← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 104

Sashe 101

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

duk kabi ka rame........ Jin abinda suke cewa yasa sumayya sauri tabar bakin kofar, jin alamun mom zata iyya fitowa da sauri ta bude kofar falo ta fita waje, muhammad dake tsaye a rumfa har yanzun rike da babyn sa, dan yanzun sunyi wayo sosai,ya tambaye ta Lafiya tun d'azun Ammar bai fito ba? "Muje kawai ba kowa a gidan" Da gaske? "Don Allah ka shiga mu tafi gidan mu pls nace maka basa nan" Ba musu muhammamd ya shiga motar yaja suka wuce gidan su sumayya. Yad'an jima a gidan kafun kiran Ammar ya shigo wayarsa, sallama yama su dada ya wuce, bayan fitar Muhamamd ne dada ke sanar da sumayya akan ta kara ma abie magana akan Amina(goggo)ya aureta don ita hankalin matar ya burge ta, Amma duk yanda dada tayi akan ya yarda Ya nemi Amina tunda dai bata tsufa ba, da yarantanta Amma yaki Amince wa. Sumayya karan kanta taji dadin Abin don babu shakka goggo macece ta gari duba da zaman da suke da ita yanzun a gida d'aya sam bata da dumuwa. Sumayya ta samu Abie akan maganar daker saida takai ruwa rana kafun ya Amince da zancen, A ranan dada ta sasa dole sai ya wuce gidan su Al'ameen sun daidaita da goggo tunda yanzun yaran basa gida sai mahmah ne kawai. Muhammad da Ammar su sukaje suka d'auko su khadija a Airport gidan su Abie suka sauka daman sumayya na gidan sosai suka musu tarba ta musamman, Sannan a nan suke xancen Abie ya tafi zance gun goggo, aiko muhamamd yaji dadi don daman tunanin da yake kenan in ya tafi karatu abroad kamar yanda uncle zulkiflu yace masa next month zasu tafi America an sama masa gurbin karatu harda sumayya da yaransu don gida yusuf ya kama musu ashan haya, yanzun ma bikin Abbajo suke jira. Lokacin da abie ya dawo sosai yayi farin cikin isowar d'an nasa hira ne ya kara barkewa a tsakaninsu sai dare su sumayya suka tashi tafiya, kiran kalamu tayi da Khadija a compound ta tambayesu shin soyayya suke kuma su fad'a mata tsakanin su da Allah? Dariya suka sake a tare sannan khadija tace wa sumayya ai tsakaninta da kalamu babu zancen soyayya asali ma Abota ce kawai da shakuwa don kalamu kamma yana da budurwa yar school nasu sunsha gaisawa da khadija a wayar Kalamu. Hakan sosai yama sumayya dadi sallama sukayi da yan uwanta. Sun isa gida muhammad kam kwanciya yayi ya barsu da khadija anan sumayya ke sanar da ita Zancen sonda Ammar ke mata, da kuma bata shawarwari da tuna mata irin Alkharin Ammar a karesu ya cancanci ta sosa koh Albarkacin Halakcin sa, saida ta tabbatar jikin khadija ya mutu murus kafun ta mata sallama ta wuce d'akin mijinta khadija kam tare da mahmah zasu kwanta. Washe gari da safe bayan sun karya Al'ameen ke tambayar ta dalilin sasa su bar gidan su Ammar bayan kuma Ammar yace masa suna nan,sumayya ke sanar da muhammad zancen Ammar da abinda ta jiyo suna tattaunawa sosai muhammad yayi murna ba d'an kadan ba, haka mahmah khadija kam kunyane kamar zai kasheta, especially jin muhamamd ya shirya ya fita wai kar Ammar yazo ya samesa a gidan tunda wajen khadija zaizo. Sumayya da khadija kitchen suka shiga bayan matsawa khadija datayi kafun ta yarda, suna aikin girki yayinda mahmah da goggo ke falo suna rirrike da yaran sumayya. Wayar mahmah ne yayi kara a d'aki mikewa tayi da na'ima a hannunta ta shiga dakin ta d'auko wayar, ganin nabila ne yasata d'auka da sauri. Ta bangaren nabila jin mahmah ta dauka jiki a sanyaye tace hello Kedai nabila anyi yar banza, sallamar ma bazakiyi ba sai wani d'an banzan hello wai gaki baturiya koh? Yi hakuri mahmah Assalamu alaikum Amsawa mahmah tayi tana tambayar nabila lafiya?jin muryarta cike da damuwa Dada kewarku nake yaushe akki (muhammada)zai dawo? Toh watoh shi kike kewa kenan banda ni? Yi hakuri harda kene mahmah Toh make damunki nabila in baki fad'amin ba wa zaki fadawa? Mahmah wallahi nifa son Akki nake don Allah kisa baki a maganar nan ki sanar da abba kice ke kikeso a had'amu ki taimaka mini mahmah......... Ruqeenjalal *MATAR MAKAHO*
Chapter 101 · 0% Book details