← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 80

Sashe 42

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma babban abun haushin shi ne, me laifin fyaɗe ya aikata, duk da tarin hujjojjin da suka gabatar a gaban kotu, haka aka kori ƙarar ba tare da la'akari da rayuwar ƙaramar yarinyar da aka lallata ba.

Mishal ba ta ƙara bi ta kansa ba sai da ta kakare a wani wuri, kuma ba ta da wanda za ta iya tambaya bayan shi, shi ɗin da a yanzu ba ta da kowa kamarsa, shi ɗin da take zaune da shi gida ɗaya a matsayin miji.

Hakan yasa ta ɗauki littafin ta matsa kusa da shi tana faɗin.

“Abu Aswad ɗan temaka min...”
Wani kallo ya mata daga ita har littafin nata, kafin ya juyar da kansa gefe, yana ɗaga kafaɗarsa ta dama.

Mishal ba ta daddara ba ta ƙara miƙa masa littafin.

“Dan Allah ka ɗan temaka min iyaka nan ne na kasa...”
“Ke wai ba ki da hankali ne?!

Ba ki ga a yanayin da na dawo gida ba?!, Ke ba za ki iya yi da kan ki ba?!

Dole sai na miki?!”
Cike da hargagi yake mata magannar, yayin da ya miƙe tsaye, har wani ɗaga hannu yake kamar me shirin kai mata duka, cike da dauriya Mishal ta miƙe tsaye, don ba ƙaramin tsorata ta yi ba.

Ido cikin ido ta kalleshi, hannunta riƙe da littafin da kuma pen.

“Kai ba ka isa ka ce ba ni da hankali ba, don kawai ina yarinya ba shi zai sa a min kallon mahaukaciya ba, ina da hankali, na kuma san inda ke min ciwo.

Don ka dawo gida ranka a ɓace sai ka huce a kaina?, Na ji ina da laifi don na maka magana yayin da kake cikin fishi, amma na roƙeka da kada ka sake min tsawa, saboda ba'a min tsawa!”
Tana kawai nan ta tattara kayanta ta yi ɗakinta cikin ƙunar rai.

Kuliya ya dafe kansa ya na rintse ido, me ya shiga kansa haka har ya mata tsawa?, ya rab!, ya kamata a ce ya na iya sarrafa fishinsa.
*
Mishal na zaune a kan wata doguwar kujerar balcony ɗin ɗakinta, littafin math ɗinta ne a je a gefenta, don ta kasa wucewa wurin, ga kuma ranta da ya ɓaci, babban ɗan yatsanta na dama sanye cikin bakinta tana sha, tana kalon hasken farin wata, wai ko zuciyarta za ta washe da wannan baƙin cikin da Abu Aswad ya ɗura mata.

Ƙofar ɗakin ta ji an turo, hakan ya sa ta juya ta kalli cikin ɗakin, Kuliya ta ga ya shigo, ya na wani abu kamar mara gaskiya, hakan ya sa ta yi ƙwafa tana juyawa, ta ci gaba da shan hannunta.

Ƙaraaowa ya yi ya, ya tsaya a bayanta, sannan ya mata gyaran murya, Mishal ta yi kamar ba ta ji shi ba, hakan ya sa ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita, littafin math ɗinta dake tsakaninsu ya kalla, sannan ya kalli fuskarta ta cikin hasken farin wata da kuma na wutar nepa.

“Wai har yanzu ba ki dena shan hannu ba?”
Yanzun ma banza ta masa, a karo na farko Kuliya ya ji haushin kansa, ya ji haushin zuciya da ta ingiza shi har ya aikatawa amanarsa haka, a karon farko ya ji cewar ya yi nadama, ya yi nadamar yi wa wani masifa.

Hakan yasa ya ɗaga hannayensa, tare da kama kunnensa.

“I am sorry Mishal!”
Wasu kalama da rabonsa da ya furtasu ga kowa tun bayan ranar da ya taso daga asibiti, bayan nan kuma ba zai iya tuna rabonsa da furtasu ba.

Cike da mamaki Mishal ta cire hannunta a baki ta juyo ta kalleshi, ba ta san shi sosai ba, amma tana da tabbacin ba saba faɗar kalaman ya yi ba, yadda suka fito daga kan harshensa ne ya sa ta tabbatar da hakan, sai kuma inkiyarta da ya kira, da idan zai ma ta magana sai dai ya ce Hafsat, amma yau Mishal yace, ga kuma kunnuwansa da ya riƙe.

Sai ya zamemata kamar wani maraya
“Raina ne a ɓace, ni kuma ba na san a min magana idan raina ya ɓaci”
Kuliya ya faɗi yana ɗaga ƙafaɗarsa ta dama, Mishal ta juyar da kanta gefe, ta na ci gaba da kallon farin wata, kafin muryarta ta fito.

“Hargagi da ɗaga murya ba ya saka mutum ya huce haushi, sannan ba ya maganin ɓacin rai”
Kuliya ya ci gaba da kallonta ya na mamakin hankalin da ya ga ta yi a yau, kamar ba wannan mashiririciyar ba.

“Me zan yi dan raina ya huce?”
Mishal ta juyo ta kalleshi, jin yanda amon muryarsa ya fito a sanyaye.

Ba tare da tace masa komai ba, ta miƙe ta zagaya ta bayansa, shi ya ɗauka ma cikin ɗakin za ta koma, be za ta ba ya ji sauƙar hannayenta a kan kafaɗunsa duka biyu, dai-dai doron wuyansa, hakan ya sa ya lumshe idonsa a hankali, don sauƙar hannun nata a kan jikinsa ya sauƙar masa da wani yanayi mara fasaltuwa.

A hankali Mishal ta shiga matsa gurin tana masa tausa, idonsa a lumshe ya ɗaga kannsa sama, hakan ya sa kansa ya karu da jikinta, ita ma idon nata ta lumshe, dan ta ji sak wannan yanayin da ta taɓa ji a sanda ya rungumeta.

Ci gaba ta yi da masa tausar, kafin muryarta ta fito a hankali, kuma har lokacin idonta a lumshe yake, kamar yanda nasa suke a lumshe.

“A duk sanda za ka yi fushi.

To wannan kake buƙata!”
Kafaɗar tasa ya motsa, hakan yasa ta buɗe idonta.

“Shin za ki kasance tare da ni a duk sanda zan yi gushi?”
Wani abu me kama da farin ciki ya motsa a ƙirjin Mishal.

Hakan ya sa ta kuma lumshe idonta tana danna masa kafaɗar.

“Insha-Allah”
Allah ne kaɗai ya san yanda abun da take masa yake sanyaya zuciyarsa, ya ji duk wata damuwa da ɓacin ransa sun bi iska.

A hankali ya buɗe idonsa, sannan ya janye kansa daga jikinta, hakan yasa ita ma ta buɗe idonta, sai ta ga ya na janyowa littafinta.

A kan idonta ya buɗe littafin, sannan ya tsaya nazartar problem ɗin, kafin ya shiga mata solving.

Cikin abun da bai fi minti uku ba, ya gama mata, kuma har lokacin tana masa tausar.

“Nagode”
Ta faɗi a saitin kunnensa, ya ɗaga hannunsa na dama ya ɗora a kan nata dake kan kafaɗarsa.

Hakan ya sa Mishal jin wani abu me kama da shock ɗin wutar nepa ya ratsa fatar hannunta.

“You are welcome!”
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja*
*10:00 PM*
RAJA POV.

“Zaid”
Rhoda ta kira sunansa, hakan ya sa ya ɗaga haɓarsa daga hannunsa da ya yi tagumi, ya juyo ya kalleta, zaune yake a kan kujerar dake ɗakinsa, gaba ɗaya tunani ya hana shi sukuni, ya kasa gane abun da ya kamata ya yi.

Kallon Rhodan ya yi na 'yan wasu sakkani, sanye take da pyjamas iri na jikinsa, hannunta a dama riƙe da trayn abinci.

Sai kuma ya juya ya ci gaba da kalon ƙofar bathroom, kamar me jiran fitowar wani daga ciki.

Rhoda ta girgiza kanta ta tako har gabansa, zama ta yi a kusa da shi, sannan ta aje taryn hannunta a kan coffee table, ta dafa kafarsa ta dama tana kallon gefen fuskarsa.

“Me cece damuwar?”
Hannunsa ya sa ya shafa gaba ɗayan fuskarsa, sannan ya sosa kansa.

“Wani tunani kike ga Ammata za ta yi a kaina?”
Rhoda ta yi murmushi.

“Dude!

Babu macen da ta isa ta ce bata sanka, baka da wani aibu, look at your self Bro, you are dazzling, smart, athletic, stylish, chaming and elegant!”
“Ummm!, Yaushe ƙanwata ta girma haka?”
Ya tamabaya yana wani murmushi ɗan guntun murmushi, Rhoda ta yi murmushi tana kwantar da kanta a kafaɗarsa.

Sun ɗan ɗau lokaci a haka, kafin ta ɗago da kanta ta na ɗaukar trayn dake ɗauke da abinci.

“Yanzu dai ka ci abinci”
Ita da kanta ta shiga bashi a baki yana ci, don zuwan nata ya sauƙa-ƙa masa ruhi, saɓanin da da komai ya jagule masa.

Maganarta ta ba shi ƙwarin gwiwa sosai, kuma ya ji cewar tabbas, babu abin da zai hana rabi'a ta so shi.
*Brickhall school, Kaura District, Abuja*
RABI'A POV.

“...Seesee!”
Mishal ta kirata, ganin gaba ɗaya hankalinta ba ya kanta, tun ɗazu take ta famar mata hira, amma ba ta amsa mata, hakan ne ya ankarar da ita cewar Adawiyyan ba ta cikin hayyacinta.

Firgi-git Rabi ta kalleta.

“Ummm”
Ta amsa tana kallon Mishal ɗin, Mishal ta kalleta cikin nazari.

“Ba ki da lafiya ne?”
Rabi'a ta girgiza kanta.

“Lafiya ta ƙalau.Tun rannan na ce miki ki riƙa ɗaura ɗankwali ko hula.

Me ya sa bakya sakawa?”
Ta faɗi cikin son bagarar da wancan zancen, don Mishal ba za ta iya mata maganin damuwar da take ciki ba, ga shi yau monday, tarradaddinta shi ne yanda za ayi ta haɗu da Raja, ta na son ganinsa, amma kuma wani ɓangare na zuciyarta ba ya maraba da hakan.

Da yake ita ma Mishal ɗin wasu lokutan ba wayo ta ci ka ba, sai ta shafa kanta, ta na sinne kan cikin alamun rashin gaskiya, saboda tun rannan Anti Adawiyyan ta ce mata ta riƙa saka hula ko ɗankwali, don a yanzu ta zama matar aure, kuma sai ba ta yi hakan ba.

“Na zo da hular fa.

Ba ri na saka”
Ta faɗi ta na jan jakarta, tare da buɗeta, wata baƙar hular sanyi ta fitar daga cikin jakar, sannan ta saka a kanta.

“Ko ke fa, ai kin fi kyau a haka”
Mishal ta ɗan yi murmushi.

“Kowa a class ɗinmu ya na ta magana a kan ball ɗin da kuka yi rannan, yaushe za ku sake?”
Rabi ta ɗan yi murmushi, don ta ɗan fara samun sauƙi a ranta.

“Duk sanda kuka saka rana, amma ban da yau”
Daga haka suka shiga hirar ball, kafin ɗaya daga cikin masu aikin shara a makarantar ta zo kiran Rabi'a, kan ta zo za ta yi aiki a ɓangaren kwanan ɗalibai.
Chapter 42 · 0% Book details