Sashe 36
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ai a shirye nake, mu je kawai”
Ta faɗi tana ƙoƙarin raɓa shi ta wuce, a karo na farko ya riƙo tsintiyar hannunta, ya na dawowa da ita baya, ba shi kaɗai ba, hatta da ita sai da ta ji kamar hysterianta na neman ta shi, sai kuma ya saki hannun nata da sauri yana kawar da kansa.
Ita kuma sai ta kalli hannunta, yati6n da take kokawa da numfashinta da ya ƙi dai-daituwa, da ƙyar ta iya ɗagowa da kansa ya na ɗaga kafaɗarsa.
“Be kamata ki fita a haka ba, saboda yanzu ke matar aure ce!” Ya faɗi ba tare da ya kalli fuskarta ba.
Mishal ta sunkuyar da kanta ƙasa, yayin da abun da ya faru da ita waccan ranar ya shiga yawo a kanta, ba ta son tuna me ya furu a waccan ranar, amma daga zarar wani abu makamancin wanda ya faru a waccan ranar ya sake faruwa da ita sai ta tuna, yanda Yazid ya finciki hannunta da ƙarfi a waccan ranar haka shi ma ya yi a yanzu, tuna sunansa kaɗai yasa numfashinta fara ciccikowa.
Da sauri ta kai hannunta kan wuyanta tana riƙewa, yayin da iskar ɗakin ta mata kaɗan wurin shaƙa, babu shiri ta shiga jan numfashi da sauri, hakan ya ankarar da Kuliya halin da take ciki.
Kallonta ya yi da sauri, a lokacin da ta kai ƙasa, tana kokawa da numfashin nata, idanuwanta sun kaɗa sun yi ja, yayin da hawaye ya shiga fita ta gefen idonta.Ji take kamar za'a zare mata numfashinta gaba ɗaya.
A ruɗe Kuliya ya zube a gabanta yana kiran sunanta.
“Hafsat!, Ke Hafsat!, Hafsat!”
Inaa, ko ganinsa ma ba ta iya yi, bare har ta saurari abun da yake faɗi, ba shiri ya kai hannun ya riƙe fuskarta, yana goge mata gumin da ya shiga tsatsafo mata, har zuwa lokacin ba ta iya numfashi, can kuma sai komai ya tsaya cak, shure-shuren da take, da kokawar da take da numfashinta, da ma hawayen da take duka suka ɗauke, jikinta ya saki, kamar wadda ta mutu.
Ba shiri Kuliya ya miƙe daga kanta, hankalinsa a mugun tashe, shi tun da yake be taɓa ganin abu makamancin haka ba, bai ma san me yasa meta ba, to ko aljanu gareta?...
Tunaninsa ya katse a sanda idonsa ya sauƙa kan wata robar ruwa dake ɗakin, ba shiri ya miƙe da sauri ya nufi robar, ya ɗako ya dawo kanta ya na buɗe robar, tuninsa ne ya bashi cewar wata ƙila suma ta yi.
Don haka ya shiga yayyafa mata ruwan a kan fuskarta da ta yi jajir, amma shiru, haka ya miƙe ya nufi work table ɗin da ɗazu ta taso daga kansa, ya ɗauko littafi ɗaya sannan ya dawo kusa da ita, fiffita ya shiga mata yana kiran sunanta.
Kamar wadda aka tsikara da allura, lokaci guda numfashinta ya dawo, ba shiri ta miƙe zaune tana wani irin tari, har lokacin Kuliya be fasa mata firfita yana jero mata sannu ba.
Sai da ya ga ta dawo hayyacinta ne ya dubeta da kyau, ya ga yanda take ta sauƙe ajiyar zuciya, be san lokacin da ya ja ta jikinsa ya rungumeta daga zaune da suke ba.
Idanuwan Mishal ne suka ƙara girma, a lokacin da ta fuskanci cewar ita ce a tsakiyar hannayen Kuliya, ita ce a kusa da shi, kusan da har suna iya jiyo bugun zuciyar juna, babu abun da ya ba ta mamaki sai yanda ta ji zuciyarsa na aiki da sauri, mamaki ne ya kamata na me ya tsorata shi har haka.
Yanda ya ƙara matseta a cikin jikinsa ne ya sa ba shiri jikinta ya shiga kyarma, tun da ta zo duniya ba za ta iya tuna lokaci guda da ta shiga yanayi irin wannan ba, tabbas tana rungumar 'yan uwanta, amma wannan rungumar ba irin waccan ba ce, wannan ta sa ban ce, kamar akwai wani abu na musamman tattare da kusancin nasu, sai ta ji ba ta son ya saketa, kamar su ci gaba da tsayawa a hakan, saboda ta ji rungumetan da ya yi kamar ya na son kangeta daga wani abu mara kyau dake shririn faruwa da ita ne.
“Daga magana sai ki suma?!, me ya yi zafi haka Hafsat?!”
Muryarsa ta faɗi bayan wani lokaci, kuma amon muryar tasa ne yasa Mishal ta ƙara matse jikinta cikin nasa, muryar kamar ba tasa ba, kamar ba Kuliya ne ya yi maganar ba, da ma ya iya magana a tausashe kamar haka?, To ai gwara da ba ya yin magana a tausashen, don wata ƙila da ace yana yi, da duniyar ce gaba ɗayanta za ta yi haske cikin duhun daren.
A hankali ya saketa yana kallon fuskarta, a karo na farko Mishal ta ji ba ta san haɗa ido da shi, hakan ya sa ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Kamar wanda aka jefowa tunaninsa daga sama haka Kuliya ya dawo hayyacinsa, sai yanzu ya gano abun da ya yi, ba shiri ya miƙe tsaye yana ɗaga kafaɗarsa ta dama, kansa ya kawar gefe, zuciyarsa na ƙara saurin gudun da take a ƙirjinsa, don sai yanzu ma ya ji wani irin shock a jikinsa na riƙetan da ya yi.
Da ƙyar ya lalubo muryarsa cikin faɗin.
“Ki...
Ki kwanta ki yi bacci kawai, sai da safe!...”
Ya faɗi ya na shirin juyawa, amma sai muryar Mishal dake ƙoƙarin miƙewa ta dakatar da shi.
“No... na ji sauƙi za mu iya tafiya”
Juyowa ya yi ya na kallonta, amma ita kuma ta ƙi yarda su haɗa ido.
Shi ya masa gane mata, yanzu fa ta suma?, kuma sai ta ce su fita?.
“No, kina buƙatar hutu, don haka ki kwanta kawai...”
Cewar Kiliyan yana ƙoƙarin juyawa a karo na biyu, amma sai muryar Mishal ɗin ta ƙara katse shi.
“Da gaske nake na ji sauƙi, babu wani babbar matsala, na riga da na saba da wannan ciwon, so it's common”
Juyowa ya kuma yi ya na kallon fuskarta dake kallon ƙasa, kamar me shirin san tantance gaskiyar abun da ta faɗi.
*
Da gudu motar Kuliya ke tafiya a kan titi, yayin da Mishal ke zaune a gefensa, kayan da suke jikinta ɗazu su ne a yanzu ma, sai dai wani baƙin gyale da ta ɗora a kanta, hanya kawai take kallo tana tuna abun da ya faru ɗazu, yanda Kuliya ya matseta a cikin jikinsa, da yanda damuwa a kulawa suka bayyana ƙarara a cikin muryarsa, abun ya burgeta ya kuma bata mamaki, ba ta taɓa ɗaukan cewa Kuliya na ɗaya daga cikin irin waɗanan mutanen ba.
Kuliya ya juyo ya kalli side ɗinta a hankali, akwai wani abu da yake buƙata a tare da ita, ba komai ba ne face son sanin alaƙarta da wannan me kama da shi ɗin, ya na son ya san inda ta san yarinyar, amma idan ya tambayeta kai tsaye ba lalle ta ba shi amasa ba, ya zama dole ya yi taka tsan-tsan wurin samun bayanen da yake buƙata a wurinta.
“Wani irin ciwo ne ke damunki?”
Tambayar ta fito daga bakinsa, bayan ta ratsa ta tsakanin mayaƙan dake san hanata fita daga bakin nasa.
A hankali Mishal ta juyo da dubanta gare shi, kafin ta juya ta ci gaba da kallon windown, sannan muryarta ta fito a hankali cikin shirun motar.
“Hysteria!... na gamu da ita ne sakamako wani bad memory da na taɓa samu”
Sai ya yi shiru ya na san ganr inda kalaman nata suka dosa, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, yayin da yake juya kan motar zuwa wata kwana.
“Wani bad memory kika samu haka?”
A wannan karon shi kansa sai da ya jinjinawa kansa na iya jefo mata tambayar, don shi ba ya surutai barkatai irin haka, idan ka ga hirsara da mutum na tsayi to a kan aikinsa ne, bayan nan kuma ba ya wata doguwar hira da kowa sai da Anna, ita ma sai su shafe tsawon wattani ba'a samu hakan ba.
“Wani cousin brotherna ne, ya...
Yi attempting min...
Fyaɗe!...”
Duk da ita yarinya ce ta san cewa sam kalmar 'Fyaɗen' ba ta da daɗin saurare, musamman ma ace miji za'a faɗawa faruwarsa a kan matarsa, abun akwai ƙona rai.
Kuma sai da ta lura kamar kan motar na shirin ƙwacewa daga haannunsa, kafin ya seta kan motar da ƙyar, ya juyo ya kalleta na wasu 'yan sakkani, amma kuma ya kasa cewa komai.
“A lokacin mun je hutu Maiduguri hutun Sallah...
Sai ɗaya daga cikin cousins ɗina ya aike ni ɗakinsa, kasancewar tare suke kwana da shi Yazid ɗin ya sa a sanda na shiga ɗakin na gashin kwance a kan gado...
Ban masa magana ba, dan da ma can Allah bai haɗa jinina da nasa ba, na nufi lokar Mu'ammar, wato shi wanda ya aikeni ɗin...
Ban za ta ba na ji ya tura ƙofar ɗakin...
Na tsorata amma ban nuna masa tsoron ba, na dake har na ɗauki abun da na zo dominsa, a sanda na juya sai na iske shi tsaye a jikin ƙofar...
Ban ƙara masa kalo na biyu ba na nufi ƙofar dan na fita, ina zuwa kusa da shi ya kamo tsintsiyar hannun, ya finciko ni da ƙarfi zuwa baya...
Ba shiri na faɗa kan gadonsa, ni kuma sai na shiga ƙoƙarin tashi, a lokacin ne ya daka min wata tsawa da har na koma ga Ubangijina ba zan manta da ita ba.
A kan idona ya shiga cire kayan jikinsa.
Ba ni da tsoro amma na tsorata a lokacin, ban ankara ba har ya iyo kaina ya danne ni, kuma cikin ikon Allah sai aka bankaɗo ƙofar daga waje.
Aki Abubakar da Aki Arman suka shigo ɗakin, ganin na jima ban dawo ba ya sa suka biyo baya na.
Ko a sanda aka fita da ni daga ɗakin ba na hayyacina.
Tun daga lokacin na gamu da Hysterianan!”
A lokacin da ta kai ƙarshen maganar hawaye har ya wanke mata fuska,duk da ita ba ta gama mallakar hankalin ba, amma tasan ciwon kanta, mace ta zauna ta na baka labarin yanda aka haike mata ba ƙaramin abun baƙinciki ba ne.