Sashe 35
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Na faɗa miki cewar I can't recall when last na buga ball, amma na san na iya, kuma a yanzu ma zan iya buga ball”
“To me yasa kike jin tsoro?, na san tsoron su Precious kike, kisa a ranki cewar su ba su isa komai ba, kuna na san cewa kina ganin saboda ke ba 'yar makaranta ba ce shi ya sa ba za ki iya bugawa da su ba, ki barni da wannan, nasan yanda zan yi da su”
Rabi'a ta ci gaba da kallonta, kafin ta rungume ƙanwar tata da take jinta kamar ƙanwarta ta jini.
“Na gode sosai ƙanwata”
“Don't mention it Seesee”
Daga haka suka yi sallama, Rabi'a ta fita daga makarantar, kasancewar har zuwa lokacin Kuliya be zo ɗaukan Mishal ba, ya sa ta samu bencin me gadin makarnatar taeu ta zauna kusa da shi, za ta iya cewa for the very first ita ce yau ke jiran a zo a ɗauketa, kullum kafin ta fito Malam Ali ya riga ya zo, shi ma Kuliyan ya mata hakan na kwana ukun da suka wuce, amma yau sai ga shi ya makara.
Kamar yanda aka saba Rabi'a na fita ta haɗu da shi, to yau ba ma shi kaɗai ba ne, ya na tare da Rhoda, wadda zuwa yanzu suka ɗinke ita da Rabi'a, don sosai suke hira idan sun haɗu.
“Menene wannan Ammata?”
Raja ya tambaya a sanda suka jera su ukun suna tafiya, Rabi ta kalli ledar hannunta da yake magana a kai.
“Jersyna ce a ciki”
“Kin iya ball ne?”
Rhoda ta tambaya ido waje, Rabi ta gyaɗa mata kai.
“Wow?, da ma a arewa akwai matan da suka iya ball?”
Raja ya ranƙwashi kanta, ta yi sauri ta dafe tana sosa wurin.
“Me kika mayar da matan arewan ne?, ko da yake ai ke ma a arewan aka haifeki, don haka ba ki isa kin ce wani abu a kansu ba”
“To ai ban ce komai ba...
Kawai dai ina mamakin abun ne”
“Wannan kuma ke kika jiyo”
Rabi ta yi dariya kamar yanda ta saba musu idan suna faɗa irin haka.
“Wani club kike?”
Raja ya tambaya.
“Bacerlona”
“Aaa!, ki ce ke tamu ce, mu 'yan PSG ne (Paris Saint Germain)” Cewar Rhoda.
Daga haka kuma sai hirar tasu ta koma ta ball, har suka iso bakin titi hirar ba ta ƙare ba, sosai Raja ya yi mamaki jin yanda Rabi'an tasan abubuwa da dama game da ball, kuma ya yi mamakin jin yanda tace musu ta na son buga ball, dama ce kawai ba ta samu ba.
Su suka tsaida mata mota ta shiga, sannan suka juyo,suna tafe suna 'yar hira.
Kamar daga sama suka ji wata murya na faɗin.
“Hello!”
Hakan yasa suka kalli inda sautin muryar ya fito.
Wata yarinya ce tsaye a gabansu, sanye cikin uniform ɗin makarantar Brickhall, a ƙiyasin shekaru ba za ta wuce 17 ba.
“Hy”
Rhoda ta amsa mata, yayin da idanuwan Raja ke kallonta ƙasa-ƙasa.
“Ko zan iya sanin sunanka Bro?”
Mamaki ya kama Raja, to me za ta yi da sunansa?, tukunna ma waye ce ita?.
“No, kada ka damu fa, ni ba 'yar yankan kai ba ce...”
Maganar tata ta bawa Raja dariya, hakan yasa suka murmusa a tareshi da Rhoda, ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama.
“Sunana Raja, ke kuma fa?”
“I'm Mishal”
Mishal ta faɗi tana gyara zaman jakarta dake goye a bayanta.
“Me yasa kike son sanin sunana?”
Sai kuma ta yi shiru, da ma gajiya ta yi da jiran zuwan Kuliya, hakan yasa kawai ta fito ta fara tafiya da ƙafarta, kuma a kan hanyar ta ci karo da wannan me kama da Kuliyan, shi ne ta tsaya don ta samu ta masa magana, wata ƙila za ta tabbatarwa da kanta abun da take san sani.
“Akwai wani yaya na da yake min kama da kai that's all”
Ta zaɓi da ta masa wannan ƙaryar, don a ganinta wata ƙila ita za ta fi bada ma'ana, saboda babu yanda za'a yi ta faɗa musu cewar da mijinta yake kama, don ba ma lalle su yardar da cewar ita ɗin matar aure ba ce, to taya ma za'ayi su yarda?.
Ba ƙaramin duka maganarta ta yi wa Raja ba, wai meke shirin faruwa da shi ne?, farko Rabi'a, yanzu kuma wannan yarinyar na faɗa masa cewar akwai wani ɗan uwanta me kama da shi, sai dai kuma shi yasan basu da wasu 'yan uwa na kusa.
Da ace ma Rabi'a ce za ta faɗi hakan sai ya yarda, amma shi yasan cewa su ba su haɗa jini da shuwa arab ba, saboda daga gani wannan yarinyar jinin shuwa arab ce, haka zalika kuma yasan cewa duk wanda ya mutu babya dawowa, Allah ya riga ya amshi rayuwar Aliyunsa, hakan tasa ya dangana, ita ma Rabi'an abun da ya sa yake bibiyarta ba komai ha ne face son sanin wani abu game da danginsa.
“Ya alaƙarku take da yayan naki ?”
Rhoda ta tambayi Mishal, dan babu labarin Raja da ba ta sani ba.
“Uwa ɗaya uba ɗaya”
Ta amsa tana kallon fuskar Raja, yanda ya yi da fuskar tasa kaɗai yasa ta tabbatar da abin da take zargi, tabbas babu makawa, duk yanda aka yi wannan ɗan uwan Kuliya ne, amma me ya shiga tsakinsu har suka rabu haka?, tana buƙatar sani.
“Ni zan wuce, Bro and Sis sai an jima”
Da kallo suka bi bayanta har ta fara tafiya.
“Yarinyar nan akwai shirirta”
Rhoda ta faɗi tana 'yar dariya.
Raja da ya gama tabbatarwa da wannan yarinyar ba a kan Aliyunsa take magan ba ya mata murmushi kawai, yana ɗaga kafaɗarsa ta dama, kafin ya ci gaba da tafiya, hakan yasa ita ma bin bayansa.
Mishal na tafe tana saƙe-saƙe a ranta, tana son sanin abin da ke tsakanin waɗanan mutanen biyu masu kama ɗaya, sai de kuma suna da mabanbantan halaye, tsayuwar da ta yi da wannan Rajan ba ta fi ta minti biyar ba, amma ta gane banbancinsa da Kuliya, wannan yana da fara'a, yayin da Kuliya ba shi da ita, wannan yana da sakin fuska, fuskar Kuliya kam kullum a ɗaure take, sannan muryar wannan akwai sanyi da taushi, yayin da ta Kuliya ke cike da hargagi da faɗa, ko maganar arziƙi yake da mutum sai ya maka tsawa, bare kuma a ce ransa ya ɓaci.
Sai kawai ta yi murmushi tana jinjinawa kanta, na sanin halayen Kuliyan a kwana huɗu kawai da suka yi tare, duk da ba wani zama suke sosai ba, haɗuwarsu ba ta wuce uku a rana, da safe kafin ta tafi makaranta, sai kuma idan ya zo ɗaukanta, sai da daddare idan ya dawo.
Kuma kwana biyu ma ba sa haɗuwa da daddarren dan sai ta yi bacci yake dawowa.
KULIYA POV.
Cikin matsanancin gudu yake tuƙa motarsa, tunawa da ya yi ya bar 'yar mutane ta na jiransa, aikin da yake ne ya sha masa kai, har ya sa ya manta da lokacin tashinta daga makaranta, kuma tun a sanda ya fito daga headquarter ya riga ya yanke hukuncin cewa dole sai dai ya nema mata driver, don ayyukan dake gabansa sun fi ƙarfinsa, idan yau ya tuna a kan kari, gobe ba llalle ya sake tunawa ba.
Amma idan ya sama mata drivern, aikin zai masa sauƙi, kuma ko ba komai shi ma zai huta, saboda a kullum sai ya dakatar da aikinsa yake iya samun zarafin zuwa ɗaukanta.
Wata yarinya ya hanga a gefen titi, kamar ita kamar ba ita ba, gashin kanta da kuma farar fatarta da ya gani ne ya tabbatar da cewar ita ce, ya kamata ace ya mata magana kan fita babu ɗankwalin nan ma, don a matsayinta na matar aure hakan be dace da ita ba.
Parking ya yi a kusa da ita, yanda ta tsaya tana kallon motar tasa ya sa ya gane cewa ita ma ta san cewar shi ne a cikin motar, to amma me take jira da taƙi zagayowa ta shigo?, ko jira take sai ya mata magana?.
Kusan shuɗewar muntina goma suna a haka, ita tana tsaye, ta kafe motar da ido, shi kuma ya kasa mata magana ta shigo, ganin kamar tana shirin ɓata masa lokaci ne yasa ya zuge glass ɗin setinta ƙasa.
Sannan ya kalleta.
Sai da ya ɗaga ƙafaɗarsa kafin yace.
“Za ki iya shigowa idan kin gama tsayuwar!”
Mishal ta yi murmushi tana zagayowa, aka ce da ba ya ji, sarai ta gane shi, amma jira take ta ƙure masa miskilancin da yake ji da shi, duk da Anti Adawiyyanta ta ce kada ta na masa irin haka, amma ta lura da idan ba haka ta masa ba, ba zai dena mata wannan abun ba.
*No.181, Guzape, Abuja....*
*08:30pm*
MISHAL POV.
Zaune take a ɗakinta, assignment ɗin da aka basu take ta ƙoƙarin yi.
Ƙofar ɗakin da aka turo yasa ta ɗa ga kanta ta kalleshi, don tasan daga ita sai shi ne kawai a gidan, kuma ta yi mamakin dawowarsa da wuri.
Kamar yanda ta saba ganinsa, sanye yake cikin baƙaƙen kaya.
Wai shi ba shi da wasu kaya sai baƙaƙe ne?, kullum sai ya yi ta saka baƙin kaya kamar me shirin zuwa jana'iza #AbuAswad Sai kawai ta yi dariya a sanda zuciyarta ta raya mata sunan, ABU ASWAD! sunan ya karɓe shi kuwa.
A hankali Kuliya ya saki hannun ƙofar yana kallonta, sanye take cikin wata blue and white boxed tie crop top da farar three layers ruffle skir.
Duk da a zaune take, yana iya ganin alamar skirt ɗin ba ta sauƙa har kan idon sawunta ba, kamar dai sauran kayan da ta saba sakawa, don duk kayan da yake ganinta da su ba sa kaiwa ƙasa.
Gashin kanta naɗe cikin french twist, daga saman gashin ta saƙala farin hair band.
Kai kace wata Disney princess ce, kallonsa take kamar yanda shi ma yake kallonta, daurewa ya yi yace.
“Ki shirya ki fito za mu je wani wuri”
Zai iya cewa ya ga wacewar wani abu me kama da farin ciki a cikin idanunta, kafin ta miƙe da sauri, ƙafarta da bakinta har rawa suke wurin faɗin.
“Fita zamu yi?”
Ya kalleta na wasu 'yan sakkani.
Jin ya mata shiru yasa ta kuma faɗin.