Sashe 12
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani abu dake ƙara burgeta da gidansu kenan.
“Ina Iqra da ijaz?”
Ta tambaya tana sakinsa.
Kanta a sama wurin kallon fuskarsa, sbd tsayin da ya fita.
Kasancewar shi dogo ne, ita kuma gata ba wani tsayi gareta ba.
“Suna waje, har da su Ammy muka taho”
Zuciyarta kamar ta fito waje don murna, Allah ya dubeta yasa ba za ta yi bikin sallah lami ba, dan tunda har duka mutanen gidansu suka zo, to shikenan, matsalarta ta zaman kaɗaici ta yanki.
*Unguwar Madallah, Suleja, Niger State*
*07:44am*
RABI'A POV.
Ba ƙaramin farin ciki take ciki ba, kallo ɗaya za ka mata fahimci hakan, saboda daga kun haɗa ido za ka ga ta maka murmushi, duk da dama ita gwanarsa ce.
Amma na yau ya fi na kullum.
Jin kanta take kamar kowa, yau Allah yasa ita ma ta saka sabon kayan da za ta tafi idi da shi.
Saɓanin sauran shekarun da ta shafe a gidan, a da sai dai Saratu ta bata kunce ta saka.
Amma yau ita ma gata da nata sabon kayan, sai dai duk da haka bata da takalmin sakawa, shi yasa Saratu ta bada ɗaya daga cikin nata, Da murnarta ta zangari takalmin ta saka.
Tun da ta fito daga wanka ta saka kayan Mama ke binta da kallo, amma ba ta ce komai ba, har suka shirya suka fito dan tafiya wurin idi.
Rabi ba ta san sanda Mama ta dawo gidan ba, ita dai kawai ta farka ta ganta.
Kuma ba ta ce komai ba, ta ja bakinta ta yi shiru, tun da har uw*rta tasan abin da take.
A bakin ƙofar ɗakinsa suka ga babansu, kowa a cikinsu ya wani ɗauke kai babu ma mai shirin gaishe da shi, sai Saratu da ita, kuma shi ma bai wani amsa musu da mutumci ba, sama-sama ya amsa su.
Ita kuma Rabi ba ƙaramin mamakinsa take ba, kusan kwanansa huɗu baya gidan, ko jiya har suka kwanta ba ta ga dawowarsa ba, wata ƙila ma da asuba ya dawo, don ba ƙaramin aikinsa ba ne.
Mutumin da ya taɓa kawo karuwa cikin gidan matarsa ta auren sinnah, ai fiye da haka ma zai aikata..
“Ah-ah, Karfa, a ina kuma kika samo sabon kaya ?, in ji dai ba sata ki kai ba?”
Muryar Habiba ta katseta, hakan yasa ta juyo da sauri ta kalleta.
Rabi ta tsorata, dan jiya basu san an bata wani kaya ba, tana shigowa da ahi ɗaki ta shige, Anti Saratu kawai ta nunawa.
“Saurayinta ne ya kawo mata, ba sata ta yi ba”
Saratu ta bata amsa.
“Sh*iya munafuka!
Ashe jiya da kika je siyan katin tsayawa ki kai a lungu ya gama lalube ki sannan ya baki kaya?”
Habiba ta faɗi cikin kama baki.
“Ai ni na jima banga baƙar munafuka irin wannan yarinyar ba, kin ga fa jiyan da ta dawo, ɓoye kayan ta yi a cikin hijabinta, dan kada mu gani”
Mama ta faɗi tana aika mata harara.
“Ya isa haka dan Allah, to duk sharrinku a ƙofar gida ya bata, da za ku ɗorawa marainiyar Allah shari, dan Allah Umma ku riƙa duba baya, idan an giram a san an girama”
“Kan abu ta kaza-kazacan!, Saratu!
Ni ki ke faɗawa irin waɗanan maganganun ?.....”
Sararu ta juyar da kanta gefe daga barin kallon Umman, ta kalli Rabi wadda hawaye suka wanke mata fuska tun a sharin farko da aka laƙa mata.
Hannunta ta ja suka fita daga gidan, dan ta ga kamar su basu da niyyar zuwa idin, su da suke da niyya gwara su yi sauri, don kada su rasa.
Da sauri Ɗan Lami ya bi bayansu, dan ko ba komai yasan akwai 'yan kuɗaɗe a hannun Saratu, shi kuma kuɗaɗen da ya ara sun ƙare kaf, bai ta shi da ko sisi ba.
Kuma gashi yana san zuwa idin, ko ba komai Saratun za ta masa kuɗin babir.
“Umma da alama fa sai kin ɗau mataki...”
Cewar Mama.
“Ni kuwa na ga hakan, kada ki damu, zan ɗau ƙaƙƙwaran mataki kuwa”
“Ke Fati, uw*r me kike a ɗakin ne?, dallah ki yi sauri ki fito”
Mama ta faɗi cike da masifa tana kallon ƙofar ɗakinsu, Habiba ta shiga soshe-soshen ƙeya.
“Amm, Mama na ce Alhajin jiyan nawa ya baki ?”
Mama ta juyo ta kalleta tana haɗe rai.
“Ni ba na san bita da ƙulli, dubu hamsin ne, ya ce babu kuɗaɗe a hannunsa, zan baki dubu biyar kawai...”
Habiba ta yi murmushin yaƙe.
“Haka ne, amma dai an kinsa dai ko kuɗin ɗinki shaddara da na ɗinka miki a sallar nan ya fi dubu biyar...”
“Ni fa Umma na gaji da gorin da kike min!, kawai dan kina min ɗinki sai ki kafa bina da bita da ƙulli?...
Da na ce dole sai kin min ɗinki?...
Idan ba ki min ba ma samari na za su min ai!”
Kamar Maman ita ce uwa haka takewa Habiban faɗa.
“Haba Mama, abun fa ba na ɓacin rai ba ne, ki kwantar da ranki mana”
Mama ta ƙara juya kai tana huhhura hanci.
Ƙarshen zamanin kenan, dama an sanar da mu cewa; baiwa za ta haifi uwar gijiyarta,to ga kyakkywan misali nan Habiba da Mama.
Sannan an ce abun da ka yi shi za'a maka, hakan ce ke faru da rayuwar gidan Ɗan Lami, amma shi sam bai lura da hakan ba, dan ba iyalan nasa ne a gabansa ba.
(Allah ya fihsemu turba mai kyau🙏).
Bayan an sauƙo da ga idi, Saratu da Rabi gida suka dawo, in da Mama ta wuce yawon gantalinta, Habiba da su Fati ma gidan suka dawo.
Kuma tana dawowa ta laftawa Rabi aikin abincin sallah, haka Rabi ta cire sabon kayanta ta hau aikin ba ji ba gani, duk da Saratu na tayata da wani abu.
Da haka har suka yi suka gama, kuma bayan sun gama ba'a bawa Rabin abincin ba, sai kusan la'asar aka ɗan zuba mata kaɗan a kwano, wai duk dan a ƙuntata mata.
Naman da kajin data soya ma ba'a saka mata ba, sai wanda Habiban ta ci ta bari, kuma ita hakan bai dameta ba, don bata damu da cin kaza ba, tafi san kifi, kaza bata birgeta a rayuwa.
Duk da haka sai da Anti Saratu ta ɗiba mata naman ta bata, tace mata ta ci, ai da kuɗin da ta nema aka sayi naman.
Bata san yi mata musu shi yasa ta ci ɗin, ba wai don naman ya mata daɗi ba.
Da la'asar Zara ta shigo gidan tace ta zo su je yawon zaga gari, da farko sai da Habiba ta hana, amma da Saratu tayi uwa tayi makarɓiya sai ta haƙura ta barta.
A wurin Rabi wannan sallahr ta musamman ce.
Saboda tana cikin farin ciki, komai na tafiya mata dai-dai.
Har ta fara ganin kamar wahalarta ta ƙare a rayuwa.
Abun da ba ta sani ba shi ne; wasu abubuwan ma yanzu ne suka soma, wata wahalar ma bata shigeta ba tukkuna, wani ciwon ma bai sameta ba har yanzu!.
Wani sabon kukan ƙunci da damuwa na nan tafe a gaba.
Akwai ƙunci da baƙin ciki a rayuwa, akwai damuwa da iftila'i a rayuwa, akwai damuwa a akan wata damuwar.
Ƙaddarar kowa da ban ce, kamar yanda Labarin kowa yake da ban.
Labarinta yanzu zai soma, haka mahaifiyarta ta faɗa.
Kuma yanzu zai soma ɗin.
Don ba ayi komai ba ma, labarinta zai sauya tare da faruwar wata ƙaddara mai zuwa nan da 'yan kwanaki masu zuwa, ƙaddarar da za ta sauya komai, ta tarwatsa komai, sannan ta gyara wasu abubuwan.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#Taurariwriters
°°°°°°°°°°°°°°°°°
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*05*
~~~
*You never have to pretend with me, just give me your raw truth, all your imperfections and fears, and i will show you how beautifully broken pieces fit together*
***
*Badawa layout, Kano...*
RAJA POV.
Kayan da ya san zai buƙata yake shiryawa a cikin jakarsa ta matafiya.
Hannunsa na dama ne ya janyowa wata riga, tahowar rigar ya yi dai-dai da faɗowar wani hoto.
Kansa ya sunkuyar ƙasa, idonsa ya sauƙa a kan fuskokin da ke jikin hoton.
Waɗanan lumsassun idanuwan nasa suka kafe hoton suna kallo.
Mutum uku ne a jikin hoton, na farko fuskarsa ce, waɗanan gray ƙwayar idanun nasa ce tasa ya gane hakan, sai kuma fuskar Aliyu, sannan ta Momma, wato mahaifiyarsu.
A hankali ya aje rigar, sannan ya tsugunna ya ɗauki hoton, har wa yau bai manta ranar da aka ɗauki hoton ba.
_“Kai Aliyu tsaye daga nan.....
Kai kuma Zaid ka tsaya a haka....”_
Wannan shi ne abinda ta faɗi a wancan lokacin.
Dariyar da suka yi a wancan lokacin ta shuga amsa kuwwa a cikin kunnuwansa.
Ba shiri ya yi saurin cilla hoton cikin jakar da zai yi tafiyar.
Zuwa yanzu hoton ya sauya a idonsa, daga cikin falon gidan da aka musu hoton, zuwa baƙin gidan da wuta ta gama cinyewa.
Wayarsa ce ta shiga ruri, hakan yasa dubansa ya kai kanta.
'UCHECHI' Shi ne sunan dake yawo a kan screen ɗin, duk yanda aka yi yasan zuwa gidan ta yi.
Rhoda da su Zuzu suka hanata shigowa.
Sai kawai ya fasa ɗaga kiran nata ya katse kiran, sannan ya aikawa Rhoda kira.
Daga can harabar gidan kuwa, Rhoda da su Alandi ne suka tare bakin gate, suna zagin Uchechi, tare da faɗa mata ba fa za su barta ta shiga cikin gidan ba.
“Ke ki bar nan!....”
Cewar Rhoda tana zare mata ido, Uchechi da ta kai iya wuya, ganin ta kira wayar Raja ya katse mata tace.
“Ba zan tafi ba, sai kun bar ni na ga masoyina...”
“Sh*giya 'yar wahala kawai...
Karya me bin maza...
A haka za ki ƙare....”
Jagwado ya faɗi cikin muryarsa dake nuna cewa a buge yake.
“Duk abinda za ku faɗa ku, faɗa, ni dai ba zan tafi ba... har sai kun barni na ganshi...”
“Ai ko za ki riɓe a nan...
'Yar akuya kawai...”
Alandi ya faɗi yana maka mata harara kamar wata mace.
Me gadi na daga bayansu yana kallonsu, kusan kullum ita Uchechin sai ta zo gidan.
Kuma da zarar su Rhodan suna nan basa barinta ta shiga.
“Rhoda!
Let her in!”
Muryar Raja ta faɗi daga bayansu.