Sashe 98
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
~ Na ~ *Rukayya* *Ibrahim* Page9 Duk masu Aljanu sun zuzzube a kasa, muhammad da gudu yayi falon cikin gidan duk da yaga tashin hankali a cameroon Amma wannan tashin hankalin tabanne koh mutum baida Aljanu indai yaga kamila sai tsikar jikinsa ya mike, yana shiga falon yaga an watsar masa da jinjiraye akan kujera, kawayen dada tuni sun ruga daki da sauri ya ciccibi yaransa ya manna a kirjinsa yanemi gefen daining ya tsaya yana jijigasu. Ta gefen sumayya kam bayan d'akunan gidan suka nufa mahmah dake dana da jiki, gudu take kamar kazan Agric irin sunyi naman nan, kowa fa gudu yake abin dariya abin tausayi a take ramadan ya kira yusuf ya sanar dashi, Ammar ma abie ya kira don su harga Allah abin ya basu tsoro especially ganin yanda kadangarun makwanta ke biyowa ta gini da gudu suzo wajen kamila, gasu bataliya guda. Ba'a d'auki lokaci ba saiga Abie ya shigo shikaran kansa abin ya masa tsoro, Amma sai yayi ta maza ganin nafisa, babban get in ya wangale galala gabaki d'aya ana kallon cikin gidan, nuni yama nafisa dasu fita waje su tsaya, ba musu ganin get a bude ta kora mai kadangaru suka fitoh bakin get suka tsaya suna hangen cikin gidan. Daidai lokacin yusuf da mijin nafisa suka iso a tare, don shima wani abokinsa dake unguwan ne ya kirasa akan yaga kamila da nafisa sai gudunsu mutane kiyi. A get yusuf ya sauka suka nufo inda abie ke tsaye, yana ma nafisa masifa akan sun shigo sun dagawa jama'a hankali, ita kuma sai hakuri take basa akan tazo tana son ganin muhammadsumayya da hafsa taji labarin duk suna gidan nan. Daker aka shawo kan abie da wasu mazajen unguwan akan yayi hakuri aji meke tafe dasu, rukiya yusuf yayi ma masu Aljanun suka farfado, matan da suka gugudu ma duk aka tarkatosu, sumayya kam d'ankwali ya fadi koh takalmi babu, muhammad har lokacin yaransa na hannunsa,shimfid'a manyan taburmaye akayi a gefe guda hudu, gefen maza daban na mata daban kowa aka ajesa, wasu da dama kam sun gudu gida wasu kuma na cikin d'akuna, sun rantse bazasu kara yarda su kara kallon kamila ba, haka masu Aljanu duk an hanasu fita. Zama akayi sarki kam kujera aka kawo masa ya zauna, yasa aka shigo da nafisa kamila kam a wajen get akace ta zauna saboda kadangarun ta. Yusuf ne ya kalli nafisa, baiwar Allah lafiya kikazo kika d'agawa mutane hankali da wanshan abin? Kuka nafisa tasa a hankali ta kalli mijinta, sam bataso yau ta sanar da sirrin ta a gabansa ba tsoron kar auren ta ya mutu gashi batasan inda zata shiga ba. Wai ba magana ake miki bane kinsan waye a gabanki kuwa, sarkine da kansa ki kama kanki baya magana biyu? Kayi hakuri nasan yau koh naki koh naso sai gaskiya tayi halinta, shiyasa na gwammaci kunyar duniya data lahira, gwara na nemi yafiyar su koh Alhaki zai barni. Shuru kowa yayi ya zubawa nafisa ido don jin me tazo dashi. Abubuwan da suka faru a shekarun baya da suka wuce, nidai sunanan nafisa Abdullahi kamar yanda wasu suka sani macece maison abin duniya gabin bokaye, bayan nayi aure da mijina saboda halayena ya rabu dani, lokacin na haifi yarinyata kwalli d'aya da Allah ya bamu mai suna kamila, duk yanda naso na koma gidan mijina sam yaki amince wa hakan yasa na shiga islamiyya saboda a lokacin bana zuwa boko sam, mun hadu da safina ne A makarantar islamiyya muka kulla kawance, a lokacin don ance hali sai yazo d'aya ake abota, kawancen mu yayi karfi a lokacin safina ke sanar dani bata da buri saina auren Abdulsalam Amma goggon ta(dada) bata bata goyi baya ba. Ni kuma jin haka yasa na bata shawara muje gun wani malami danaji labarin sa, nima so nake na koma gidan mijina ba musu safina ta samo kudi muka kama hanya har Ardo-kwala wajen wani hanshakin boka. Bayan munje da bukatan mu yake sanar damu Auren safisa da Abdul bazai taba yuwa ba, mundin yana tare da hafsa don soyayyar su na daban ne kuma mai karfi, dole rabasu shine zai iyya taimakawa ta samu Abdul salam. Babu musu mukace mun Amince a rabasu, nima na shaida masa bukatana nason komawa gidan mijina aiko cikin sati d'aya baban kamila ya dawo yace shi kaf duniya saini, na koma gidan mijina aiki yayi kyau sai dai aikin safina shuru baici ba, haka muka koma wajen bokan nan yake sanar damu saimun kawo idanun jariri, kafun mu iyya dishar da soyayyar dake tsakanin su,yaji kwata-kwata baya ganin farin hafsa sai bakinta, sannan bazai iyya rabasu ba sai safina ta had'a da kirsa. Babu musu na samo wasu rikakakun yan daba muka biyasu suka sato mana jinjiri, haka ba tausayi aka kwakule idanunsa a take ya mutu koh shurawa baiyi ba, muka kaiwa boka ido yayi aiki aiko koh sati ba'ayi ba rashin zaman lafiya ya wanzu a tsakanin ma'auratan nan, yayinda na baiwa safina shawara ta shiga sacewa mutanen gidan Abubuwa daga karshe ta likawa hafsa. Aiko shawarata taci don cikin wata d'aya akayi hakan kuma aiki yayi Abdul ya sake hafsa. Bayan nan muka koma wajen boka ya mana wasu aikin gabaki d'aya ya rikitar da dada da yan uwanta akan sai Abdul ya Aure safina kuma duka aikin bokane. Bayan auren kuma safina tazo da bukata akan tanason a raba sumayya da Abdul don ta fahimci yana tsananin son yarsa, shawara na bata akan basai mun koma wajen boka ba ita ta d'auki mataki da kanta, amma abin mamaki har Kashe mata aure dukan sumayya yajawo wannan dalili yasata tayi sanyi ganin babu yanda ta iyya da sumayya. A lokacin da sumayya takai shekara 14 sai gabaki d'aya hankalin safina ya tashi ganin irin kyaun data tashi dashi, gashi koh a gidan su farin jinine da ita gashi kowa na dangi baida magana sai sumayya, kome sumayya hakan yasa safina fara kishi da sumayyar. Kasa hakuri tayi muka koma wajen boka akan a raba tsakanin sumayya da ubanta, dayan gidan su suji sun tsaneta yanda zatayi rayuwa cikin kaskanci, Amma boka yace hakan bazaiyu ba sai an diga magani a idanun yaro matashi mai tashen balaga kuma ya kasance tauraren sa nada karfi, wannan zance da mukaji yamatukar d'agawa safina hankali don ita tana da tsoro ba kamar ni ba. Nikam jin haka sai wani tunani ya fado mini na Al'ameen dake likewa yarinya ta, kwata kwata bana sonsa da yarinyana,gashi nayi iyya kokari na babanta ya rabasu yaki itama duk irin lallama da dabara da zan mata ta rabu dashi Amma taki, hakan yasa na kirawo wa'innan yan daban da suka taba sato mana jinjiri na basu hoton muhammad dake wajen kamila na d'auka, na musu kwatancen makarantan su a ranan suka kama muhammad bayan sun bugar dashi suka daukesa har Ardo-kwala wajen boka, sai da akayi sati baya cikin hayyacinsa, ana masa wankan magani da digawa a ido, kafun aka mayar dashi bayan gari aka jefar. Wannan shine dalilin makantan Al'ameee, ta karasa maganar tana kuka, jama'ar dake wajen salati suka buga, Muhammad kam gabaki d'aya jijiyoyin kansa su mike bacin raine karara a fuskarsa wanda kallo d'aya zaka masa kasan ran maza ya baci, mikewa dada tayi tsaye habba nafisa mai muka miki? yanzun da haden bakin safina aka aikata wannan mummunan aiki, Sai kuma ta fashe da kuka take surutai ya fara tashi kowa yana furta Albarkacin bakinsa. D'aga hannu sarki yayi tare da bada umurni kowa yayi shuru, aiko shurun akayi ya bawa nafisa dake kuka damar ci gaba da bayaninta. Bayan an gama aiki kuma yaci, sai dai sam bai kama Abdul ba iyya yan gidan ne sukaji basa kyaunar sumayya sam, sai kuma Abdul ya d'agata ya maidata hostel wanda hakan ya rage musguna mata da ake, kuma hakan baiwa safina Dadi ba, taso abar sumayya a gida taci kwakwa. Duk yanda mukayi babanta ya rabu da ita abin ya gagara karshe dai haka mukayi hakuri aka cigaba da rayuwa, kamila ma taki muhammad a lokacin ganin ya makance. Lokacin da sumayya ta zama cikekkeyar budurwa hankalin safina ya tashi hassada take da sumayya karta samu mijin dayafi ubanta kudi, koh wani mai mulki kwata kwata so take taga sumayya ta kaskanta a rayuwa wannan dalili yasa muka koma wajen boka daman sumayya nada wani hali na raina wa mutun ArZiki, aiko da halin nan nata aka samo mafita wajen mata magani yanda samari zasuji basa sonta kwata kwata wanda majority zasuce halinta ne ya ja mata. Bayan nan sumayya ta rasa manemi sai dai ba'anan gizo ke saka ba, sumayya na samun kudi sama da safina don tana aiki, ga kaunar da mahaifinta ke mata, shawara na bata muje wajen wani bokan aiko munsamu wannan aiki da wanshan ya kasa wannan yace zai mana amma da sharadi, shine sai an nemi makahon yaron da mukama asiri, mu had'asa aure da sumayya wannan ne zaisa ta fita a zuciyar Abie,yanda mukasa muhammad yana kallon baki, haka su dada ke kallon bakin sumayya, kuma duk adadin sex da zasuyi, haka aiki zai kara karfi tamkar muna bawa shuki ruw, tsanar ta a zukatansu zai karu, amma aiki zai lalace mundin aka rabasu misali d'aya na wani kasa d'ayan na wani kasa aiki zai karye. Ba musu muka abince daman safina ta shanye kowa a gidan, kowa tsoron ta yake sai abie kawai baya shayin ta, wannan dalili yasa ta samu su babuji da dada ta tilastasu akan aurar da sumayya kuma ita ta sama mata miji ba musu suka amince jiki na bari. Mu muka nemi mamman dayaje ya samu muhamamd akan shine uban sumayya, zai basa auren ta amma dayake Al'ameen nada tunani sai yaki Amince wa, karshe dai wajen Bappa suleman akaje don munji labarin yanada son kudi, mamman ya sake masa kudi masu yawa akan zance, wanda gaskiya lamari sharri muka ma suamyya akan tayi ciki saurayin da zata aura ya fasa, a taimaka a had'ata da muhamamd ba musu ya amince da zancen. Bayan auren sumayyya da muhammad magani yaci Abdul ya tsane yarsa, duniya kaf babu wanda yaki jini irinta, muma sosai muka sakawa rayuwar sumayya ido duk wani motsenta muna