← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 104

Sashe 93

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~ Na ~ *Rukayya* *Ibrahim* Page9 A ranan da aka nad'a yusuf a ranan mahaifinsa yake sanar dani, akan na fad'awa yusuf ya d'auko iyalansa, ya masa hakan ne don yaga zai masa biyayya koh zai bijire masa, Amma tunda ya yarda da auren lawiza kuma ya hau karagan mulki ya yafe masa duniya da lahira. A hankali yusuf ya kalli mahaifiyarsa, mahmah meyasa kika hanani? Kayi hakuri yusuf nayi hakan ne don banason kayi nisa dani, nayi tunanin koh inna sanar dakai hakan zaka iyya bijire wa mulki. Ramadan ne ya kalleta Amma wallahi mama baki kyauta ba, duk irin ciwon da yaya yake Amma mahmah baki tausaya ma d'anki ba?kowa yasan dalilin ciwon yaya yusuf Amma ga magani a hannunki mahmah kika kasa basa habba mama mulki yafi lafiya ne? Kuka mahmah ta sake tana nuna Alhininta. Kaga ramadan ya isa haka mahmah uwatace har abada babu wanda yakai uwa son d'anta don haka ni mama bata mini kome ba. Jin abinda yusuf yace sosai jikin wasu yayi sanyi, Al'ameen hannu yasa a wuyansa ya zaro sarkan tare da mikawa mahaifinsa, Abbajo ga sarkanku a sawa wanda ya dace? Kallonsa zulkiflu yayi, akan me zaka cire, wayace maka baka dace da magaji ba? Ah ah uncle kai ya dace kasa koh uncle Ramadan nikam banida sha'awar sarauta so nake nayi karatu mai zurfi na zama soja mai mukami. Kowa dake wajen da kallo yabi muhammad jin abinda ya fad'a, murmushi sarki yayi hade da cewa yan uwansa, bazan tilasta muhammad ba daman na basa sarkane badon na shaida shine magaji ba, na basane don na gane sa aduk shekaru da zai gabato duk da Akwai kamar jini, Amma zan aje shaida don haka Za'a d'aurawa zulkiflu. Da sauri zulkiflu yace Ah ah wallahi yaya nikam banaso gaskiya, amini afuwa adai bawa Ramadan. Ba musu aka d'aura wa Ramadan sarkan magajin masarauta, sannan a mana booking in fly next week zamu shige nageria. Jin Abinda sarki yace yasa zuciyar muhamamd rawa, ganin wani rawan jiki da mahaifinsa keyi zashi nageria duk zatonsa matarsa na raye, Abbajo nace dukan mu zamu wuce ne? Ah ah muhamamd bazamu wuce mu biyar ba, tunda in muka d'auko su dawowa zamuyi nan? Shuru muhammad yayi yana kallon Mahaifinsa, ya sake juyawa ya kalli mama kamar hadin baki suka had'a ido da nabila kauda fuskar sa yayi. Waini muhammad baka bamu labarin abubuwan da suka shafeka ba, da Alakar ka da sarkin shayi da yaran nan?, zulkiflu yace yana nuna su gidado. Da sauri muwaddat tace eh hakane Akki. Kasa magana yayi yana kallon yusuf, gyad'a masa kai yusuf yayi Alamun yayi maganar sa, A hankali ya fara basu labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyar yusuf da wahalar da suka sha da abubuwan da suka faru da ubangari da zainab, da mutuwar Maminsa da kaninsa harda Aurensa da sumayya, sai dai bai fad'a musu dalilin da yasa aka aura masa ita ba, don baidace yace dangin ta sunyi mata kazafi ba, har kawo zuwansa cameroon. Muhammad na bayani mutane wasu na kuka wasu na salati wasu najin haushin zainab da mahmah data hana a d'auko yaran yusuf, kuka itama mahmah ta sake tana cewa su muhammad su yafeta ta cutar dasu. Yusuf kam zaune yake akan karagan mulkinsa sosai fuska tayi zahur, jijiyoyin fuskarsa ya mike alamu dai ran maza ya baci, gashi a fada yake dole ya matse irin na sarakun, abin tsoro koh bacin rai da tausayi baya bayyana a fuskarsu mundin suma gaban jama'arsu. A take aka matso da tafiya zuwa jibi in Allah ya kaimu da rai da lafiya sai NIGERIA!!!!!! Mikewa yusuf yayi ya koma falonsa kafun kowa ya mike ya fita, nabila kam jiki yayi sanyi saibin mahmah take a baya, yayinda muwaddat da muhibbat suka likewa d'an uwansu sai hira suke masa da tambayarsa labarin khadija, sosai yaji wani irin farin ciki ganin yan kannensa, lawiza ma tashi tayi batama kowa magana ba tayi flat nata, da fari tad'au abin da zafi Amma jin irin wahalar da su muhamamd sukasha da mutuwar Aisha sai taji jikinta yayi sanyi. *************** Sumayya ce zaune a kitchen tana girka pepper chicken zallah, don ita yanzun nama kawai takeci sai shayi, yanzun ma khdija taje islamiyya ne shiyasa ta shiga kitchen da rarrafe zata girka abinci. Sai karfe 5:21 khadija ta shigo falon da sallama, sanye take da riga da wando sai hijab babba na islamiyya, hannunta d'auke da jaka. Amsa mata sumayya tayi tana binta da kallo ta rasa meke damun khadija a kwana biyun nan, gabaki d'aya ta shanja bata da nutsuwa sam, kullum ta zauna shuru koh aiki ta sata bata gamawa akan lokaci, shiyasa wasu aikin take lallabawa tayi duk da nauyin cikinta, don yanzun saidai ta ja ta shiga d'aki indai khadija bata nan"khadija zonan"? Ba musu ta kwabe hijab nata tazo ta zauna kusa da sumayya, Aunty gani. "Khadija meke damunki"? Babu Aunty "Wani irin babu kome, ki dubi halinda kike ciki duk kinsa rayuwar ki a garari, sai kinzo kin samu ciwone a koma ana sayan magani koh yaya"? Babu kome fa Aunty "Bankai ki fad'amin damuwarki ba koh"? Sunkuyar da kai khadina tayi bata iyya cewa sumayya kome ba, tana wasa da yatsarta. "kunyi fad'a da kalamu ne kwana uku yau baizo ba" Wallahi Aunty bansan meke faruwa ba yau kwana uku bai kirani ba, inna kirasa wayar sa a kashe. "Ok abinda ke damunki kenan?amma meyasa baki tambaye kannensa ba tunda islamiyyar ku d'aya kuma boko ma d'aya" Wallahi Aunty kunya nake ji, karsuce da wani abu. "Kunya?lallai khadija bakisan inda ke miki ciwo ba, yaro kullum sai yazo wajen ki kwana uku bakisa sa a idanunki ba, bazaki iyya shigiyarsa ba? Sai gobe innaje school saina tambaye falmata(kanwarsa) " ohon miki" Tashi khadija tayi jin amsar da Auntin ta ta bata. Washe gari bayan khadija ta dawo gida take sanar da sumayya ai kalamu ba lafiya yana hospital, kasancewar sumayya tayi nauyi, khadija ce tayi girki mai rai da lafiya, kawarta ta rakata suka je asibiti wajen kalamu, sosai suka samu jikin nasa yad'anyi sauki, kuma taji dadin tarbar da aka mata maman sa nada kirki sosai, haka ma babansa, wanda ke d'auke da zanen kanuri a fuska, amma mamansa bata dashi, haka kannensa sukayita tsokanarta wai budurwan kalamu ne, sosai tayita jin kunya. ************ Kwana biyu da muhammad yayi a gidan sarauta, da ace zasu hadu da wanda yasansa a baya indai ba farin sani ba, bazai ganesa ba, ya samu gata kota ina bana wasa ba yayi kyau ya kara fresh yana cin mai kyau yana shan mai kyau, ya kwanta a maikyau baida buri daya wuce yadawo yaga matarsa abar sonsa, sannan yana iyya bakin kokarinsa wajen ganin mahaifinsa bai saka damuwar rashin Aisha da salim ba, sosai yake kula dashi baya barinsa shi kad'ai mundin yabar fada, toh zasu kasance tare haka yan uwan babansa na sonsa, kannensa ma duk ya shaku dasu, nabila ce kawai bata samu fuska a wajen saba duk da mahmah tasata ta basa hakuri kome ya wuce, kuma ya nuna ya hakura Amma bata ganin fuska koh hira yake tazo wajen sai yayi shuru abinsa koh ya tashi. Su gidado da sarkin shayi duk sun dawo gidan da zama. Waya mai tsada zulkiflu ya saya masa da kayayyakin sawa masu yawa, wanda zaina sawa. Kamar yanda Aka saka rana yaune za'a diro nigeria, maimartaba ne da mahmah sai muhamamd da zulkiflu Adda maisara, dayake su muwaddat na jarabawa an barsu da lawiza a gida, karfe 2 na rana jirginsu ya d'aga zuwa Kasarmu ta gado!!!!! Sun sauka lafiya, suna fita a jirgi dayake sarki yasan da zuwansu yasa suka samu tarba na musamman direct gidan sarki suka nufa, duk da muhammad yaso ya fara zarcewa sintali sai dai ba dama. Bayan sunyi wanka sunci abinci,kasa hakuri yayi ya ce zaije sintali ramadan ya rakasa a mota tare da driver. Tunda suka shigo sintali yake bin koh ina da kallo yana tuna abubuwan da suka shude watan nin baya, har kofar gidan Adara akayi packing in motar,jikinsa har rawa yake yana Allah Allah ya fitoh, saura kad'an ya buge kafarsa saban sauri ya bude motar ya fita, gashi daman yammane ana shirye shiryen kiran mangariba, abin mamaki yana fita babu wanda ma ya zaci shine, harya ratsa mutane sai binsa ake da kallo ganin babbar motar da ya sauka a ciki. Shiga gidan adara yayi kamar yanda ya tsammani hakan ce ta faru, wato jama'ar gidan na tsakar gida, duk juyawa sukayi suna kallonsa harya karaso tsakar gidan, gaidasu yayi da sauri gabaki d'ayansu suka Amsa hade da shiga shock, indai ba gizau ba Al'ameen ne, duk gatan da ya samu bazai hana su kasa gane saba. Da sauri iro ya mike bura uba wanake ganin nan kamar muhammad ina ka shiga? Bai samu daman basu amsa ba, kofar su kawai ya nufa cikin sauri ya bude kofar shashen, da mamaki yakebin kofar ganin duk datti, Alamu dai an dade ba'a share ba da sauri ya karaso kofar, yana bin koh ina da kallo,da sauri ya shiga kitchen insu ga mamakinsa kome a zaune yayi kura, da sauri ya fitoh a kofar, daidai lokacin Ramadan ya shigo gidan, da sauri muhammad ke tambayar yan gidan da har yanzun suke a tsaye sun maidashi madubi,tambayar su yayi ya yaga kofar sumayya a kulle? Inna asabe ce take sanar dashi ai ba'aga sumayya ba, kama kai kawai yayi yana salati, da sauri ya fita a gidan da kafa ya taka har gidan goggo, yayinda su iro ke mara masa baya, duk inda suka wuce saisu cewa mutane ga MAKAHO ya dawo ga makaho, har gidan goggo va tare da wani neman izini ba ya shiga gidan. Goggo dake zaune a gindin bishiya, gabaki d'aya ta rame ta zama abin tausayi zaune take tayi tagumi, jin sallamar muhammad yasa ta mike da sauri, wanake ganin nan kaman muhamamd?Allahu Akbar Allah mungode maka sai kuma ta fashe da kuka tana rungumar Al'ameen. Saida tayi kukanta mai isarta kafun Suka gaisa na yaushe rabo, hade da karama mujammad karin bayani akan batan su sumayya, wanda shagari ya sanar dasu guduwa sukayi bawai sacesu akayi ba, sosai muhammad
Chapter 93 · 0% Book details