← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 104

Sashe 103

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page1 Wani irin magana ne haka nabila?toh nidai baza'ayi wannan haukar dani ba, kinji na fad'a miki taya yaro da matarsa koh sanin dadin aure basuyi ba, gani tsohowar banza nazo nasa bakina a sha'aninsu salon nayi bakin jini a wajen baiwar Allah, yarinya na ganin girmana najawa kaina raini wallahi da sakel ki barni na mutu da mutunci na. Kuka nabila ta sake cikin maganar shagwaba tace, ni shikenan babu inda zanje naji dadi, dedena naje mata da zancen zagina tayi kema shine xaki mini haka? Jin abinda tace yasa mahmah kashe wayar ta aje ta fita a d'akin. Ammar yazo sun gaisa da khadija kuma ba laifi ta sake jiki dashi kad'an, kuma yana samun hankalinta, Amma ba karamin kunyar muhammad yake jiba duk lokacin da zaizo sai ya tambaye khadija a waya yayan ta na nan intace eh tofa ba zuwan zaiyi ba. Bayan sati uku Ayau ne dubun Al'umma suka shaida d'aurin auren sarki yusuf mutallaf tare da Amaryar sa zainab Rabi'u ubangari sai kuma Abdulsalam Abdul'Aziz shugaba da Amaryar sa Amina Ahmad Adara, d'auren auren da ya samu halaktan manyan mutane daga nijar har nigeri'a tabbas yan uwan zainab sun nuna mata gata a bikinta. Bayan d'auren Auren ne mahafin Ammar ke wa yusuf zancen khadija, wanda yace sai dai aje nijar ayi batun Auren tunda canne mahaifarsu kar yan uwa suga ana musu wariya. Su sumayya da muhammad harda khadija ayau sukabi gida gidan yan uwa domen musu sallama, washe gari taje abuja tama mahaifiyarta sallama zasu tafi nijar wajen dangin mijinta, kuma daga wajen zasu wuce America. Ayau ne sumayyya dasu khadija da mahmah tare da tawagar sarki da Amaryar sa,suka nufi nijar, sun samu kyakkyawar tarba, saidai fa sumayya ta fuskanci sauyi a wajen nabila wanda hakan yasata shawa nabila mur, ganin duk lokacin da taga Al'ameeen zatana wani kwarkwasa shikam baima nuna yasan tanayi ba, ga lawiza da kishi ke cinta, Amma dai ta kwantar da hankalinta ganin yanzun tana samun kulawa a wajen mijinta fiye da da. Nabila tayita nacewa mahmah akan zancen ta da muhammad, wanda abin yasa mahmah tarar yusuf da zancen, kai tsaye yace mata, mahmah banki bin umurnin kiba amma mama inkin duba duk abubuwan da suka faru Nine na fata ballo ruwan, da ace nayi biyayya ga mahaifina da duk abinnan bai faruwa ba, duk da bawa baya wuce kaddararsa mama bazan iyyama muhammad wannan zancen ba,A tausayawa yaron nan yasha wahala A rayuwar sa yanzun lokacine daya kamata Ya huta, duba da irin halakcin da yarinyar nan ta masa bata cancanci haka ba, in shine ya taso da zancen aure bazan hanasa ba, Amma mama bazan iyya tikasta masa ba kiyi hakuri bawai don yana d'ana ba, zaki iyya tuntubarsa duk Abinda ya yanke shikenan. Jikin mahmah yayi sanyi kuma taji shawaran da d'anta ya bata don/a dalilin Auren dole yusuf yasha wahala, hakan yasa bata ma tinkare muhammad da zancen ba. Gidado da badaru dayake ba boko sukayi ba, kuma yanzun sun wuce shiga makaranta, yasa sarki bada umurnin a sasu a islamiyya, da kuma yaki da jahilci koh karatun hausane da turanci su iyya,ya bude musu manyan shaguna a kasuwa,in sunje boko sun dawo sai kuma su tafi shago, asabar da lahadi suje islamiyya. A kasuwa gidado ya hadu da indo kanwarsa na bara, cikin wani irin yanayi ya tisata har inda suke da zama, aiko suna zuwa saida yayi hawaye ganin wani kazamin waje kusa da bola innarsa ke rayuwa gata a kwance ba lafiya ga yarsa cikin datti ,sai abinda indo tayi bara ta sama musu, d'aukar su yayi wanda a lokacin inna koh sanin wake kanta batayi ba. Sarki a washe garin ya tura su saudiya da inna,saboda ciwonta ya kazanta blood Cancer ne, yayinda indo ke zaune a gidan sarki tare da lantana karama. Muhammad da sumayya sun wuce America tare da yaransu suna mai kewar kasarsu da yan uwansu. Bayan tafiyar su akayi auren Gidado da nabila sai badaru da wata yarinya yar tsohowar unguwansu, sarkin shayi ma Yusuf ya had'asa da wata bazawara an had'asu aure. Jikin inna yayi sauki inda sarki yasai musu gida ita da indo da yar gidado , d'aya shashin kuma gidado ne da nabila, dataga ba sarki sai Allah ta aure sa abinta. Su sumayya basu dawo ba saida sukayi shekara d'aya, lokacin auren khadija da Ammar sukazo, khadija tayi weac dayake har lokacin tana Nigeria a abuja wajen hafsa, yayin da yaran sumayya suka cika shekara 1 da watanni a lokacin kowa yaga sumayya da muhammad sai sun basu sha'awa, gaskiya ne mahakurci mawadace, mai hakuri yana tare da riba, sannan duk mai biyayya ga iyaye zaiga Amfaninsa wata rana. Ana bikin Ammar da khadija suka koma wajen aikin Ammar a maiduguri bayan aure ya maidata makaranta, don result nata yayi kyau sosai, su sumayya sun koma America bayan biki. *************** Bayan wasu shekaru......... Wani matashin magidanci ne tsaye a wani hadedden compound mai d'auke da shuke shuke mai ban sha'awa, sanye yake da kakin sojoji a jikinsa wandone da riga, kansa ba hula sai gashinsa dake kwance baki kirim yana sheki, yayi farine tas yayin da idanunsa ke d'auke da bakin glass, dukar da kansa yayi yana kallon agogon sa mai masifar tsada, dake hannunsa d'an yamutsa fuska yayi hade da dan sakin tsiririn tsaki,ganin 7:21pm Amma har yanzun gimbiyar tasa bata fitoh ba bare yaransa, jin karan bude kofar falonsu da akayi yasa sa saurin d'agowa. Sanye take da siket baki mai kauri yana nan kamar pencil Amma ba'a tsaga baya ba,sai takalmi mai tsini a kafarta dake d'auke da socks baki, shirt ne a jikinta white mai botur da dogon hannu, wanda tayi stokin dashi, Have sunnah ne a wuyanta baki, da agogo fari a d'aure a farin tsintsiyar hannunta, sai jakan office dake rataye a hannunta d'aya Tabar daya hannun na lilo, fuskar nan nata yayi fayau babu kwalliya alamu dai jin dadi ya samu waje, rike take da wani kyakkyawan yaro fari yana sanye da uniform na primary bazai wuce shekara 5 ba, ga wani yaron na binta a baya zaikai 7 shima yana sanye da uniform hannunsa d'auke da jaka d'aya hannun kuma lunch-box nasa. Da sauri ta kara hanzartawa ganin fuskar mijin nata a hade, don tasan tabbas sun sasa jira don yau dai sun makara. Yanzun ke kullum in zamu tafi aiki da safe sai kin sani lettin kike jin dadi, ki duba yanzun minutes 30 ina tsaye ina jiranku? "Don Allah kayi hakuri dear wallahi neman socks in na'ima nake wai bataga d'aya ba" Toh surutun ma ai ya cinye lokacin daya saura manan, yace yana kamo yaron dake hannunta ya bude seat back ya ajesa, kallon mai shekara bakwan yayi, Au kaima salim(takwaran salim marigayi, muhammad ya hana a masa inkiya yace a barsa da sunan sa)so kake na d'aga kane koh me? kana tsaye. Washe fararen hakoransa yayi cikin dariya ganin yau ran baban nasu a bace, yace, sorry Dady. Shiga gaba sumayya tayi ta aje jakanta akan cinyarta da mamaki Al'ameen yake kallonta, wai sumayya ina sauran yaran ne? "Au wai basu shiga bane tare fa muke futowa dasu" Kinsan Allah sumayya yau in kikayi tsiya sai kija mota da kanki tunda dai naga kowa nada shi, ya fad'a a hankali yanda yaran bazasu ji ba. "Kayi hakuri toh" kawai tace tana fita a motar daidai lokacin wasu yaran mata da zasukai shekara 10 masu tsananin kama da juna, gasu kyawawa sanye suke da uniform suna gudu da school back a hannu d'aya nabin d'ayar da gudu. Da sauri sumayya ta kalli wance ake binta da gudun, tazo ta makale a bayan Dadynsu,"Na'ima mekika mata"? Momy wallahi babu abinda na mata. Kallon na'ifa dake hawaye a gefenta tayi, tana tsaye batabi na'ima bayan dadyn sun ba" meta miki kika biyo ta"? Wallahi momy colour nata d'auka guda hudu, kum drewing zanyi dashi fa. Ke na'ima ina naki colour da zaki d'auka mata nata? Dady toh banga nawan bane bafa. Da sauri sumayya ta karbi maganan jin Amsar data bawa muhammad"Daman ke haka kike kome naki ba'a gani, kina ganin da safen nan harkin batar da socks naki daker na gane inda kika aje, kome naki baya lastic wannan biro in aka saima yar uwarki sai yayi 1 month tana amfani dashi, amma ke koh kwana bayayi sai kice ba pen ah ah pen ya bata, don haka oya bata colourn ta koh na saba miki"? Ba musu ta bude jakanta ta mikawa na'ifa abinta, sai kuma ta fashe da kuka. Muhammad dake tsaye ne ya dubeta, toh wai kukan na menene? Dady kuma fa bangama drewing ba gashi uncle yace duk wanda baida colour waje zai korasa bazai masa makin ba. Ina dai akan colour ne?muhammad ya tambaye ta. D'aga masa kai tayi alamun eh. Toh muje a hanya saina sai miki sabo koh?yanzun ku shiga mu wuce mun kusa makara. Dady nimafa bani da calculator? "Da sauri sumayya ta dubi yaron ta, kaji tsoron Allah khaleefa(yusuf) ba jiya naga calculator a jakan ka ba" Momy Abokina kullun sai uncle ya bugesa wai bayida calculator, shine na tambayesa mai yasa ba'a saya masa ba, wai Auntin sa(step mother)in dadynsa ya basa kudin saita kwace, shine na basa kyautan nawa jiya. "Masha Allah yaron kirki haka nakeso Allah ya muku Albarka" Gabaki d'ayansu suka Amsa da Ameeen . Jan motan muhammad yayi mai gadi ya walgale musu makeken get nasu suka fice. Sai da suka bi ta bookshop ya sai musu abinda suke bukata, yaran ya fara saukewa a school, kafun ya kama hanyar bank da sumayya, tun a hanya ta makala ID card nata a wuya, suna isa bank ta sabi jakanta sukayi sallama ya wuce wajen aikin sa. Misalin karfe 4:30 na yamma muhammad ne zaune a office yana aiki, yaji ring na wayan sa kamar bazai d'auka ba don aiki yake mai muhimmanci,d'auka yayi yana kallon mai kiran nasa da sauri yayi picking yasa a kunne,Assalamu Alaikum Ta d'aya bangaren Ammar ya Amsa wa'alaikumu salam, Captain muna fa Airport azo ya d'auke mu. Da sauri muhammad ya mike cikin mamaki yace What? kana nufin kun shigo Lagos koh note's babu? Surprise muke son muku. Amma gaskiya
Chapter 103 · 0% Book details