Sashe 39
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Aisha ya Tashi matuka don shi Karan kamshi korinda Yama Aisha na haushin yaran Yusuf ne, Amma Yana son yarsa tura su Salim yayi gidan Amina (Goggo) shi Kuma ya wuce gidan Bala agun ya samu wa'inda ke zaune aka fita da Aisha, aka Masa kwatancen asibitin da aka Kai Aisha Bayan zuwansa ne yaji labarin abinda ya haddasa ma Aisha nakudar Dole abakin Matar Bala,shima sosai ransa ya baci duk da Bai gamu da zainab a asibitin ba Amma ransa ya matukar baci gida ya koma ya sanar da yaransa da yaran Yan uwansa akan suje su fara d'aukar mataki akan zainab kafun hukuma ta shiga Ayarin gidan ADARA daga Yan Mata har zaurawa da samari sukaye Ayari guda suka fasa unguwa da kafa suka taka har gidan ubangari. Zainab Kam gabaki d'aya ta rasa nutsuwarta Koh zama takasa waje Daya, tunda ta gudo daga hospital karshe dai Saida mamarta ta tambaye ta Koh meke damunta haka? tunda abinnan ya faru ta fahimci walwalar zainab ya d'auke, zainab Kam kin fad'a Mata gaskiya tayi Suna zaune dukansu a gida dayake yau Friday ne ubangari ya dawo aiki da wure haka Yan makaranta,ji kawai sukaye an bankado get in gidan an shigo ciki kafun ma su gama tantance suwaye ne har kanwar Aisha ta nufi d'akin zainab jawota sukaye har kofar gidan da gudu su ubangari suka Mara musu baya. Rufeta da duka ADARA sukaye, saiga khairat tafitob gida makwantan su, Aiko kamota sukayi suka Had'asu suna jibga duk yanda Yan unguwa da ubangari suke kokarin k'wace zainab da khairat abin ya gagara ganin zasuye kisan kai don zainab ta Suma Amma haka Ayarin gidan Adara Basu daina jibgarta ba Saida ta farfado da duka Police aka Kira lokacin unguwan ya cika makil day'an kallo, abinka da Friday kowa na gida, bayan zuwan police kafun aka samu aka k'wace su zainab anso Kama Yan ADARA Amma Ina abin ya gagara don fad'ane ya kusa zama na police da Yan gidan Adara,ganin jaraba irin na Yan gidan yasa polisawan tambayar musabbabin fad'an don dai sunyi sunyi su bisu station aye kome agun Amma sunki, D'aya daga cikin samarin gidan ne ya nuna zainab,ke don uwarki fada musu meya faru tsakaninki da yusuf mijin Aisha? Hakika zainab tayi mugun tsorata hakan yasa Bata boye kome ba ta fad'a duk abinda ya faru,atake Alumman suka fara Allah wadai da zainab da khairat ubangari Kam yanke jiki yayi ya Fadi hawan jininsa ya tashi, police ma tafiyarsu sukaye Basu d'auki kowa ba. Ta bangaren Aisha Kam ganin tana kokarin rasa Ranta yasa likitoti Mata operation aka cire baby girl bakwaini aka saka a kwalba,Aisha na farfadowa sunan mijinta ta fara Ambata tana sambatu,tunda ta farfado batada magana sai a kaita wajen Yusuf ta nemi gafaransa Amma ba'a barta ta fita a asibitin ba saboda yanayin jikinta Dana baby. Ta bangaren ubangari ma hakan take jinya ya kwanta har kusan sati baisan inda kansa yake ba abubuwa sun taru sun Masa yawa,Yana Jin sauki kad'an ya Tashi da kafarsa ya koma wajen Alkalin da yayi musu Shari'a, An nemi ganin Yusuf don a wankesa a kotu Amma abin tashin hankali shine, Yusuf a Randa aka kaisa prison Bai kwanaba ya fita tare da sa hannun kotsosin kasa Wannan magana ita tafi ko wace magana tashin hankali agun Aisha don anye iyya bincike an had'a hannu da masu kudin da Yusuf yayi mu'amalan kasuwanci dasu don binciko inda Yusuf yake Koh suwa suka fiddasa Duk Wanda aka tuhuma Mai hannun a cire Yusuf magana D'aya yake fad'a baisan Yusuf ba kawai umurni aka basa daga sama Wannan magana tayi mugun dagawa Aisha hankali atake ta sake kwantawa ciwo Wanda an rasa kansa kullum gaba gaba yake duk abinda babanta ke dashi ya kare a jinyar Aisha da Salim don shima zuwa lokacin zuciyarsa ta fara tashi. Tsawon wata biyar ana binciken case in Yusuf Amma shuru ba wani cigaba,yau dai jikin Aisha da sauki,bayan Salim da Yusuf sunzo duba mamar tasu ,don yanzun suna zaune a gidan Adara ne A hankali ta Kama hannun Al'ameen ta rike cikin nata ta fara magana hawaye nabin Gefen idanunta,Al'ameen ga kaninka nan da Yar uwarka khadija Muhammad ka kula dasu ka zama uba a garesu Koda kowa zai gaji dasu Kai ka zaman musu gata, jagora,Garkuwa,inaji a jikina wata Rana zaka Hadu da mahaifinka,kace Masa ni Aisha Ina neman afuwarsa ya yafe mini Koh Zan samu salama,ka zamo Mai hakuri kamar mahaifinka duk abinda zakaye a rayuwa ka ringa bincike karka yanke hukunci a cikin fushi don karshin sa Dana sanine. Al'ameen duk da yarone Amma hankalinsa in yayi dubu toh ya tashe in Bai manta ba haka abbajonsa yayi Masa, shikenan ya gudu ya barsu don shi har yanzun baisan takammamen abinda yake faruwa ba, Mami kema gudu zakiye kamar abbajo ki barmu?yace Yana kuka shida Salim dake kusa dashi Ah ah Yusuf ba gudu zanye na barku ba inda zanje kowa ma zaije in lokacin sa yayi sanan abbajonka Bai gudu ba wata Rana zai dawo kaji,ga kaninka na kuka ka rarrashesa karka barsa ya zubda hawaye kasan ciwonsa bayason damuwa Koh?ta tambaye sa muryanta na shakewa Kai muhammad ya gyad'a Mata hade da Kama hannun Salim Yana rarrashensa, Ji kawai yayi mamin su na wani irin shakuwa hade da Kiran sunan Allah,da sauri ya fita a d'akin yaje Kiran Doctor Suna shigowa dakin da sauri Muhammad ya matso gareta cikin matukar razana ganin maminsu Bata m...................