← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 104

Sashe 94

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yaji wani irin ciwo na abinda dangin sumayya sukayi bayan rabuwar su, taya zasuce ya rabu da matarsa akan wani dalili, anan yake sanar da goggo abubuwan da suka faru sannan yace mata yana son zuwa gidan su sumayya don ganawa da iyayenta, koh Allah yasa sunsan inda sumayya zata iyya zuwa. Ba karamin mamaki Goggo tasha ba jin wai yusuf sarkine yanzun, Allah sarki duniya, mikewa gogho tayi tad'au hijabinta suka fita gidan da Al'ameen, ai suna fita kofar gida, me zasu gani mutane ne makil a kofar gidan, sunzo kallon Al'ameen don lokaci d'aya labari ya samesu makaho ya dawo yayi kudi, goggo ma a take ta kara musu da wani ai yanzun d'an sarki ne babansa yana mulkin wani gari, a nijar, muhamamd in ma kudi ya ciro a Aljuhunsa ya rarraba musu dubu bibbiyu. Yana gama raba musu kowa ya watse yana saka masa Albarka, harya juya zasu shiga mota,don driver yajawo ramadan dake ciki har kofar gidan goggo, yana shiga tun daga nesa ya fara jin ana kwala masa kira oga oga oga!!!! Shagari ne ya iso wajen da gudu, da ido muhammad ke binsa koh ba'a fad'a ba yasan shagari ne daga muryarsa ya gane sa. Oga sannu da dawowa ka dawo lafiya, yanzun Abdu ra'uf kece mini wai ka dawo. Murmushi muhammad yayi, lafiya Alhamdulilah shagari. Da sauri shagari yace munyi kewarka oga shagon mu ya bunkasa nima, yanzun ina makaranta bara na kira Ammar na sanar dashi daman ina da number sa? Ah ah basai ka kiraba ka bani number sa zan kirasa. Kallon ramadan da goggo dake mota shagari yayi sai kuma ahankali yace oga tafiya zakayi ne? Ah ah shagari ina Taraba har sai anga sumayya. Number Ammar ya basa sukayi sallama suka tafi, dayake shugaba family house sanannen gidane kuma driven dan garine, yasa da kwatance suka gane gidan, goggo ramadan da muhamamd suka shiga gidan,ganin zubinsu yasa mai gadin basu hanya suka wuce cikin compound, ya shiga gidan don musu sallama da mai gidan, ba'a jima ba saiga Uncle Abubakar ya fitoh suka gaisawa, sannan suka gabatar masa da kansu, kuma suna son magana da mahaifin sumayya, da rawan jiki Abubakar ya musu iso zuwa cikin gidan, da gaggawa ya hado kan mutanen gidan a falo, kowa na zazzaune don su daman ba farin sani sukayiwa muhammad sosai ba, a d'auren aure suka fara ganinsa hakan yasa basu wani ganesa ba, gashi ba'a makaho yake ba yau. Bayan sun zazzauna wannan zaman ma ba momy a ciki, a nitse goggo ta musu bayanin ga mijin sumayya ga kuma bappansa ta nuna Ramadan, da mamaki suke tambayarta ba'ance mijin sumayya makaho bane kuma ya bata. Ramadan ne ya musu bayanin kome a take jikinsu yayi mugun sanyi, sannan suke sanar dashi rashin ganin sumayya anyi iyya bincike Amma shuru, duk inda ake tsammanin zataje ba'a ganta ba, abie har wani ya samu ya tura unguwan su Hafsa a maiduguri a dubo masa koh sumayya ta gane gidan kakan ninta shan taje, amma an samu tabbacin banan sumayya taje ba, Asali ma hafsa tayi aure bata maiduguri yanzun. Hankalin muhammad ba karamin tashi yayi ba, fiye da hankalin yan gidan duk da abie ya shiga damuwa don har rama yayi mai tsanani, suna tsaka da maida zancen sukaji an turo kofar falon koh sallama babu. Gabaki d'aya suka juyo suna duban falon, safina ce ta shigo Alamu dai daga unguwa take, duk suka bita da kallo itama, d'aga ido tayi ta kalli jama'an falon da karfi ta kwala kara ta zube a kasa sumammeya.. Da sauri dada tayi kanta, sabanin Abie da sauran yan gidan dako a jikinsu alamu dai ba karamin tsanarta sukayi ba, muhammad ma mikewa yayi shida ramadan suka nufi kan momy, da taimakon su aka kaita asibiti don anyita watsa ruwa bata farfado ba, gashi yan gidan koh a jikinsu, sune suka d'auketa har asibiti suka biya kudin kome suka tafi suka barta da dada, gida suka koma bayan isha'i suke sanar dasu yusuf abubuwan da ya faru da batar da sumayya tayi,sosai suka nuna Alhininsu da damuwa sosai muhamamd ya basu tausayi yaro tun yana karami yasan wahalan duniya, har tashinsa ma yayi gwagwarmaya. Washe gari da sassafe saiga Ammar a gidan sarauta, daya samu aka barsa ya shiga ya tura wani dogari yace ana sallama da muhamamd bakin Niger, ba'a jima ba sai ga muhammad ya fitoh, tun daga nesa yake kallon muhamamd kamar bashi ba gabaki d'aya rayuwa ta sauya, sanye yake da jallabiya yar saudi sai hula taba kaji hadisi, sosai yayi kyau saidai fuskar sa a tamke take alamu baya cikin walwalarsa, yana karasowa da sallama a bakinsa, amsa masa Ammar yayi ai yana jim muryar Ammar da sauri ya rungume sa, cikin farin ciki suka hau hira har cikin gida muhammad ya shigar da Ammar suka gaisa da yan uwansa da mahaifinsa, sai a lokacin yake sanar dashi ai shagarine ya kirasa yake sanar sashi muhamamd ya dawo, yana gidan sarki kuma ya basa number Amma shuru Al'ameen bai kirasa ba shiyasa yabuga sammako yazo ya gansa. Abinci aka kawowa Ammar, suna zaune a d'akin da aka sauke muhammad ana hira da labarun abubuwan da suka faru a baya harda Ramadan, kawai saijin muryar jama'a sukayi a sashen sarki, dayake window d'akin da aka sauke muhammad yana saitin sashen. Mikewa sukayi gabaki d'ayansu suka zagaya zuwa falon sarki,family shugaba ne, suka gaishe dasu abie, aka daura zancen batan sumayya kowa na kawo shawaran sa, karshe dai akace za'a dage da rokon Allah da sadaka sannan za'a zuba jami'an tsaro a bincike su, kafun kowa ya watse, daman yan gidan su sumayya gaida yusuf sukazo da mahaifiyar sa tare da bada hakuri akan abinda ya faru kuma ba laifi sun nuna musu bakome, kome ya wuce Allah ya kiyaye na gaba. Satin yan nijar biyu a taraba ba'aga sumayya ba, gashi kaf gidan su an duba hotonan ta duka ba'a gani ba, hatta dakin su muhammad ya koma yayi bincike sap baiga wani hoto ba, don sumayya ta tafi da hotunan su, gashi na wayar maimuna kanwar Ammar ma, wayar ta lalace harma ta saida ta, bare su samu ho tunan su, da yake yanzun zamani ya sauya ba kamar daba, mutun ya bata a gari ma ba'a ganesa sai da rabo bare a kasa sukutum, dole tasa Yusuf komawa dasu ramadan aka bar mahmah da muhammad, kafun su tafi saida aka sai musu gida mai shegen kyau a Amazon suka koma ciki su uku harda goggo, kasancewar mijinta ya rasu bayan tafiyar sumayya hakan yasa muhammad d'aukar ta suka koma gidan su suna zaune tare da mahmah. Wasa wasa saida muhamamd suka share wata biyu a jalingo Ana kan bincike har yanzun shuru ba'aji duriyar sumayya ba, koh khadija sosai abin ya dame muhammad koh abinci baya iyyaci sosai, ba irin tunanin da baiyi ba don shi gani yake saceta akayi tunda makiyansa suka iyya saka a kashesa, Amma ammar na yawan kwantar masa da hankali ba kad'an ba. Ta bangaren safina dai tunda ta farfado a gadon asibiti ta makance bata gani kwata kwata haka magana ma bata iyyawa saboda bakinta daya koma gefe, fuska ya karkace ya murd'u ya wainu wanda likitoti sun tabbatar hawan jinine daya hau lokaci d'aya, daya bugar da ita ta fadin nan, shine ya kaushar mata da fuska, sai dai makantar ne basu gano sila ba, kuma kaf gidan babu wanda ya damu da lamuranta sai dada ita ke jinya amma hatta abie yaji ya tsaneta hakama y'an gidan wanda basu san dalili ba, dada ma daurewa take Amma ba kaunar safinan take ba yanzun. Ammar ne zaune a falon gidan su shida kannen sa, abinci yake ci gabaki d'aya hankalin sa nakan TV, yayinda iyayen sa ke hiran batar sumayya da dawowar Al'ameen wanda Ammar ke kawo musu zancen, don iyayen sama sunje har gidan muhammad, suka masa jaje, kaninsa ne kawai baya falon. Kwala masa kira yaji kaninsa yayi daga d'aki sai gasa ya fitoh da gudu hannunsa d'auke da waya yana zuwa baiyi magana ba, kawai ya mikawa Ammar wayan. Kallon wayan yayi hotunane akayi posted nasu a instagram guda uku, Khadija ce sanye da uniform ita da wani bakin yaro wanda zaiyi sa'ar ta koh ya fita da kad'an shima da uniform in nurse suka d'auki hoto a unguwa mai kyau, sai na biyun tana sanye da uniform in islamilayya nan ma su biyu sai na ukun ita da yaron suna sanye da kayan hausa atamfa da shadda. Jikin Ammar na rawa yake tambayar Abdul wanene yaron nan? Aboki nane kalamu-wahid, school namu d'aya dashi a abuja naga yayi post kuma naga kamar khadija? Ba kama bane Abdul itace, yanzun kasan inda yaron yake takamamme a Abuja? Eh na sani yaya don inban manta ba kafun mu dawo hutu yayi ciwo danaje asibiti dubasa na samu an sallamo sa, so yamin kwatancen gidan su naje. Waya kawai Ammar ya fitar a Aljuhunsa yana lalubar numban muhammad gabaki d'aya yabi ya gigice. ******************* Kalamu yaji sauki har ya dawo da normal life nasa, a haka sukaci gaba da rayuwa abinsu cikin farin ciki duk da basa rasa kalubalen rayuwa. Sumayya ciki ya shiga wata tara duk rashin tausayin mutun inya ganta sayya tausaya mata, cikine yayi kato matuka yayi tsayi ga nauyi don yanzun koh tafiya bata iyyawa sai dai rarrafe abin tausayi bata fita koh ina daga falo sai toilet khadija ke kome wani sa'in kalamu zaizo ya tattara wankin ta ya kai mata dana khadija, wani sa'in har girki yake zuwa ya taya khadija in ayyuka sun mata yawa, sumayya kam yanzun sai a hankali, koh riga bata iyya sawa sai wasu manya manyan vest na gwanjo da zani shine kayanta, sosai laila ke tausaya mata. Yau laila da mijinta harda yaranta sunyi tafiya zuwa Adamawa wajen dangin mijinta, bayan isha'i kalamu yazo ya kawowa sumayya balankun nama, amma ta kasa ci saboda ciwon kanda ke damunta, suka sha hira da khadija suna cin nama, bai koma gida ba sai kusan 9 ya ma khadija sallama ya wuce, don zuwa lokacin sumayya ta dade da kwanciya. Da misalin karfe 1 na dare sumayya ta farka jin wani irin
Chapter 94 · 0% Book details