koh Mai ban shafa ba na zura kaya atamfa super Mai kyau siket da riga Mai k'wala da hannun roba* dinkin zamani *abinci na zuba ina ci daidai lokacin shima wankan ya shiga yana fitowa wanka ya shigo dakin, Alhamdulillah Koh ba kome na Lura Yana da tsafta duk da bana rayawa a Raina Koh da Wasa zanyi rayuwar aure dashi Mai tsayi dole ya sake ni yaje ya nemi miskiniya irinsa Amma kafun lokacin bazan cutu da wari ba tunda Yana wanka ( lol uhmm muje zuwa zakiyi bayani ) *Fita nayi na basa waje* Kaya ya saka wani jimemmen t-shirt da wando jeas duk da tsofene Amma sunyi Masa kyau sosai ya laluben kujira yayi ya zauna, Ina waje ban kulasa ba naci gaba da cin abinci na kammala zamana nayi A wajen naki basa abinci shi kuma Bai tambaye ni ba Danna waya nayitaye sai kusan goma na safe na iba Masa a plt da shaye a Kofi na shiga dakin na aje Masa na koma Kan gado na kwanta, ya jawo plt in yayi Bismillah ya fara ci Yana tsaka dacin abinci muka ji bugun kofar shashen mu mikewa yayi zaiji ya bude na dirko daka kan gado cikin fada fada nace "bazafa ka bude kofar nan ba don yau bamai shiga kofar nan ehen kaji na gaya maka don Naga alama Yan gidanku basuje islamiyya ba" Baice mini kome ba ya koma ya zauna Jin Mai bugun yaki barin kunne na ya huta, hijab na dauka na zura na fita ,don gani wani isheshshine, Bude kofar naye idona y sauka akan wata yarinya kyakkyawa sosai farace Mai Kama da MAKAHO sak banbancin ita mace Mai karancin shikaru 18 zuwa 19 she Kuma namiji ne sanye take cikin riga na kodadd'in shadda sai hijab wuyan duk ya sabule gashinta har ya leko ta gaban goshi, *Tunda aka kawoni wanna kaddararerren gida ban ganta cikin yaran gidan da suka zo kofana ba, Aunty Ina kwana tace hanya na Bata cikin dakewa nace "lafiya shigo" Shigowa tayi daidai lokacin shi kuma ya fitoh cikin dakin murmushe dauke a fuskarsa itama murmushin take da sauri tazo ta amshi kwanukan hannunsa hade da gaishe sa ya amsa,Yana tambayar ta ya su Goggo Aminar, Ta basa amsa Tace in nazo nace tana gaida Amarya,ta fada tana kallona Amsa Mata nayi ba yabo ba fallasa "Ina amsawa" Fita zaiyi hade da tambaya ta Koh akwai abinda za'a saya Kai tsaye nace "babu "sa Kai yaye ya fita hade da cewa Khadija in Zaki tafi ki biya ta guna, da toh ta amsa Masa Nidai daki na wuce naje na kwanta sai da Naji fitarsa tukum na kwala Mata Kira " Khadija shigo daki Mana kina tsaye a waje" don haka kawai naji yarinyan ta kwantamin sosai a Rai duk da bansan Alakarsu ba amma nasan akwai alakar jini a tsakanin su, Da sallama ta shigo dakin na amsa Mata tana kukarin zama a kasa nayi saurin cewa tahau kujira Amma Taki da kerta zauna, firij na bude na dauko mangoron jiya da yayanta ya kawo na hada Mata da drinks harda ruwa na aje mata hira take mini Kamar na saba da ganin akwai ta da surutu sosai tun Ina amsa Mata har bacci ya dauke ni, Ban farka ba sai 1:30 na Rana shima kiraye kirayen sallane ya tashe ni sai a lokacin na tuna Ashe fa Ina da bakuwa, A hankali na sauke idona akan kujiran da na barta akai da mamaki sai Naga wayam ba kome, Sauka nayi a gadon na fita a dakin cike da mamaki nake bin kofar da kallo har idona ya sauka akanta cikin sabon mamaki ganin ta a cikin.................... Good morning fan's An gaishiku Yan free books MATAR MAKAHO FAN'S GROUP Naga comments naku naji Dadi Kuma Ya karfafa mini gwwa My WhatsApp number 08084453785080844537850808445378508084453785awata ta kaina Salma Adam Allah ya bar *MATAR MAKAHO* ~ N *Rukayya Ibrahim* Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa Free book *More comments* *More post* Page6 shanyan Kayana da sukaye datti harda zanin gado Ashanye a igiya an wanke harda kayan yayan Khadija (MAKAHO) Khadija na gani cikin kitchen, tana aiki, * a Hankali na daga kafata na Isa kitchen in, "Khadija kece akitchen?" da murmushi a fuskarta ta amsa mini da Aunty, Naga har Rana baki tashiba shine na daura Miki Abinci shinkafa da wake miyane ban Gama ba ya kusa, "Kayan nan fa waya wanke ?" Nice Aunty ta bani Amsa, *wallahih in banji Dadi ba nayi karya sosai naji yarinyar ta shiga Raina sosai da fara'a nace Mata" gaskiya Khadija nagode wallahih Amma aikin ya Miki yawa da baki wanke Kaya ba, La Aunty babu yawa fa kayan, ta bani Amsa "Khadija tashi muyi Sallah tukum tunda miyar kin daura a wuta" ..Toh Aunty Sallah mukayi, na sauke abinci na raba na zuba Masa na hada Kamar jiya, na Bata ta Kai Masa " in kin Kaifa ki dawo Khadija" da toh ta amsa mini, Tana dawowa na iba Mana nida ita a plt daya, Muka zauna a waje munaci muna Hira cikin hiran nema nakejin ainahin sunan sa a bakin Khadija Ashe *Al'ameen* ne sunan sa saboda larurar da Allah ya daura Masa shine aka batar da sunan zuwa MAKAHO Kai duniya, "Tambayar ta nayi a gidan nan take"? Ah ah Aunty ni agidan Goggon mu nake , "Har wani unguwa ne haka"? Ta bayan layin nan ne tsakanin mu ba nisa sosai Aunty, Sosai muke Hira Kamar mun Dade da sabawa, "Aikin dare na hanatayi nace ta Huta ni nashiga kitchen nakama girki* kin zama tayi dutsen guga ta dauka ta fara gogan kayan da ta shanya duk yanda na hanata sai da ta gogi, 4:10 na yamma tace min zata tafi hanata, nayi sai da na Gama girkin abinci na sata tayi wanka Kayana na Bata cikin dogayen rigunana nakanti na Bata daya Dayake tana da tsawo sosai ya zauna Mata na hada Mata da gyele medium size kalar fulawar rigan, Sosai kayan ya karbe ta na hada Mata da Mai turare harda powder,man baki, da Jan baki biyu, maskaras da sauran kayayakina da basa cikin set na make-up kit Ina na babata daker ta karba sai godiya take min, *nayi nayi taci abinci dare Amma Taki,zuba Mata nayi a kula Taki karba sai da nace Goggo zata kaiwa kafun ta Amsa ta wace, Fitar Khadija sai da ta biya wajin yayanta sosai take basa lbrn abin arziki Dana Bata da irin sakar Mata fuska da nayi, Har cikin ransa yaji dadin daraja.masa kanwa danayi sosai, Hatta damuwar da ya fita da ita na safiya ganin yanda yau na tashi da zafi zafina abin ya tsaya Masa a Rai, Wannan abinda nama Yar uwarsa tilo da yafi so sai yaji zuciyansa wasai. Mangoro ya bata hade da naira dare ta rike a hannunta ya kara Mata nasiya sosai da hakuri A duk inda Allah ya ajita kafun ta wuce, *Khadija na fita wanka nayi nasa siket in kanti da t-shirt Mai kyau na daura gyele karami a kaina laptop na..... Sai kusan shidda ya dawo gida yauma da kwandon sa a hannu, da sallama a bakin sa *amsa Masa nayi, kaina nakan laptop, * Wanka yayi ya tafi masallaci yauma Bai dawo ba sai Isha waje na fita ganin yau ba NEPA, na fitar Mana da babban darduma na shimfida, *abinci na iba masa, nasa nawa na aje Mana tare da Masa Bismillah zama yayi shima Muka fara ci * Khadija ta tsanar Dani abin arzikin da kika Bata na gode, naji muryansa cikin sanyi sanyin sanan, Ba kome wallahih abinda ba yawa, Jin yanda na Masa magana a mutunce abin sai ya Masa Dadi sosai, mun Gama cin abincin har lokacin NEPA shuru na kasa shiga dakin saboda tsananin zafi da ake yau ga sauro, Tashi yayi ya fita yaje ya sai Mana maganin sauro, Yana dawowa na karba na kunna, kitchen na shiga na yaga caton in indomie, zanyi fifita dashe, * Wanka na sake shiga tsaban zafin da nake ji Kaya nasa vest sai wando Yale yale dogo har kasa, Kushin na dauko a daki na zuba akan cafet in na kwanta Ina fifita,Yana zaune a gefe shima ya jingina da jikin gini, Shuru mukaye dukan mu ba Mai magana,shikam tunani yake azaman da yaye da Sumayya ya fahimci Abubuwa cikin halayan ta, in Abu ya Bata Mata Rai, toh kowa ta shafa, in aka faranta Mata kowa zaiga fara'ar ta akwai ta da tsafta akwai iyya girki ga nutsuwa sam.bata da rawan Kai, *Har Sha biyu bamu shiga ba, ganin dare yayi ban tashiba ya mike a hankali yaji ya rufe kofar shashen mu, ya dawo ya shiga dakin ya cire kayan jikinsa yadau wando iyya gwuiwa sai riga Mara nauye , ya dauko filon kujira ya rufe kofar dakin harda k'wado key in yasa a cikin filon sa, Dawowa yayi ya tsaya a gefe cikin sanyin jiki yace "uhmm Daman Naga Kamar baki shiga daki ba kwanan waje zamuyi kenan? "Eh wallahih Amma tunda akwai maganin sauro"? Sake tambaya yaye in akwai wani abin kwanciyan a bani,Gefen dardumar na nuna Masa ya kwanta hade da furta" ita dayace" kwanciya yayi tare da Addu'an bacci, a hankali bacci ya dauke sa *Sai kusan karfe daya kafun bacci ya dauke ni da ker' Saboda rashin samun bacci da wure da bayi ba shiyasa yau Bai tashi yin sallar dare ba *Nikam ban sake sanin kaina ba sai asuba........ Ayi manage ba yawa Masu complain in page na kadan My WhatsApp number *MATAR MAKAHO* ~ Na ~ *Rukayya Ibrahim* Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa Jumma'at Mubarak to All my fan's Free book Page7 *A hankali nakejin sanyin asuba na ratsani har cikin kashi kowa yasan