← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 104

Sashe 78

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

jin fulatanci duk ta maida martani na bata wuya, amma babu abinda zaka fad'a da fulatanci bata sani ba, dayake gidan sosai suka rike yarensu, suna hausa Amma ba sosai ba. Sumayya(momcy) tana da shekara hudu Abie inta ya shigar da ita makaranta, lokacin hafsa(ummi)ta kammala karatunta na jami'a ta fannin koyarwa, taso kara gaba Amma abie ya hana, aiki yasama mata na koyarwa a makarantar secondary, wannan kenan. Sumayya na cika shekara biyar kanin Dada Allah ya masa rasuwa a gembu, dukansu sukaje taziya, bayan sadakan bakwai dada ta d'auko yarsa daya haifa guda d'aya, mai suna safina(momy), bayan dawowar safina family shugaba, sai abubuwa suka fara bullowa saboda tunda safina ta shigo gidan shikenan ta fara likewa Abdulsalam(abie)duk wani iyayinta abie baya kulata, asalima sai ya daina zaman falo kwata kwata koh abinci ne saidai suci da ummi a d'aki, abin har yakai ga dada ta lura da hakan, sosai ta nuna masa bacin ranta akan yana nunawa safina mugun hali don tana zaune a gidansu. Zama ya fara rashin dadi lokacin da safina ta fitoh karara tace ita abie take so, sam abi yaki zancen kuma ya nuna bazaiyu ba, ummi karan kanta a lokacin ba karamin bakin ciki taji ba, don gwara tayi kishi da kowa akan safina, irin yaran nan ne shegun kauye masu shiga idon mutane, gashi batada kunya sam. Dada fa ta tuntube abie akan zancen ya nuna bazaiyu ba, hakan yasa dada bata tilasta masa ba ta watsar da xancen, abinda ya konawa safina rai kenan, kaf gidan babu mai supporting nata, kowa ya nuna baya goyon baya akan zancen, harda matan babuji basa sonta. Safina makaranta aka saka ta na islamiyya, don sam taki zuwa boko duk yanda akayi bazata ba islamiyyar ma daker ta fara zuwa, zuwan ta islamiyya shiya had'ata da kawa nafisat, nafisa irin yaranan ne watsansu marasa jin magana, haduwar su da safina, yasa nafisa nunawa safina abubuwa da yawa, ta kara kangarar mata da kai, bata tsoron uban kowa. Abin yayi matukar d'agawa dada hankali duk yanda taso rabata da safina abin ya gagara, gashi a lokacin nafisa bazawarace harda y'a d'aya take dashi, hakan yasa dada mawa safina barazanan zata maidata kauye, amma safina koh a jikin ta, ta nunawa dada koh ta maidata kauye tasan hanya, duniya da fad'i. Bayan wata uku da haduwar safina da nafisa, lokacin sumayya nada shekara 6 a duniya, hafsa ta fara ganin change a zaman su, sam yanzun zaman ba dadi tsakanin ta da mijinta, kullum cikin rikici suke wanda itama karan kanta batasan dalili ba, sosai abin ke damunta, wasu lokacin har Abdulsalam na dukanta, Amma bata taba fad'awa iyayen ta ba, koh wani nata saboda tanason mijinta, sai kawarta wance suke karantar wa a makaranta d'aya, don lokacin kanwar ta da aka kawo mata lokacin cikin sumayya tayi aure, batada wani nata kusa. Yau an waye gari da wani masifa a gidan shugaba, amma dada satan sarkan gwal inta, sosai tayita masifa tana zagin yan aikin gidan wance ke mata gyaran d'aki kamma koranta akayi, koh sati ba'a kara ba aka sake ma hajjo(matar babuji) sata, ba'a kama barawon ba, haka aka ringa sace sace kusan wata har rashin yarda ya shiga tsakanin juna, kowa na zargin d'an uwansa, ba yan aiki kad'ai ba. Kamar yau aka sacewa Matar abubakar agogonta na demond, yau kam masifa aka sake akan sai anbi d'aki d'aki anyi bincike, sai an fitar da barawon don kaf gidan tunda safe babu bakon daya shigo koh ya fita, kuma kowa na gida ranan don weekend ne. Bincike aka ringayi har akazo d'akin hafsa, kamar a mafarki aka ga agogo da wasu sarkoki na dada a cikin wardrop na ummi abinda ya kawo cece kuce dacin mutuncin hafsa a gidan. Daman mai hakuri bai iyya fushi ba don ita da iyya gaskiyar ta, bata d'auki kome ba yama za'ace a iyya tsawon zamansu bata taba sata ba? sai yau sannan ita aitafi karfin sata tunda bayar matsiyata bace ita, sosai ta fara maida martani kowa ya gaya mata bakar magan fad'a masa take ita ma, ana cikin haka abie ya dawo daidai lokacin dada ke zagin hafsa, ita kuma ta gaya mata bakar magana, daman tun asali bata son zaman ta da d'anta, shiyasa ta had'a baki aka lika mata sata. Abie babu tambayar ba'asi yaja ummi d'aki ya rufe, duk da sumayya yarinya ce, amma a ranan tasan gidan shugaba sunyi ma mahaifiyar ta ba daidai ba, duka abie yama ummi kamar zai kasheta daker aka kwaceta. Cikin kuka ummi ta kira kawar ta a waya don ta tsorata lokacin, ganin jini nabin kafafunta, bayan zuwan kawarta, asibiti ta kaita ashe karamin cikine da ita wanda likitoti suka tabbatar daya zube, ga rauni kota ina a jikinta, wayar hafsa kawarta ta d'auka ta kira iyayenta, ta fad'a musu duk abinda ke faruwa tun zaman hafsa a gidan, kamar yanda hafsar ta taba fad'a mata. A ranan mutanen borno suka diro Taraba, cikin tsananin bacin rai, direct hospital suka dosa, duk da isan dare sukayi, ganin halinda hafsa take ciki abin yayi matikar musu ciwo sosai, kotu suka maka abie Amma ina abin ya gaggara saboda iko da kudi da abie suka fisu dashi a jalingo, hakan yasa shari'a taki bima hafsa hakkinta, karshe dai mahaifinta yayi rantsuwa hafsa bazata zauna da Abdul ba, saiya sakar masa da yarinyarsa, ba jinkiri agun abie ya saketa, ya basu takarda a hannu, wannan ciwon yasa mahaifin hafsa yace koh bayan ransa baiyarda hafsa ta kuskura ta sake taka gidan shugaba koh da wasa ne babu ita babu sumayya, ta manta ma ta taba haifar y'a, yajama abie kunne mundin ya taka kafa a gidansa koh sumayya , zai nuna masa ikonsu a maiduguri. Wannan shine dalili koh ince musababin rabuwar sumayya da hafsa, su karan kansu yan gidan basuso sakin hafsa ba duk da abubuwan da ta sace musu, Amma bakin Alkalami ya bushe. Bayan tafiyar hafsa sosai sumayya ke kewar mahaifiyarta, kullum haka zatayi ta kuka a kaita wajen ummin ta, duk yanda dada zatayi rarrashe ki take, karshe da abie yagaji bulala yake mata kafun tayi shuru, a haka haka ta fara cire abin a ranta, soyayya sosai ake gwada mata a gidan baga dada ba wanda ita ke kula da ita yanzun, d'akinsu d'aya haka matan gidan na mugun sonta da mazan, wannan karon harda safina amasu nuna mata so, ba kamar daba inta ganta kamar ta cinnnta a wuta, sosai yanzun sumayya ke wa yara lalle na wasa, daman tunda haka ta tashi da abin abien ta na kara mata karfin gwuwa, duk da kananun shekarunta don lokacin tana neman shekara 7. A wannan lokacin ne safina ta sake yad'a manufarta nason auren abie, kamar wanshan karon ma abie yaki amince wa, amma dada ta murza ido tace bata yarda ba aure dole koh yaso koh yaki, haka abie yana ji yana gani aka D'aura masa aure da safina, batare da son ransa ba, sam sam yarinyar batayi masa ba yaji baya kaunar ta. Tirkashi dada batasan wannan aure shine ummul'kaba'isin kome ba.............. Anya gobe akwai update kuwa *MATAR MAKAHO*
Chapter 78 · 0% Book details