← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 104

Sashe 82

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

gashi yan gidan Adara ba mutunci bane dasu bare ya Tambaye su. Fita yayi kofar gidan ya tsaya yama rasa me zaiyi don shi gabaki d'aya tunanin sa ya basa khadija tabi sumayya gidansu kenan, kuma me yasa basu ma goggo sallama ba,motar sa yake kokarin shiga saiga mototin su abie, dakata wa yayi yajira sukayi packing yana mamakin ganinsu. Matsawa yayi garesu suka gaisa, Anan nefa yakejin wai sunzo d'aukar sumayya, da mamaki yake sanar dasu ai sumayya bata nan kofar ta a rufe tun 9 yazo mata sallama amma bai ganta ba. Ai abie baisan lokacin da ya zauna a dakalin kofar gidan adara ba, ya dafe kansa shikam ya shiga uku, Anya sumayyar sa daya sani ne mai tsananin sonsa da masa biyayya Amma yau ya zana mata layi ta ketare, sai yanzun yake nadamar auren ta a gidan Adara, don shi duk ya ta'alaka rashin jin sumayya, da auren tan nan da suka mata, tunda har tasan tasa kafa ta gudu, don dada da kanta taje kofar sumayya ta sake lekawa taga a rufe, ga shagari dayazo wucewa ma ya musu bayanin tun asuba sumayya suka bar gari, waya Ammar ya fitar yayi ta kiran sumayya amma bata d'agawa, Abie ma yayita kira Amma ba'a picking karshe dai dukansu suka d'unguma har tasha, Amma koh maikama da su basu gani ba, kowa suka ma kwatance sai yace bai gansu ba. Haka abie suka dawo da sanyi jiki gabaki d'aya hankalin sa a tashe, yar yarinyar sa guda d'aya dayake da ita, tasa kafa ta shiga duniya ita da ba sanin kowa tayi ba ina ta shiga, Ammar karan kansa tafiyar sumayya ya d'aga masa hankali, wani irin abune haka sumayya ta aikata yanzun barin gari da tayi menene Amfanin sa, yau in muhammad ya dawo fa, me zaifad'a masa don Allah, gashi wani Al'amari mai girma dake zuciyar sa yana shirin fiddawa sumayya tasa kafa suka gudu da khadija shidai ya bonu. *********** Washe gari bayan sumayya sun tashi da asuba sunyi sallah wayar ta ta d'auko wanda tasa a silent ta bude ganin miss call na yan gidan su, da sabon number har da messenge yasa ta bude wayar ta zaro sim in dake ciki ta bude Aljuhun akwatinta ta saka sim in a ciki, sannan tama khadija gargadin karta fad'awa kowa gaskiyar abinda ya kawo su Abuja, koda kuwa laila ce ta bari da kanta zata mata bayani. Khadija ce tama laila shara da moping in tiles, sumayya kam bacci ta koma don har yanzun akwai gajiya a jikinta, sai kusan 10:00 suka karya su uku saboda yaran laila biyu ne kuma duk sun tafi makaranta abinsu. Laila ce ta kalli sumayya,sumayya gaskiya nayi mamakin ganin ki a tasha jiya, garin yaya zakizo gari bakisan kowa ba?gari ma irin Abuja sumayya wallahi jiya ban d'auka ke bace don rabon mu dake tunda muka gama school, ban sake saki a ido ba,dayake a lokacin bata mu ake ba manyan yara. Dariya kawai sumayya tayi tana kallon laila, Allah sarki rayuwa da laila ba karamin sonta take da kawance ba, amma kullun sai tayita wulakanta ta , gashi yau itace ta mata rana gaskiya ne da akace A rayuwa koh wani mutum yana da ranan sa"wallahi laila tafiyar gaggawa ce, bamma sa tsamanin Abuja zanyi ba" Bangane ba sumayya?gaki na ganki da ciki don nasan wannan jikin naki da biyu ne. "Hhhh kai laila ba halin nayi jiki kenan"?tayi maganar tana kallon khadija data mike ta koma d'akin da suka sauka, jin hiran nasu na manya ne. Ah ah sumayya wannan jikin yafi karfin jikin jin dadi, kinga yanda kirjinki ya ciko ga hips yafi kome cika kamar me, ga jikin ki ma yayi d'anye. "Ke abar zancen nan ni duk ba wannan ba, a ina xan samu gidan haya kamar nakun nan, na kama"? Ah ah sumayya baki bani Amsa ta ba tukunna?cikine dake koh ba ciki ba? " cikine laila" Ok Aure kikayi ne, kuma meya kawoki Abuja da yarinyar shan? "Aure nayi laila, dalilin zuwa na kuma mijina akayi kidnap insa shiyasa nima na gudo daga Taraba na dawo nan" Baki da gidan iyaye ne? naga dai ke yar masu haline baza'a rasa tsaro a gidan kuba ai? "Kinga laila rabu dani bana sha'awar komawa gidan mu kwata kwata wallahi, kawai in zaki nema mini mafita ki nema min tunda kikace mijinki yau zai dawo kinga bai dace mu zauna miki a gida ba" Kwantar da hankalin ki sumayya, in gidane zaki samu don wannan gidan ma za'a samu waje, Amma sumayya kinsan rayuwar Abuja ba d'aya bane da Taraba koh? gidan nan da nake ciki dubu dari biyar ne a shekara , haka mijina ke biya. "Karki damu indai kudin hayan ne zan biya laila ba damuwa, har school nake son ki taimaka naje na saka khadija" Sumayya kamar nawa kika shigo dashi abuja ne wai? "Million d'aya da dubu d'ari hudu" Hhh lallai sumayya don kunzo da wa'innan kudi kike tunanin zama a Abuja, nifa bawai na yarda dake da abinda kikace bane, na sanki sarai da zurfin ciki, Amma fa ki sani wallahi wa'innan kud'aden da kikazo dasu wallahi bazasu miki kome ba, saidai in kin shigo da result naki nasa mijina ya nema miki aiki koda a office insu ne? "Laila banzo da kome daya shafe karatuna ba, sannan ni ina da sana'a wanda nake saka tsammanin zan iyya neman na kaina da shi, kuma yarinyar nan kanwar mijina ce, marayu ne su biyu Iyayen su suka haifa,mijina bayanan shiyasa narike ta a hannu na, kuma karatun ta nada muhimmanci aguna" Toh wani sana'a kenan kike bayan Lalle sumayya? Ita khadijar bata da dangi ne? "Harda make-up kuma khadija ta iyya kitso inso samune shago nake so na kama sai mu fara muga yanda Allah zaiyi damu" Anya kuwa sumayya gaki da ciki in kika haihu d'awainiyar abinda kika haifa zai dawo kanki, ga khadija ga kudin haya ga kayan da zaki sawa d'akin da zaku kama, ga kudin makarantar ta anya abinnan zai hadu kuwa? "Insha Allah laila Allah zai dafa mana, yanzun dai so nake kimin hanyar da zansamu dakin gidan nan da kikace ya saura, don so nake kafun mijin naki ya dawo mun bar muku kofa, tunda kikace jiya ma kinje d'aukosa a tasha kika samu bai iso ba, motar su ta samu matsala" Ba kome tashi toh muje gidan, mai gidan yana tsallaken titi bara na kira mijina na fad'a masa. Ok sumayya tace suka wuce gidan mai gidan hayan, bayan laila ta nemi izinin mijinta a waya. Bayan sunje a take sumayya ta wuce bank dayake babu halin transfer, tunda ba sim a wayar ta, kudin hayan suka kawo wa mai gidan,bayan sun dawo kudi sumayya ta baiwa khadija da laila suka tafi kasuwa, ita kuma bude d'akin da suka kama tayi, sashen mai kyau two bedroom da falo ga daining area ga toilet a cikin koh wani daki, ga kitchen a ciki daki dai mai kyau dashi yasha tiles kamar d'akin laila, kome a ciki. Bayan su khadija sun dawo katifa suka sayo babba, da zanin gado sai hot plate mai kai biyu, da sandan moping sai bokati biyu, soson wanka dadai d'an abubuwan Amfani daidai talaka, bujuwan su biyu, khadijar ce ta ibi ruwa a panpon gidan ta wanke musu d'akunan tayi moping, yana bushewa suka shimfid'a katifar a falon, suka kai sauran kayan da suka saya kitchen, suka shigar da akwatuna su cikin d'ayan d'akin, suka kwanta a katifar su ita da khadija a falo sosai gidan ya musu d'adi ganin kowa na d'akinsa babu tsegumi kamar gidajen hayan da suka sani. *********** Ta bangaren Al'ameeen, suna zaune a gindin bishiyar ga gajiya ga yunwa, Gidado dake gefene ya fashe da kukan bakin ciki, Al'ameen da yaron fulanin nan sukayi wajen sa da sauri, duk da raunukar dake jikinsu, don gabaki d'aya kafafunsu kayoyi sun bula gashi hannun muhammad sai yanzu yake jin tsamin sa ga giransa dake ciwo, Gidado lafiya kuwa ?sukace har suna had'a baki. Kuka gidado ya sake da karfi, sai kuma ya bude baki Amma ya kasa magana, da hannu kawai ya nuna musu gefen jikin bishiyar da yake. A matukar kidime muhammad yace, innalilahi wa'inna'ilahi raji'un sarin ka yayine gid'ado............ Ruqeenjalal [10/24, 2:18 PM] +234 903 356 9641: *MATAR MAKAHO*
Chapter 82 · 0% Book details