← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 104

Sashe 84

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~ Na ~ *Rukayya* *Ibrahim* Page8 Mikewa Sukayi da sauri suka nufi kofar gidan, ba tare da wani tsoro ba suka zare sakatar, me zasu gani?bawan Allah nan ne aka d'ago rababe-rababe kamar kayan wanki, cikin hanzari suka bawa mutane biyu da suka d'agosa hanya suka shigo dashi cikin gidan, direct d'aki suka nufa dashi suka kwantar. Al'ameen dake binsu a bayane ya tambaye su meya faru dashi? Wani a cikin sune yake tsanar dashi wai ashe faduwa mutumin yayi a gidan da yake aiki, kafarsa ya karye shine aka kaisa asibiti aka d'aure kafar, amma yaki zaman asibiti wai sai dai a dawo dashi gida yayi jinya. Allah ya kiyaye na gaba Su Al'ameen sukace suna komawa d'akin mutumin. Kallon kafar da aka d'aure muhammad yayi, Sannu baba Allah ya kiyaye na gaba? Amsa masa yayi da, Ameen Al'ameen. Sannu baba, gidado da badaru sukace a tare, Amsa musu yayi a hankali, tashi Al'ameen yayi ya fita a d'akin, murhun inda ya gani na karfe d'an karami ga gaushi a ciki, nitsuwa yayi ya hura wutan ya d'aura butan shayi, atakaice dai shayi ya had'a a cikin butan ya had'a da kofi ya kaima mutumin, ba musu mutumin yasha kad'an, Al'ameen ya sake fita ya d'aura ruwan zafi, yana dumi ya d'auko a roba ya had'a da tsumma yazo ya gogewa mutumin jiki, ya shanja masa kaya, sosai mutumin yaji dadi yayita sama Muhammad Albarka. Da dadare ma su gidado sun koma dakin su, yayinda Al'ameen ya kwanta da mutumin a d'akinsa tare, tsakar dare mutumin ya farka da taimakon muhammad yayi fitsari ya sake dawo dashi ya kwantar, a hankali mutumin ya kalli muhammad sai kuma ya bude baki ya fara magana, Allah ya dubi halinda zan shiga ya aiko mini ku muhammad, da ace yau babuku a gidan nan bansan halinda zan tsinci kaina ba, bani da kowa gashi ba Aure nake dashi ba bare yara. Babu kome Baba fatan mudai Allah ya baka lafiya. Ameen muhammad, Akwai wani taimako da nakeso kamin, in babu damuwa d'an nan? Ba kome baba indai har baifi karfina ba, kuma bai sab'awa shariya ba, zan maka kome da kake bukata, kayi mana kome baba tunda ka bamu matsuguni a gidan ka. Muhammad a gidan da nake aiki tsawon shekararu a gidan, tun lokacin da mahaifina ke aikin a matsayin da nake yau, ina binsa muje tare har Allah ya d'auki Ransa, ni na cigaba da aikin kamar shi, a yanzun bani da kowa ba uwa ba uba ba yara ni kad'a nake rayuwa ta a gidan nan, sai yanzun da Allah ya turo mini ku, in ba damuwa so nake muhammad kaje a matsayina, kaci gaba da aikin da nake har Allah yasa na samu Lafiya, kaga bazanso ace aikin da nake tsawon shekaru, yau a samu wani ya karbe mini ba, tunda ciwon bana kwana biyu koh uku na warke bane?sai nayi jinya mai tsawo. Shuru muhammad yayi na d'an wani lokaci kafun yace, ba kome baba zanje nayi aikin har Allah ya baka lafiya, Amma wani irin aikine don ni baba banyi karatu mai zurfi ba? Murmushin karfin hali mutumin yayi, bafa aikin da ya shafi ilimi bane, aikin gidan sarauta ne, kuma nine sarkin shayi na gidan. Muhammad ne ya kalle sa da mamaki, Gidan sarauta kuma baba? Eh d'an nan zakaje ka zauna a matsayina tun jiya na sanar dasu zaka fara zuwa aiki gobe. Aini baba ban iyya dafa shayi irin naku ba, kadai ga yanda na had'a shayin d'azun baiyi irin wanda ka had'a mana ba. Karka damu muhammad akwai wa'inda zan turaka wajen su, 'yan gida nane suna taimaka mini wajen raraba shayi a gidan, Na sarki ne kawai nake kaiwa da kaina, kaima yanzun kaine zakana kai masa,sannan shayi kala uku ake, akwai na sarki shinasa dabanne, akwai na family akwai na bayi. Baba anya zan iyya aikin nan kuwa, gidan sarauta fa kace? Zaka iyya muhammad ka taimaka kaje kaji? Shikenan Allah ya kaimu goben lafiya, Amma baba wazai nuna mini gidan, don ni bako ne , bansan ina ne gidan sarkin garin nan ba? Karka damu muhammad akwai yaron makwantan mu gobe zan turaka gidan su saiya kaika. Shuru muhammad yayi ya kwanta, Amma ya kasa bacci haka kawai yaji yana fargaban zuwa gidan kodon bai taba zuwa bane oho. Washe gari muhammad ne yayi wa mutumin Alwala da ruwan zafi ya saita sa gabas, sukuma suka wuce masallaci. Bayan sun dawo kamar jiya suka kimtsa gidan yau harda karyawa suka had'a mai kyau, bayan muhammad yayi wanka, baba kaya ya sakasa ya d'auka irin na buzaye, wando kato da rigansa mai aiki a gaba sai rawanin su, muhammad kasa nad'a rawanin yayi, Amma haka mutumin nan a bashi da lafiya saida ya nad'awa muhammad, rufe masa fuska yayi da rawanin babu abinda ake gani a fuskar sa sai kwayar idanunsa, sosai Al'ameen yayi mamaki harya kasa hakuri yayi magana, baba basai an rufe fuskar duka ba? Ah ah muhammad ina son koh kaje gidan karka bude fuskar ka, ka barsa a haka, kuma kayi taka tsamtsam da kowa na gidan, karka yarda da kowa kayi abinda ya kaika ka dawo, ga wannan in kaje get sai kanuna, kafun a barka ka wuce ciki. Karba muhammad yayi yana karanta abinda baba ya basa, get pass ne d'auke da rubutun larabci, a jiki saidai bai gane me aka rubuta ba, kasancewa yare aka rubuta da harufan Larabci sai hoton zaki a bayan get pass in, Muhammad fita yayi bayan yama su gidado bayanin inda zashi, sosai suke da Zuzuta karbar da kayan ta masa kamar buzun gaske, bayan ya fita a gidan, gidan makwancin su ya wuce ya masa bayani kamar yanda baban yace masa, had'asa da yaron sa mutumin yayi, ya rakasa gidan da baba ke aiki. Tunda suka sauko a machine yakejin wani irin masifeffen bugun zuciya, ga wani irin fargaba dake cikin ransa ya rasa dalilin da yasa? ya tsinci kansa da tsoron zuwa gidan, tun daga nesa ya hango wani irin gini mai d'aukar hankali gini ne irin dogin nan masu masifar tsaho, ga wani fankamemen get fari mai d'auke da hoton zaki babba a jiki, gidane na Alfarma koh ince unguwa guda tun daga nesa zaka tambatar gidane na sarauta, masuji da mulki,yanda suke matsowa gidan haka bugun zuciyar Al'ameen ke kara yawaita, karasowa sukayi bakin get in, masu tsarone sanye da bakaken kaya hannunsu d'auke da manya manyan bindigogi cikin tsawa d'aya daga cikin su ya dakawa su muhammad da karfi cikin yare yake musu magana. Daskarewa muhammad yayi jin yanda mutumin ya hayayyako musu kamar zaicisu d'anye, gashi sai yare yake shikuma baji yake ba, Allah yasa yaron da suka zo tare yana gun shiya musu bayanin zuwansu cikin yare tare da sanar dasu muhammad d'an uwan Sarkin shayi ne, zaizo ya karbe sa daidai yaji sauki. Basu barsu sun shiga ba har saida Al'ameen ya nuna musu get pass da baba ya basa kafun suka barsu suka shiga ciki, mutuwar tsaye muhammad yayi lokacin da idanunsa suka sauka a compound na gidan, duniyace babba gida mai matukar girma, a haka suke taka tsakar gidan daidai sun iso tsakiyar gidan muhammad yaga gunkin zaki babba mai matukar girman gaske, An kawatashi a tsakar gidan a zaune kamar mai rai, wucewa wani shashe sukayi da yaron sai gasu a wani kayatancen falo mai masifar kyau da d'aukar hankali, kujerune na Alfarma a cikin su, zarce wa sukayi cikin wani kofa dake gefen falon, shidai muhammad idone nasa yake bin koh ina da kallo, har suka shiga cikin d'akin, wow shine abinda ya fitoh a bakin sa ganin wani irin kitcheen na Alfarma mai dauke da kayan Alatu na zamani, sai samari guda biyu dake kitchen in a tsaye suna aiki,jin motsen su muhammad da sallamar suce yasasu juyowa. Amsa sallamar sukayi, bayan sun gaisa da yaron yake musu bayanin Al'ameen ne zai karbi, sarkin shayi harya warke, sannan sarkin shayi yace su koya masa had'a shayi, sannan shi zaina kaiwa sarki shayi kullum, duk da yare yaron ke musu bayani. Muhammad kamfa ya shiga tsaka mai wuya don shi dai ba yare yake jiba, tayaya zai iyya zama da wa'innan mutane wai daman babu hausawa ne a nijar koh dai wannan garine baida hausawan oho?kuma gashi baba ya iyya hausa? Yaron ne yajuya zai fita a kitchen in da sauri muhamamd ya bisa a baya, da mamaki yaron ya juyo ya kalli muhammad cikin mamaki yake tambayar sa yaya kuma zaina binsa? Gaskiya nifa ban gane ba kowa a gidan nan sai yare yake mini, nifa baji nake ba. Dariya yaron yayi karka damu kaji, wasu a cikin su suna ji sai dai in an ganka za'ayi tunanin koh kanajin yarene shiyasa wasu ke maka yare, Amma in suka maka magana kana musu hausa kaji zasu maka suma. Toh nagode kawai muhammad yace, ya koma kitchen in, sosai suka sakasa aiki goge kofuna d'aura shayi saka wanshan ganye ah ah yi kaza sai kusan azahar, bayan sunyi sallah aka fara rabon shayi a gidan, shima wasu kofuna da buta na Alfarma masu shegen kyau da sheki ruwan Gold suka zuba shayin a butan, aka jera a karamin tire da shukali sai bolw na zuma, shima Golden colour da shukali biyu, mikama Al'ameen sukayi Hade da had'asa da wani a cikin ma'aikatan ya nuna masa flat na sarki. Duk abinda Al'ameen kiyi tsananin bugun zuciyar sa nayi, har wa yanzun da suke nufar sashen sarki, hannunsa d'auke da tiren kayan shayin, suna isa kofar shiga falon, ma'aikacin ya koma ya bar muhammad tare da nuna masa kofar da hannu alamu dai nan zai shiga, yafi minutes 2 yana tsaye ya kasa shiga zuciyarsa na matukar buga wa da sauri-sauri, ganin wani bawa zai wuce yasa muhamamd saurin sa hannu ya murd'a kofar falon bakinsa d'auke da sallama, Amma bai shiga ciki ba a bakin kofar ya tsaya. Amsa masa sallamar akayi saiga wata mata ta fitoh, sanye da kayan da bayin gidan ke sanyawa, hade da masa iso zuwa cikin falon, shigowa Al'ameen yayi yana bin bayanta har suka karaso cikin falon, falone babba mai girman gaske da kawatuwa irin falon nan na sarakuna, masu ji
Chapter 84 · 0% Book details