Sashe 47
Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kawai ba'a basu ba, a kasuwar ta baiwa tailor ya d'inka musu kala ukune jibi khadija zatazo ta karba Turare ta saima khadija da mayuka masu kyau sai Dutsen guga karami na wuta. Cefene tayi mai yawa sosai ta sai harda su drinks, doya, dankalin hausa, harda na turawa, vegetables, kai abubuwa sosai sumayya ta saiya saida kudin hannunta ya kare na machine kawai ya rage musu da d'an abinda baza'a rasa ba Bayan sun dawo gida da sallama, suka shiga gabaki d'aya dan dazon yan gidan suka bisu da ido ga kaya niki niki kamar masu kaura suka wuce suka shiga kofar ga yara na rirrike da laidodi Wa'alaikumus sallam, sannun ku da hanya Al'ameen yace yana cire hannunsa daga cikin kwanukan da yake wankewa "Yauwa yayan khadija" sumayya tace tana bin kofar da kallo ganin kayansu daya wanke ga randa a cike da ruwa Alamu dai jido yayi Yaran na sauke kayan sumayya 10 10 ta basu da murna suka karba kowa na jin dadi suka fita Sallah khadija da sumayya sukayi kafun suka baje cefenen suna dubawa, khadija kam ganin yanda sumayya ta loda mata kayan sayayyanta a gabanta kuka kawai ta sake tana rungumar sumayya,yanzun aunty duka wannan nawane? yaya kaga kayan kuwa wai duka nawa , tana fad'a tana kamo hannun yayanta ta d'aura akan damin kayayyakin abin ma abin dariya da tausayi Shima karan kansa Al'ameen yayi mamakin kayan, sumayya abubuwan nan basuyi yawa ba kinje kin kashe kudi da yawa haka sumayya kina ga ba aiki nake fita ba bazaki tattala kudinki ba sai kina fashaka haka. "Allah zai kawo kuma maganar baka aiki bazai hana nayi walwala ba kaima insha Allah kafun d'aya ga azumi zaka daina zaman gidan nan" Allah yasa Amma dai sumayya kayan yayi yawa Babu wani yawa yar fa makaranta ce sai da guga da wanki da gyara, kema khadija duk safiya kina zuwa kafun ki tafi makaranta kizo ki karya,ki karbi kudin tara dana keke kinsan sunce sai 2 ake tashi kuma ana dukan letti Toh Aunty amma zanna karyawa a gida saina zo na karbi na kudin. "Shikenan monday zaki fara zuwa jibi, kije ki karbi uniform in ki gobe ki goge, gata sai school" Hhh hakane Aunty in tafi da kayan naje na nunawa goggo kona barshi Anan? "Ai yanzun kayanki ne ki tafi dashi" Toh aunty tace tana rungumar kayanta ta fita Khadija na tsananin farin ciki yau wanda rabon dana gansa har na manta, Al'ameen ya fad'a yana lalubar hannun sumayya ya kama "Insha Allah zaka yita ganin sa yanzun harka gaji" Allah yasa, kema Allah ya biyaki "Ameen, na sai maka waken Amma na gaji gaskiya bazan iyya dafawa yanzun ba kasan sa da wahalar nuna" Shikenan sumayya Allah ya kaimu goben "Ameen", tace tana d'aukar wayanta dake neman agaji"Assalamu Alaikum" Shuru tad'anyi sai kuma yaji tace "toh bara na tura miki ta WhatsApp" "Ok shikenan", tace tana aje wayan "Kasan waya kira"? Ah ah ... "Yar kanwar deputy ne waina tura account number" Toh Allah ya bada sa'a Ameen, bara na tura musu Tashi Al'ameen kam yayi yaje ya cigaba da wanke wanken sa sumayya kam Account numbar ta tura musu koh minutes 10 ba'ayi ba taji Alert kudine ya shigo account in khadija dayake da layinta aka bude account in..... Khadija kam na fita a gidan yayanta da kaya niki niki sai sauri take kamar zata fad'i damuwarta kawai taga ta isa gida ta nunawa goggo abin Alkhari data samu, bata hankalta ba tazo tsallaka titi koh ganin gabanta batayi, ji kawai tayi jama'a na illalilahi keeee kalli gabanki Ai jiii kawai kake kiiiiiiiiiiiii kauuuuuuuuu............. *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara* *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* *Na tsunguno(habil)* *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* ) *Turaren turara jiki after birth* , *Na d'aki(halud Al'oud)* *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* Contact them vie 08028827241 or 09033791049 IG @umsadincense *MATAR MAKAHO*