← Book details Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 104

Sashe 10

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba Shikam tsabar damuwa har jiri yakeji yana ibansa ,a rayuwar yanzun in baka dashi kana ji kana gani harka mutu indai baka da kudin jinya ba Mai taimakon ka, zama yayi a bakin barandan pharmacy in yayi shuru cikin tashin hankali da alhini, Bayan fitar Al'ameen khadija na zaune har lokaci hawaye baibar zuba ba sai ta gogi wani ya zuba, har hour 1 yayanta Bai dawo ba, *** A hankali nabude idona na sauke akan Khadija dake ta hawaye ido harya kumbura abinka da farin fata fuska tayi ja" khadija lafiya kuwa meya faru Naga kina kuka"?? Babu Aunty Daman na tsorata ne danaga cikin ki ya Tashi Ashe haka kike fama da Jin jiki sannu, Murmushi nayi "haba Khadija Menene na kuka baki ga naji dauki ba" Toh Aunty, "Yauwa khadija nikam likita ya fadi abinda ke damuna ne, Koh yake sani ciwon cikin nan"? Kafun ta bude baki ma sai ga doctor ya shigo,Wai har yanzun baku samo kudin aikin ba Koh bakuji condition inda nace muku tana ciki ba Wai ina MAKAHON yake ne? "Doctor ban gane mikake nufi ba" nace ina kallon sa? Au baku fada mata bane? Yana kallon khadija alamar tambaya Eh doctor bata sani ba khadija ta bashi Amsa,, "Wai meke faruwa ne kun sani a duhu" waza'a ma aiki?? Kece appendix ya kumbura sosai tun jiya na sanar dasu Amma haryau shuru Basu biya kudiba yanzun haka hour 3 na Basu su kawo kudin Dan kina bukatan aiki gaggawa Amma an share hour 1 shuru, Banga alaman zasu biya ba Da mamaki nake kallon khadija"yanzun khadija Ina fama da wannan babbar matsala irin wannan Amma kuke mini Wasa da rayuwa Ina da kudin da Zan iyya biya ba bandashi ba" Kiye hakuri Aunty Daman Yaya ne yace shi yake son biya " Koh ance lallai sai yayanki ne ya wajaba ya biya ai ni Karan kaina nasan Bai dashi don Bai biya ba ai bazai zama wani abu na daban ba" menene riban ya fita yana neman bashi alhalin Ina da kudi"?? Kiye hakuri Aunty,ta fada jikinta a sanye ganin Raina ya baci "Nawane akace kudin aikin"? ......50k ne "Khadija tashi ki dauki key kije gida ki dauko mini jakana wani yellow a cikin whtdp nawa ki dauko mini jakan akwai kudi a ciki" Toh Aunty ta fada tana mikewa daukan key in tayi a jakan kayana ki hadamin da wayata ki dauko darduma babba da filo, ga kayan da nacire ma kikai mini gida kisa a basket in bayan kofa" "Kihau nepep ya kaiki kofar gida ki shiga in kin dauko kudin saiki shiga ya dawo dake ki basa 1k ya d'auki kudinsa karfa kice Zaki tafi da kafa"?? Toh Aunty ta d'auki kayan nawa ta fita a dakin, doctor Kam Dan kallo ya zama Daman tun da ya ganni yake ganin alamun Jin Dadi a tare Dani Amma abinda ya daure masa Kai mutanen da suka kawo ni asibitin abin yana bashi,mamaki harda Nurses Amma basuga fuskar tambaya ba **komawa nayi na kwanta shima doctor fita yayi Tsabar rudewa Khadija Koh yayanta Bata Lura dashi ba akan baranda ta wuce, Shikam ganin lokaci na wucewa yasa ya Tashi ya shigo dakin,da sallama a bakin sa, **Amsa Masa nayi Ina kallon sa yazo ya zauna a kujiran gefena, Sumayya,yakira sunana "Na'am" na amsa Masa Kiye hakuri Sumayya na kasa kula dake wallahih nayi iyya kokari na Amma ban samu kudin ba Daman appendix ne ke damunki Kuma ya kumbura, shine ake son Miki aiki kuma........ **Da nayi niyar rufesa da matsifa Amma sai jikina yayi sanyi Jin bayanin da yake mini" ban bare ya karasa ba na katse sa"ba kome, me amfanin Ina dashi kaje kana,.. baran attaimaka maka kazo ka biya mini kudin aiki"? Karka sake mini irin wannan banaso duk abin da zai taso a waje na Koh Khadija Koh Kai, in baka dashi karka sake zuwa gun wani da sunan ya taimaka maka indai abin baifi karfina ba pls" Kiye hakuri insha Allah bazan sake ba, **Shuru na Masa Jin Bata amsa ba ya sashi yin shuru Khadija na Isa gida ta samu jama'a na cike a kofar gidan dam alamu dai wani abinne ya furu don harda motar police ga jama'an unguwan makil............... *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara* *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* *Na tsunguno(habil)* *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* ) *Turaren turara jiki after birth* , *Na d'aki(halud Al'oud)* *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* Contact them vie 08028827241 or 09033791049 IG @umsadincense my WhatsApp number 08084453785 08084453785 08084453785 0808445378508084453785 *MATAR MAKAHO* ~ Na ~ *Rukayya Ibrahim* Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa Free book Page 1 Cikin tashin hankali Khadija ta nufi kofar gidan tana isa taga an fitoh da inno Akan kadon asibiti da ake daukan gawa Koh Mara lfy tana kwance Koh motse batayi aka shigar da ita Ambulance sai su Inna asabe da baba lami suke ta rusan kuka Kamar ana yankasu, Khadija Kam iyya rudewa ta rude ganin Yan matan gidan duka kuka suke harda wasu mazan ma Bappa Dayyabu da bappa sulaiman harda kawu tafawa suka shiga motar Yan sanda da gani dai abin Case ne babba Ta rasa wama zata tambaya ga Goggo Amina sai kuka take , Ganin lokaci na tafiya tasan yanzun bazata samu amsar tambayar taba yasa ta wuce kofar yayan ta shanyar kayan dazun da safe takai d'akin jakar ta dauka da Abubuwan da ta lissafa Mata duka,ta rufe kofar tayi kofar gida Da sauri ta fita daga gidan ganin har yanzun jama'a na tare Tam, Hospital ta wuce direct tana isa dakin ta baiwa Sumayya jakar, Budewa nayi na zaro kudi 50k na mikawa yayan khadija "ga kudin ka dau takardan khadija ta rakaka kuje ku biya" ...Toh Al'ameen yace Yana laluben kudin ya karba hade da zaro dubu goma da dari biyar in safiya da Khadija ta basa ya hada da dari biyar in mangoron sa,ki cire dubu goma da dari biyar a cikin kudin sai na hada Dana wajena na ciki ta na biya, "Ka bar na wajen Kan ai ba'a sallame niba zasu bukace mu Sai wasu abubuwan irin su hand gloves Koh ruwa da allurai duka ai bamu Gama kashe kudi ba ba iyya aikin bane kawai ka rike kudin a gunka," Toh khadija Tashi mu tafi Toh yaya, ta basa amsa **Fita sukayi nikam zuciyata tsinkewa ya ringayi da fargaba gani nake kamar bazan rayu ba, Waya ta da khadija ta kawo mini na dauka number abie na Kira Amma Bai dauka ba, Sake Kira nayi harna fidda tsammani naji ya dauka cikin sanyin jiki na Masa sallama"assalamu alaikum abie" Waalaikumu salam ke lafiya? Lafiya Alhamdulillah abie Daman na kiraka ne nace maka za'a mini operation yau don Allah Abie in nayi maka ba daidai ba kayi hakuri abie ka yafe mini bansan Inna shiga operation room xan fita da Rai Koh a mace ah ah shiyasa na kiraka naji muryarka abie ka samin albarka Koh xanga nasara a rayuwa ta Dan Allah" Keeeeeee!!!! ce Miki akayi in za'a ma mutum tiyata mutuwa yake ne kin wani kirani kina fadamin Zaki mutu ki mutum Mana keee!!!! bara ma na fada Miki daga yau karki sake kirana!!!! wallahih, tunda na aurar dake ki barni na huta mana, ***Hawaye ne keben fuskata Wai meke faruwa da rayuwa nane haka,, Yanzun mahaifina in ma ya juyamin baya, ganin shigowar Al'ameen da Khadija yasani share hawayen, "Khadija kin biya"? Eh Aunty.... Sunce 7:00 na dare za'a shiga operation room in, "Toh bara nayi sallah mangariba Koh kafun Azo a dauke ni" na fada zuciya takaraya sosai wallahih, Shima masallaci ya tafi nida Khadija mukayi Sallah muna idarwa na sakasu suci abincin da ya rage tun safe Basu sake saka kome a cikin su tun karyawan safe na taliya da wake,, Daker suka iyyaci Amma kadan nikam na kasaci tsabar fargaba, Karfe bakwai akazo za'a dauke ni, *** Da kafata na fitoh nurse suka sakani a gaba har nayi nisa Al'ameen ya k'wala mini Kira tsayawa nayi ya iso inda nake lalubar hannuna yayi ya rike cikin damuwa sosai nasan daurewa yake, Sumayya insha Allah Zaki fitoh cikin nasara kinji ki cire tsoro a ranki kinji Allah ne ya jarabceki Kuma insha Allah shizai baki lfy kinji, "Kukane ya k'wace mini yau wa'innan bayin Allah sune gatana a yau bani da kowa a kusa Dani sai su dame Zan biya su babu, Allah ne kawai xai biyasu" rungumar sa nayi cikin kuka nake cemai "insha Allah insha Allah" Lokaci fa na wuce wa ki shige mu tafi Naji muryan Nurse ***Sakensa nayi na rungumi khadija wance tun tuni kuka take, ***Na juya Ina tafiya a hankali Kamar wance k'wai ya fashewa a ciki sudai suna bin mu a baya har Muka Isa kofar operation room aka dakatar dasu tare da nuna musu su koma Kan kujirun d'ayan block in su zauna...... Bayan da Al'ameen baiyi ba Khadija ta koma gida taje ta kwanta Amma Taki tace anan zata kwana sai da ya nuna Mata Jan ido kafun ta yarda zata tafi 500 ya Bata ta hau nepep sauran change ta rike a hannun ta ,,, . godiya ta Mar sosai ,ta dauki kula ta fita,..... Zama Al'ameen yayi agun har akayi Kiran isha'i yaje yayi sallah yanata Addu'a Allah ya yasa aiyi aiki a sa'a ya Bata lfy(muma mukace Ameen) Bayan wasu hours Sumayya aka fitar akan gado tare da kayan tiyata da hulan duka Koh motse batayi aka kaita dakin da ake aje,wa'inda akama tiyata Basu farfado ba shima binsu yayi har dakin ya shiga sun dauke ta sun daura akan gadon dakin, kujira ya samu a Gefen gadon ya zauna ganin an shanja musu daki ba dakin emergency
Chapter 10 · 0% Book details