Sashe 23
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saurin dafe ƙirjinta ta yi tana karanto duk addu'ar da ta zo giftawa ta tunaninta.
Ta ƙarasa saka takalmin, sannan ta kama hanyar fita.
“Ke Rabi!
Zo nan!”
Kamar daga sama muryar Habiba ta katseta, hakan yasa ta tsaya da tafiyar, gabanta ya ci gaba da bugu.
Tsoro ya mamaye mata ruhi.
Da ƙyar ta iya juyowa ta kalleta.
Suka haɗa ido, ba shiri gabanta ya ƙara tsnanta bugu.
Haka kawai ta ji ba ta yarda da wannan kiran da ta mata ba, ta haɗiye wani kakkauran miyau, sannan ta soma takowa zuwa gareta.
Kusa da ƙofar ɗakin ta tsugunna.
“Ungo shanye!”
Habiba ta faɗa tana miƙo mata wani abu a kofi, kallon abun dake cikin kofin kaɗai ya haddasawa Rabi faɗuwar gaba fiye da ta da.
Ta juya kallonta kan Habiban, ta ga yanda ta tsareta da ido.
Hannunta na rawa ta kai ta karɓi kofin, sai da ta raintse idonta, ta yi bismillah, sannan ta kafa kai ta shanye abun cikin kofin.
Taste ɗin bakinta ya mata wani iri, dan abun sam ta kasa gane na miye, sai dai tana da tabbacin koma miye sharri ne.
Kofin ta aje mata a gabanta, ta miƙe, ta kama hanyar fita.
Habiba ta bi bayanta da kallo tana murmushi, tasan kamar yanda yayarta ta faɗa mata ne, komai ya zo karshe tun da ta sha wannan abun, saura kuma jiran ganin sakamako.
“Honeynah, Ya kika yi shiru?”
Muryar Yaya ta faɗa, yayin da yake kallon Rabi'a, wadda ke zaune a kan wani benci dake bakin shagon, shi kuma yana daga cikin shagonsa, wayar Anti Saratu riƙe a hannunsa, yana tura mata abubuwan da Rabi'an ta lissafa masa.
Rabi'a ta sunkuyar da kanta ta na murmushi.
“Ni kam ina san wannan kunyar taki, tarbiyyarki da kyawunki su ne ke ƙara min shauƙin ƙaunarki Rabi'ata...”
Rabi ta ƙara sinne kai tana wani murmushi me kama da dariya.
Shi ma Yayan murmushin ya mata, yana juyar da kansa ga turin da yake mata.
Kafin daga bisani ya shiga ba ta labarin yanda wasan jiya ya kasance, dan yasan yanda take matuƙar san ball, kuma shi ma yana tayata.
Sai da suka ɗan taɓa hira, sannan ta masa godiya ta fito daga shagon.
Wata mota ta ga ta yi parking a bakin titi, kasancewar shagon Yayan a bakin titi yake.
Fuskar Mama ta gani a gaban motar zaune a gefen drivern.
Kanta ta girgiza kawai ta yi gaba, ta zo wucewa ta kusa da wasu matasa dake kan benci suna hira, hirar ta su ta ɗauki hankalinta.
“Wannan 'yar gidan tsohon najaduncan ce ko?”
Na kusa da shi yace.
“Ko ba Mama ba ?, Ita ce, kai kuwa barewa ba ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ?...
Ai kamar Kumbo kamar kayanta ?”
“Allah ya kyauta mana kawai...”
Sauri ta ƙara, gudun kada ta ji abun da zai sa ta fashe da kuka nan take.
Daga can cikin motar Mama ta shagwaɓe fuska tana kallon sabon Alhajin da ta yi.
“Gaskiya Baby ni sati zamu yi”
Alhajin ya yi dariya irin tasu ta goggagun 'yan bariki.
“Baby Mamancy!
Ai sai yanda ki ka ce, idan kin ce mu yi wata ma babu wata matsala”
Daɗi har ran Mama, ta je ta yi wata a England ita da wannan Alhajin?, ai har ta hango irin kuɗin da za ta yi.
“Shikenan, zuwa yaushe za mu tafi?”
Alhajin ya shafo ƙaton tumbinsa, sannan yace.
“Nan da next week, kawai dai ki zama cikin shiri, sannan ki aikomin da hotonki na passport”
“To sai na jika”
Ta faɗi tana masa wani farrr da ido, sannan ta kama ƙofar motar ta buɗe.
Idan ka hangeta daga nesa, cewa za ka yi sam ba ta haɗa jini da hausawa ba.
Wata matsataiyar duguwar riga ce a jikinta, sai wani ɗan fingil-gilin mayafi da ta riƙoshi a hannunta.
Small knotless barid ɗin dake kanta, wadda aka kitsa mata ita da wani golden attachment ta sauƙo tana lilo a gadon bayanta.
Fatar jikinta har wani pink-pink take, don tsabar man bleaching ɗin da take shafawa.
Ga wani nose ring da ta saƙala a gefen hancinta.
Duk wanda zai mata kallo ɗaya, a tashin farko zai kirata da karuwa!.
Ko sallama babu, haka ta sa kai a cikin gidansu.
Habiba da har lokacin na zaune a ƙofar ɗaki ta miƙe tsaye tana washe baki.
Ganin Maman ma na fara'a.
“Umma, mu shiga daga ciki”
“To...To!”
Habiba ta faɗi cike da zumuɗi, ɗakin nata suka shiga, ta tsaya tana kallon Mama, tana jiran abun da za ta faɗa.
“Wannan sabon Ahajin da na yi ne, tafiya ta kama shi zuwa ingila, kuma yace da ni zai tafi”
“Ayyirri!...Yirriri!”
Habiba ta rangaɗa guɗa tana kama danannen hancinta hancinta.
“Ni na san ban yi haihuwar banza ba, ni da kaina na san cewa na yi farar haihuwa...
Ingila fa Mama?, Ƙasar turawa ?”
“Nan fa”
Mama ta tabbatar mata murmushi kwance kan fuskarta data sha mai.
Saratu da Rabi dake ɗaki suna iya jiyowa komai, zuwa lokacin Fatima ba ta ɗakin, dan Anti Saratu gama mata faɗan ta tashi ta fice ta bar gidan gaba ɗaya.
Anti Saratu ta girgiza kai cike da takaicin mahaifiyarta da ƙanwarta.
Rabi da ta fara kallon wasan a waya ta kalleta.
“Ba ƙunci ya kamata ki yi ba...
Ki musu addu'a kawai”
Anti Saratu ta yi murmushi.
“A kullum ina yi Rabi, amma gani nake kamar abun nasu ba na ƙare ba ne”
“Kada ki ce haka Anti Saratu, Allah ma jiroƙon bayinsa ne, ki dage da addu'a, Allah zai amsa miki ”
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*09*
~~~
*Someday, you will get everything you deserve, and it will be beautiful*
***
*Shekara ta 2000*
*Kano...*
“Aliyu!, Aliyu!
Wai kana ina ne ?!”
Zaid ke ƙwalawa Aliyu kira, bayan da ya dawo gidansu bai tarar da shi a inda ya barshi ba, sanye yake da wannan uniform ɗin islamiyyar da ya rage musu.
Babu datti a jikin kayan, kasancewar ya na ɗaukowa ruwa a tuƙa ya musu wanki, sai haske da yadin kayan ya fara, alamun ya na jin jiki.
Hannunsa na dama riƙe da ledar ƙosan da ya samu ya siyo, bayan ya je ya yi bara a bakin titi, Bara?!, a yanzu ita ce abin da yake dan ya samu ya kawowa ƙaninsa abin da zai ci.
Sati ɗaya kawai Maman Naufal ta yi tana basu abincin da ba ya ƙosar da su, daga nan idan ya shiga gidan sai ta ɗaure fuska, har ta kai da ta ce masa kada ya ƙara shigowa gidanta.
Ga shi su kuma babu gidan da suka sani a unguwar, da ma gidan nata ne kawai suke ɗan shiga, ganin yunwa za ta lahanta masa ƙani ne yas sa ya fara barar, sai ya tafi bakin titi ya tsaya yana roƙar jama'a.
Da haka yake ɗan samun abun da zai kawowa Aliyun ya ci.
To yau da safe ma ba su tashi da komai ba, hakan ta sa da wur-wuri ya fice ya tafi barar, sai da ya shafe sama da awa uku.
Sannan ya samu na siyan wannan ƙosan...
Tunaninsa ne ya katse, a sabda ya ɗora idonsa a kan Aliyu dake durƙushe a bayan gidansu.
Hankali tashe ya yi cilli da ledar ƙosan ya yi kansa yana kiran sunansa.
“Aliyu!
Aliyu!
Kai Aliyu me ya ke faruwa da kai haka ?”
Ya tambaya a sanda ya ɗago shi, ya na kallon fuskarsa da tai jawur, kasancewarsa me farin fata, ga idanuwansa sun yi ja, kuma a 'yan kwanakin Zaid ɗin ya gano cewa dukansu sun rame.
Sannan ya san ba komai ba ne face yunwa, musamman ma Aliyu da sam ba ya iya jurewa yunwa.
“Yunwa kake ji ?”
Zaid ɗin ya tambaya yana miƙar da shi, da ƙyar Aliyu ya iya gyaɗa masa kai, a hankali Zaid ɗin ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya miƙar da Aliyun gaba ɗaya.
Kama shi ya yi har suka shiga cikin ɗakin da suka saba kwana, ya zaunar da shi a bakin katifarsu, sannan ya koma bayan gidan ya ɗauko ledar ƙosan da Allah ya temakesu bai zube ba, ya haɗo da wani plate da suka saba cin abinci a ciki, sannan ya ɗebo masa ruwa.
Ya dawo ya zauna kusa da shi, ya juye masa ƙosan a plate, tare da tura masa shi gabansa.
“Ka ci Aliyu”
Aliyu ya kalli ƙosan, sannan ya kalli yayansa, ƙwarin gwiwarsa, farin cikinsa, uwa, ubansa duka a halin yanzu Zaid ne.
Sai ya kai hannu ya ɗauko ƙosan guda ɗaya, me makon ya kai bakinsa, sai ya kai setin bakin Zaid.
Zaid ya kalli ƙosan, sannan ya kalli Aliyu, wata ƙwalla me ɗumi ta sauƙo masa, a hankali ya buɗe bakinsa, Aliyun ya ƙarasa saka masa ƙosan, yana taunawa hawayen na ƙara kwaranyo masa.
Ya kai hannunsa ya ɗauko ƙosan shi ma, sannan ya kaiwa Aliyun baki, Aliyu ya karɓa ya na murmushi, da haka suka cinye sannan suka sha ruwa.
Sai kuma suka zauna suna biya tilawar islamiyyarsu, dan bayan faruwar iftila'in nan sun ɗan je.
A lokacin biyan kuɗin wata ne malaman suka korosu, makaranatar safe kuwa l ba su kusanceta ba, dan sunsan babu me barinsu su shiga basu da uniform, kuma ga shi term ya kawo ƙarashe.
Karatun ƙur'anin dai shi suke ɗan taɓawa da ka.
Bayan sun yi sallahr azahar, Zaid yace zai fita ya nemo musu abin da za su ci na rana.
“Zaid ka tafi da ni...
Ba na san zama ni ɗaya”
Cewar Aliyu ya na miƙewa, Zaid ya ɗaga ƙafaɗarsa ɗaya, sannan yace.
“To muje”
Aliyu ya ɗaga ƙafaɗarsa ɗaya yana kama hannun Zaid.
Har suka fito daga cikin gidan, Zaid ya ɗauki wani ƙyallen tsumma ya ɗaure ƙofar gidan, kana suka kama hanyar bakin titi.
Idan daga nesa ka gansu za ka ce mutum ɗaya ne, kasancewar komai nasu kala ɗaya ne, farin fatar, kyan fuskar, hatta da takunsu iri ɗaya suke, na Zaid ne kawai yafi nutsuwa.
Idan wannan ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sai ka ga wannan ma ya ɗaga, abun nasu gwanin ban sha'awa.
A sanda suka fita titin, Zaid ya nunawa Aliyu wuri yace masa ya zauna, shi kuma zai je ya na barar.