Sashe 9
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dan kaf duniyar nan Abubakar ɗin ne kaɗai abokinsa, ba shi da wani aboki da ya wuce shi, sai Sharon da suke ɗan jitiwa, ita ma kuma ba kullum ba.
*Badawa layout, Kano....*
RAJA POV.
“Raja dan Allah, dan Allah!.....”
Cewar wani mutumi a galaɓaice, yayin da yake durƙeshe a gaban Rajan.
Kuma bai ko gama rufe bakinsa ba, Rajan ya ƙara tsinduma kansa cikin bahon dake aje a gabansa, wanda yake cike taf da ruwa.
Haka mutumin ya yi ta motsi da kansa a cikin ruwan, saboda azabar da yake ji.
Zaune yuke a harabar gidansa.
Yayin da Rhoda da su Zuzu ke tsaye a bayansa.
Waɗanan lumssassun idanun nasa na kallon mutumin da kansa ke fancal-fancal cikin ruwan sanyin. wannan innocent face ɗin nasa fayau!, banu wani abu da za ka iya tsinta a cikinta.
Kai ba ka ce mamallakinta ne ke wannan aikin ba.
Ƙarar ringing tone ne ya karaɗe wurin.
A hankali Rhoda ta duba screen ɗin wayar 'Oga Garuje', shine abun da ta ga an rubuta, dan haka da sauri ta ƙarasa kusa da Raja.
“Garuje ne ya ke kira”
Bai kalleta ba, sai ma bindigarsa ƙirar pistol da ya ɗora a kan fuskar mutumin da ya tsamo kansa daga cikin ruwan.
Sannan wannan kamillar muryar tasa ta furta.
“Me yasa ka ci amanar mu?”
A nitse muryar tasa ta fito, cikin wannan sautin nata mai nuna tsantsar innocent ɗinsa.
“Dan Allah Raja....Dan Allah...”
Ji kake Tas!!.
Ƙarar bindiga ya karaɗe harabar gidan.
Me gadin gidan ya yi saurin faɗawa ɗakinsa.
Duk da yasan cewa abun ba zai komo kansa ba.
Amma wai me hausawa suka ce ne?, idan ka ga gemun ɗan uwanka ya kama da wuta, to ka shafawa naka ruwa.
Raja ya yi wani murmushi me kama da dariya, a sanda ya ga shigewar me gadin nasa.
Kafin ya saki gawar mutumin nan da ya harba a ka.
Jini har ya ɓata masa hannu.
Ba tare da nuna damuwa ko wani tashin hankali ba, ya sunkuya ya wanke hannunsa cikin ruwan bahon nan.
Kuma har zuwa lokacin wayar tasa na riging a karo na barkatai.
“Ina ji”
Nutsatsiyar muryarsa ta faɗi,bayan ya amsa wayar, cikin wannan kamala da kamewar tasa, kai ba ka ce shi ne ya kashe rai yanzu ba.
“Raja!, Oga ne da kansa ya yi waya, ya ce ya na buƙatar ka je ka same shi a Abuja....”
Raja zai iya rantsewa kan zuciyarsa sai da ta buga sau biyu a lokaci guda.
Kenan tsawon shekarun da ya kwashe yana wannan aikin sun kusa ƙarewa?.
Shekaru sama da uku ma rayuwarsa ya kwashe yana bautar da bai san ranar ƙarewarta ba.
Sai a yau ne komai ya ke gaɓa.
Komai ya ɗauko hanyar ƙarewa.
Ya kawo inda ya ke matuƙar burin kaiwa.
Sai dai a yanayin fuskarsa ba za ka tsinci hakan ba, dan miƙewa tsaye kawai ya yi, sannan ya juya yana kallon su Rhoda.
Da waɗanan lumsassun idanuwan nasa, ƙwayar idon wadda ta kasan ce gray color tana kallon yanda su Zuzu ke magana ƙasa-ƙasa.
Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ce.
“Yaushe kenan ?”
“Ko zuwa nan da sati ɗaya ne, dan da alama ka koma can da zama, ka ga kenan sai an nema muku gidan da zaku zauna, da dai sauran su...”
“Na fahimta!”
Kuma da ga haka ya tsinke wayar.
“Alandi, Zuzu, ku fita da gawar nan da ga gidan....”
“An gama Oga Raja!”
Suka faɗi suna yin wurin da gawar ke yashe.
Sannan shi kuma ya yi hanyar shiga cikin gidan, da hannu ya yiwa Rhoda alamu da ta biyo shi.
“Rhoda, mun kai ga gaci....”
Wannan salihar muryar ta faɗi a sanda suke zaune a falon gidan.
”Me ya faru?”
Rhoda ta tambaya.
“Alhaji Bala ne da kansa ya ce na je na same shi a Abuja”
Cike da mamaki, murna da kuma farin ciki take kallonsa.
“Kenan mun kusa zuwa ƙarshe?”

“Kusan zan iya cewa hakan”
“Kai amma fa na yi farin ciki...”
Ta faɗi da iyakar gaskiyarta, dan ta yi farin cikin, tana ganin kamar komai ya kusa ƙarewa, kamar an gama komai, kamar wannan wahalar da suka sha tsawon shekaru ta ƙare.
Kuma ba ita kaɗai ke wannan tunanin ba, shi ma kansa Rajan haka yake tunanin sun kammalla komai, komai ya zo gangara, gangarar da zata gangaro da ƙarshen wahalar da suka sha tsawon shekaru.....
Sai dai abinda bai sani ba shi ne; yanzu ne ma komai ya fara, a yanzu LABARIN zai soma, sai a yanzu ne babin ƙaddarar tasa zai buɗe.
Wani sabon babi fil!, wanda babu ɗigo ko ɗaya a ciki, sai na wanda ubangiji zai hukunta.
Saboda wata ƙaddara da ke shirin faruwa 'yan kwanaki masu zuwa.
Ƙaddarar da zata tarwatsa komai, ta kuma gyara wasu lamuran.
A dai-dai lokacin ƙofar falon ta buɗe, Jagwado ne ya shigo, dan da ma banda shi aka tafi yasar da gawar.
Lighter ce riƙe a hannunsa yana ƙyasta ta, yayin da sigari ke maƙale a bakin.
A sa'ar da Raja ya ɗora idonsa a kan wutar, a lokacin ne kuma wannan tsoron ya shige shi, tsoron wuta da Allah ya saka masa tun bayan abinda ya faru da shi.
Baya san ganin wuta sam, domin wuta na ɗaya daga cikin abin da ta zama silar rabuwarsa da mutane uku da suka fi soyiwa a ransa.
Da farko ta raba shi da mahaifiyarsa, sai kuma ta zo ta raba shi da ƙaninsa, ɗan uwansa abokin tagwaitakarsa.
Sai ku ma Maman Rhoda, wata mace da ta taka rawa mai makuƙar muhimanci a cikin rayuwarsa.
Wani irin wahallallen nunfashi ya ja, ya samu kansa cikin irin yanayin da ya saba shiga a duk sanda zai ga wutar.
Duk da yanda yake ta kokawa da tunaninsa kan kada ya koma baya, amma sai hakan ya ci tura.
LABARINSA na baya ya soma kunno kai cikin nazarinsa.
_“Zaid, ku tafi, kada ku tsaya a nan.....idan kuka tsaya wutar za ya iya ƙona ku....ku tafi na ce!.....” _
Amon wannan sautin nata ya shiga maimaita kansa a cikin tunaninsa, falon ya shiga rikiɗewa yana komawa gidansu, gidan da suka rayu a ciki, gidan da suka ci gaba da kwana a cikinsa har bayan sanda wuta ta gama ɗaita shi, wannan gidan da suka gina yarintarsu shi da ƙaninsa a ciki.
Sannan hoton ya sauya a idonsa, ya na ganin yanda take watso musu kayansu ta window, yayin da ƙofar falon take a kulle, ta kasa fitowa bare ta buɗe ƙofar har ta samu damar tsira.
Sannan ya kallin kansa da ma ƙaninsa Aliyu dake ta kuka, ƙaninsa me tsantsar kama da shi, dan idan suka kalli juna sai ka ce kansu suke kallo a madubi.
Dan kammanin da suke ya ɓaci, tsayinsu ɗaya, farar fatarsu ɗaya, girman idonsu ɗaya, komai na hallitarsu ɗaya ne, in ka ɗauke ƙwayar idon Zaid da ta kasance ash, sai kuma totsiyar karen dake haƙorin Zaid ɗin.
Amma hatta wata ɗabi'a ta ɗaga kafaɗa dukaninsu suna yi.
“Jagwado menene haka ?, Sarai ka sani cewar Raja ba ya san ganin wuta!”
Muryar Rhoda da ke wa Jagwado faɗa ta dawo da shi zahiri.
Bai ƙara ce musu komai ba, ya miƙe tsaye, tare da ɗaga kafaɗarsa ta dama, ya yi ɗakinsa, yana jin yanda Rhodan ta balbale Jagwado da faɗa, shi kuma sai aikin bata haƙuri yake.
_________________
_To fa....
Bana kuma nan muka leƙo?_
_Na ce ba, wai Rajan ne ko Zaid ne?_
_Dan ni na kasa ganewa, kamar Zaid da Aliyu mutum ɗayane, kamar kuma....._
_Ko da yake, ba sai na faɗa ba ai😂_
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#Taurariwriters
°°°°°°°°°°°°°°
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*04*
~~~
_-*What she really craves is a wild love, from a steady pertner...*-_
***
*1987*
Alhaji Ali Wakili, babban mutum ne me tarin arziƙi.
Haifaffen garin haɗejia ne, kuma ya ci gaba da zama a cikin garin har bayan lokacin da ya fara tara iyali.
Kasancewarsa mutum me nasibi a harkokin kasuwancinsa, ya sa shi gyara gidansu na gado, ya ci gaba da zama a ciki shi da 'yan uwansa.
Alhj Ali na da mata biyu, hajiya A'i, yaransu tara da ita mata biyar maza huɗu, matan sun haɗa da Lawisa, Fatsima, Kaltume, sai 'yan biyun gidan, Maryam da Rabi'a, Mazan kuma sun haɗa da, Abdullahi, wanda ya kasance shi ne na farko, sai Mansur, Haladu da lawan
Hajiya Kande ita ce matarsa ta biyu, yaranta huɗu da shi, kuma dukansu maza ne, Kabir, Sagir, Jamilu da kuma Jibrin.
Duka yaran gidan suna karatu, matansu da mazansu, kuma duk da kasan cewar sun taso a gidan yawa, akwai zaman lafiya a tsakanin yaran ahalin, dan iyayensu jajirtattu ne a kan tarbiyar yaran nasu.
Rana ɗaya da gaba ɗaya ahalain gidan ba zasu manta da ita ba ta kasance Asabat, inda labari ya riske su cewar an yi wa Rabi'a 'yar biyun Maryam fyaɗe.
Duk wani nau'i na tashin hankali babu wanda bai yi ba a gidan, dan da aka tambayeta ta shin san wanda ya mata fyaɗen?. cewa ta yi bata sani ba, dan hankalinta a gushe yake.
Haka aka gama jajjaɓin lamarin kafin aka watsar da zancen, kowa ya ci gaba da lamuransa.
Bayan kwanaki da faruwar lamarin, Alhj Ali ya nemawa Maryam gurbin karatu a garin Suleja, dan haka ta tafi can ta ci gaba da karatunta.
Watanta ɗaya da tafiya, alamun samuwar ciki suka fara bayyana tattare da Rabi'a.
Tun tana ɓoye abun har ya zo ya bayyana, har kowa na gidan ya sani.
Alhaji Ali ya yi tsallen albarka ya ce sai dai a zubar da cikin.
Itama kuma Rabi'a ta yi tsallen albarka kan cewar ba za ta zubar da cikin jikinta ba, hakan yasa shi kuma yace sai de ta bar masa gidansa.
“In dai har ba za ki zubar da cikin jikin ba sai dai ki bar min gidana Wallahi!...”
Haka ya faɗi, a ranar da yake watso mata kayanta ƙofar katafaren gidan nasu.
Gaba ɗaya mutanen gudan sun firfito, an tsaya a bakin gate ana kallon abin da ke faruwa.