← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 104

Sashe 49

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page 4 Da karfi khadija ta watsar da kayan hannunta tsungunawa tayi jikinta na bari ta kama kai, gabaki d'aya ta gama sadakar wa yaukam sai Ta Allah Cikin zafin nama da haushi mai motar ya fitoh da fad'a fad'a,kee wace irin wawuyace wai kina tafiya koh ganin gabanki bakyayi da yanzun na kadeki fa baki jawo mini matsala ba gashi yanzun kinsa na buge keke napep innan da sai dai me zan buge? nosense kawai stupid Khadija kam har yanzun bata dawo daidai ba ga kuma tsawar da ake buga mata, d'aga kanta tayi tana kallon mutumin don Allah kayi hakuri wallahi bangan ka bane Da mamaki mutumin ke kallon ta sai kuma yayi murmushi, ke bakece kanwar Al'ameen ba? Eh.....eh..nice Murmushi kawai yayi hade da dukawa a tsakar titin yana tattara mata kayanta,saiki taso ai inba so kike wani motar tabi ta kanki ba Khadija kam cikin had'a fuska don sai yanzun takejin haushin zagin da ya mata, mikewa kawai tayi ta koma gefen titin Kizo ki shiga mota na kaiki gida? Bazan hauba, kuma ka bani kayana nikam. Kinji haushine khadija? Da mamaki take kallonsa toh a ina ya santa gashi itama tun d'azun sai tunanin inda tasan wannan fuskar take Ke yar Kauye bar kallona Naki dainawa kuma miko mini kayana, ta karasa maganar da kai hannu zata karbi laidodinta Da sauri ya kauce hade da cewa, ke khadija nifa yau gidan yayanki zaki kaini yau kusan wata biyu ina sintiri a sintali kowa na tambaya Al'ameen mijin sumayya sai ace ba'a gane saba yau ma Allah ne yasa zamu hadu shiyasa na biyo ta bakin kasuwa. Aikuwa bazan nuna maka ba, ba zagina kake ba Yi hakuri haushi naji Shiyasa yanzun muje ki nuna mini gidan yayan naki Gaskiya ni yanzun gida zan koma ba gidan yaya ba sauri nake iyeee nace ki nunamin gidan da nafi wata biyu ina nema shine zaki wanice kina sauri Kaga malam ni yanzun ma haka gidan na fitoh gaskiya bazan koma ba saidai nama kwatance Toh shikenan yi mini, kuma ga kayanki karki shiga motar inkin ga dama Oho maka dai, inka tsallaka titin nan sai ka mike kaga lungun shan kana shiga zakaga babban titi da yayi barade ka tambaye masu shagunan wajen, gidan Adara za'a nuna maka saika aike yaro kofar MAKAHO Ok toh shikenan naji, yace yana komawa wajen mai keken biyansa yayi asaran da ya masa, ya shiga motarsa yaja Khadija kam da ido ta bisa ta kasa tuna inda tasan bawan Allah nan Amma tabbas akwai inda ta sansa. ************** "Yayan khadija gaskiya nifa yau bazanyi girki ba wallahi na gaji wanka zanyi na kwanta " Kidaiyi wanka amma banda kwanciya kinsan bakyau bacci bayan la'asar koh? "Gaskiya ne amma dai zan d'an taba kafun goshin mangariba saika tashe ni" In ance abu ba kyau sumayya ki gujesa don Allah kidai kwantan koh waya koh TV ki kallah Amma banda bacci kam. "Toh shikenan akwai kudi a purse nawa anjima ka sayo mana abinci" Ah ah zan dafa... "Zaka dafa kuma yayan khadija, kaji mini kaudi" Nine mai kaudi? "Eh man in ba kaudi ba ina kai ina girki, salon kaje ka kone koh ka yanke ba" Amma dai wallahi sumayya kin gama raina mini wayo me kika maidani ne wai? "Sorry toh me zaka iyya girkawa" Oho..... "Yi hakuri mana wasa fa nake maka" Ba wani, ya karasa maganar yana zama a bakin dakalin "Banace kayi hakuri ba, habba danejo Am heedee Am buddi Am yafannam lee"ta karasa wakar da kamo hannunsa ta nufi kitchen in dashi Kinga sakeni nafa fasa girkin bara kiji karma ki kama mini wani waka wai ma tsaya ke bafulatana ne daman? "Bororoje ce ba bafulatana ba, kuma girki sai kayi ehen" Ke wai ana girkin dole ne? "Yau sai kayi ai duk wanda yayi niyar aikin lada sayya karasa" Toh nace na fasa koh "Nikuma nace sai kayi" ta karasa maganar da dokarasa akan kujeran kitchen in Kin zama yayi inta dosana sa saiya cije"wai kai kam menene haka kasan Allah yau saikayi girkin nan" Zama yayi ba yanda ya iyya "Me ka iyya girkawa"? Me kikeso na girka miki? "Iyeee lallai ma watoh am bani zabi kenan irin ga k'wareren nan" Eh fad'a mini me zan girka miki? "Waken gembun jiyan nan zaka girka" Ah ah gaskiya banda shi don nidai ban iyya ba, don ni ba d'an gembu bane. "Hhhhh bakar magana koh"? Kema Aishi kika fad'amin "Shikenan yanzun me ka iyya dafawa maganar gaskiya nafa gaji da tsayuwa kwanciya nake son nayi fa" Doya na iyya soyawa da indomie, kwai, harda taliya dafa duka sai Tie "Doya Da k'wai ka iyya soyawa ko daban daban"? Soyayyen doya,kwai ma soyawa na iyya, da dafawa "Ok sai ka soya mana doyan da salt daban saika soya kwai shima daban akwai yaji a roba ka hada mana da ruwan bunu" Sannu hajiya, yace yana kokarin lalubar bojuwa(tukunya) "Waye hajiyan kadaiji dashi"bojuwan sumayya ta wanke ta d'aura akan hot plate tasa masa mai Amma bata kunna ba Albasa ta yanka a ciki, doya ta d'auko da kwai tarugu Albasa lawashi maggi gishiri ta aje masa a kusa dashi koh wanne a roba koh tire koh gwangwa ninsa ruwa ta iba a boket tasa kofi ta aje masa duka don ya huta da tashi koma ransa innan" ga kome a zaune Allah yasa yayi dadi"tace tana fita a kitchen in Baiyi magana ba kawai wuka ya d'auka yafara feran doyan Ruwa sumayya ta iba tayi wanka kaya tasa ta kwanta duk da Al'ameen ya hanata amma baccin tuni ya sace ta Al'ameen na tsaka da feran doya yaji salaman yaro, amsa masa yayi Wai ana sallama da MAKAHO Inji wa? Nima ban sansa ba yace dai in masa sallama dakai Ok kaje kace masa ina zuwa Toh, yace yana fita a kofar Tashi Al'ameen yayi ya wanke hannun sa ya shiga d'akin, sumayya!ya kira sunanta jin shuru bata amsa ba sai numfashin ta dake sauka akai akai, girgiza kai kawai yayi ya d'auki sabon riga da wando da sumayya ta sai masa ya saka ya cire 3quiter dake jikinsa, waje ya fita yana mamakin waye yazo gunsa yau haka Waje ya fita yana tattaba jikin ginin kofar gidan don jin ina mai sallama dashin ya tsaya jin baiji motsen saba ya sakasa, kara maimaita sallamar Wa'alaikumu salam Al'ameen Laiiiiii wana kejin muryarsa kamar Ammar? Baka mantani ba Al'ameen ka rike sunana baka manta ba. Habba Ammar wanda ya maka hallaci irin wanda kamin ai ba mutumin da zaka manta dashi bane Hakane Ya mai jikin? Da sauki sosai Ammar, ya aiki ya gida? Lafiya kasan yau kusan wata biyu da dawowa na ina zuwa unguwan nan ban gane kaba wallahi har Hospital in na koma sukace ai an mata tiyata ma har an sallame ku tuntuni Eh kam satin mu d'aya aka sallame muma tuni. Allah sarki yamai jikin toh? Da sauki fa sosai kamar ma ba'a taba yanka taba, na barka a tsaye muje bakin dakali Ok toh in ba damuwa naga dakalin da rana kazo mu shiga cikin mota mana? Tsakake Al'ameen yayi yana nazari kutt anya zai yarda ya shiga motar mutun da bai sansa ba(lokacin da ya taimake ka ka sansa ne) Am daman ina d'an aikine a gida nama manta na d'aura tukunya Murmushi Ammar yayi watoh har yanzun Al'ameen bai yarda dashi ba kenan, toh ba kome nima bara na wuce naga yamma tayi sai na sake zuwa Toh shikenan nagode da ziyara Ammar Toh aje a cigaba da aiki mijin hajiya hhhhh Hhh Ammar kenan, ya fad'a yana mikama Ammar hannu sukayi musabaha a karo na biyu Bayan tafiyar Ammar cikin gida Al'ameen ya wuce yana tunane tunane sai kuma yaji bai kyauta ba da Ammar nason cutar dashi da randa ya d'auke sa da sumayya ya cuce su, ta wani bangaren kuma sai yaji gwara masa hakan babu ruwansa da mutanen duniya sai mutunci yanzun bai yarda da kowa ba haka zalika tsoron shiga mota ne dashi tunda masu mota suka makantar dashi, kauda tunanin yayi ya cigaba da aikinsa, daya ya gama fere doyan ya zuba a roba wankewa yayi ya tsame a kwando ya zuba gishiri kunna hot plate in yayi ya kama Aiki. Bayan kammala girkin Al'ameen juyewa yayi a kula ruwan shayi koma a flask wanka yayi yashiga d'akin, har lokacin sumayya bacci take, hawa yayi kan gadon a hankali ya kamota d'agata yayi cak yayi waje da ita ajeta yayi a kan dakali Ido sumayya ta ware jinta a sama kafun ma ta gama nazartar inda take taji an ajeta a dakali"menene haka"? Mangariba ake kira baccin ya isa haka, watoh bakiji bakisan baccin mangariba akwai matsala bako "Baccin kwasheni yayi ai" Sai kiyi Alwala nikam na tafi masallaci, bai saurare abinda zatace ba ya fita abinsa Itama samayya Alwala tayi ta shiga d'aki... Bayan sallan isha Al'ameen ne ya shigo kofar su, kitchen ya wuce ya d'auko kulan da ya shige d'aki Sumayya dake kwance fuskarta sanye da glass ta d'aura system inta akan cikinta tana daddan nawa,d'ago kanta dake kan fillo tayi tana bin Al'ameen da kallo ganinsa d'auke da kula sosai tayi mamaki matuka, don ita harma ta manta da zancen zaiyi girki" ikon Allah wai da gaske kake kayi girki"? Idanunki zai nuna miki, yana magana yana fita a d'akin bayan ya aje kulan hannun sa da plate da shukula, sai kuma gashi ya dawo dauke da flask da cups, ajewa yayi a hankali akan cafet ya zuzzuba doyan da kwai sai yaji a gefen plate ya tsiyaye tie a kofuna Itakam sumayya sai ido kalala take kallonsa dashi"wai duk wannan kaika soya"? Eh man bakin raina ni ba an gaya miki in mutum baida ido shikenan sai akace bazai iyya abinda masu ido keyi ba, ai harma yafi namasu ido muna iyyawa "Ah ah kwadai kwatanta Amma badai yafi ba malam" Au karya zan miki kenan? "Bance ba,ina nawa doyan naga ka zuba plate d'aya"? Eh namu ne yau tare zamuci a plate d'aya Sumayya batayi magana ba sauka kawai tayi akan kujeran hannu kawai tasa ta fara cin doyan " kai maggi yayi yawa" Kiji tsorin Allah fa sumayya
Chapter 49 · 0% Book details