← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 80

Sashe 26

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Eh, a nan nake da zama”
“Wannan ɗayar ƙanwarka ce ?”
Ta kuma tambaya, hakan yasa ya kalleta kaɗan, wato jiya shi ya mata tambayoyi, yau kuma ita ce ke masa.

Kafaɗarsa ya ɗaga cikin faɗin:
“Sunanta Rhoda, kuma ƙanwata ce”
Rabi ta gyaɗa kanta tana kallon hanya.

“Kai ma Cristian ne ?”
Sai da ya ɗan tsaya ya kalleta na 'yan wasu sakkani, sannan ya ci gaba da tafiyar.

“Ni musulmi ne”
“To miye ma'anar RAJA ?!”
Ta tambayi abin da ke mata yawo a ka tsawon lokacin da ya faɗa mata sunansa.

Bisa ga mamakinta sai ta ji ya yi murmushi, hakan yasa ta juya ta kalleshi, murmushin kuwa yake, wanda ya ƙara bayyana kamarta da shi.

“Raja na nufin Fata, i mean wish, za kuma ki iya kiransa da hope, amma sunana na gaskiya Zaid ne!”
Zaid?!, Zaid!?, Zaid?!...

Ta maimaita sunan kusan sau biyar a cikin ranta, to Zaid ɗin bai fi ba?, amma ya na wani kiran kansa da Raja.

Sai ta tsaya a sanda suka fito bakin titi.

Kamar jiya yau ma sai da ya tsaida mata taxi, sannan yace kada a ɗau kowa sai ita.

Daga haka ya ɗaga mata hannu, ya koma layin da ya fito.

Rabi ta yi murmushi tana kallon hanya.

Hirarta da shi na sa ta nishaɗi sosai.
*No. 213, Naf Belly Estate, Asokoro, Abuja*
KULIYA POV.

A hankali ya sako ƙafarsa ta dama cikin falon gidan Anna, wadda take zaune a kan kujera tana tsige zogale.

Kanta ta ɗaga ta kalleshi.

Ba shiri ta miƙe tsaye, hakan yasa trayn zogalen dake kan cinyarta kifewa a ƙasa, zogalen ya zube.

Ba komai ya bata tsoro ba, sai ganin yanda idanuwan Kuliyan suka yi ja, fuskar tasa ma ta yi ja, bisa ga dukkan alamu kuka ma ya yi.

Suna haɗa ido da ita ya fashe da kuka, ba ƙaramin razana Anna ta yi ba, sanin halin ɗan da ta rena, Kuliya ba ya kuka a kan abu ƙarami, idan har ka ga ya yi kuka, to abun ba ƙarami ba ne, ita za ta iya cewa ma tun ranar da ta dawo da shi Abuja har wa yau bata taɓa ganin kukansa ba.

Da sauri ta ƙarsa kusa da shi, kuma tana zuwa kusa da shi ɗin ya rungumeta yana fashewa da kuka.

Anna ta ja hannunsa ta zaunar a kan kujera bayan da ya saketa, da gudu ta shiga kitchen ɗinta, ta ɗauko ruwan sanyi ta ba shi.

Sannan ta zauna a gefensa tana shafa kansa.

“Me ya sameka Aliyu?”
Kuliya ya aje gorar ruwan da ya shanye kusan rabinta, sannan ya share hawayensa.

Yana kamo hannun Anna.

“Ba na faɗa miki cewar yau za mu fita kame ba ?”
Ya faɗi cikin wata murya mai rauni, wadda za ta iya cewa sam ba ta san ɗan nata na da ita ba.Da sauri ta gyaɗa masa kai tana shafa kansa.

“To a wurin ne...

Ɗaya daga cikin 'yan ta'addan ya yi ƙoƙarin harbi na, shi...

Shi ne Abubakar abokina, ya ture ni...

Shi...

Shi kuma harbin ya same shi!”
Annan ta gyaɗa kai, dan tasan Abubakar ɗin.

“To yanzu me ya samu Abubakar ɗin ?”
Ya haɗiye yawu yana share hawaye.

“Shi ne muka kai shi asibiti...

Bayan an masa tiyata an cire alburushin...

Yace a kira masa kawunsa...

Ni da kai na...

Na kira kawun nasa, na yi masa kwatance, ya zo ya samemu har asibitin...”
Ya kai hannu yana share hawaye, sannan ya ci gaba.

“To Kawun nasa na zuwa, yace yana so a ɗaurawa ƙanwarsa aure kafin ya rasu...

Da kawun nasa ya tambayeshi waye mijin...

Sai...

Sai yace ni ne, cewa ya yi ni ne Anna!”
Ya ƙarashe a raunane.

Anna da ta fara fahimtar inda zancen ya dosa, ta share masa hawaye ta na masa alamun ta na jinsa.

Sai da ya ja hanci sannan ya ci gaba.

“Yanzu haka an ɗaura mana aure da ƙanwar tasa, Anna wani irin so Abubakar yake min?, da har zai iya kasada da rayuwarsa ya ceci tawa, sannan ya aura min ƙanwarsa da yake ganin ita kaɗai ce ta rage masa!”
“Kana da zuciya me kyau Aliyu, duk da kana da saurin fusata, ni nasan kana da kyawawan halayen da za'a so a tare da ɗan adam na gari...

Yanzu ina Abubakar ɗin?”
Annan ta tambaya tana ƙara share masa hawaye, bisa ga mamakinta sai ta ga ya kwantar da kansa a kafaɗarta yana fashewa da kukan da ya fi na ɗazu, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.

“Anna Abubakar ya mutu!, Muntuna biyar da gama ɗaurin auren ya mutu!, Anna kuma bai mutu ba sai da ya kama hannuna, sannan yace na kula masa da ƙanwarsa, kada na bari ta wahala, Anna ina zan kai wannan nauyin?, Ina zan kai nauyin da ya ɗora min?!”
Anna ta rintse ido, a sanda take jin sauƙar hawayensa a kan jikinta, da ƙyar ta daure ta ci gaba da shafa bayansa.

“Allah zai temakeka Aliyu, shi kuma Abubakar Allah ya ji ƙansa, ya sa mutuwar ita ce hutu a gareshi, Allah ya baku zaman kafiya da matarka, ya kauda idomln maƙiya daga kanku!...”
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*10*
~~~
*Do something for her that no one has ever done, love her for who she is.*
***
*Shekara ta 2000.*
“Malam Ila ina kwana”
Cewar Zaid yana tsugunnawa har ƙasa, a sanda ya shigo shagon Malam Ila, wanda ke saida kayan provision a 'yar ƙaramar containerrsa.

Baki washe Malam Ila ya amsa masa, kafin Zaid ya miƙe ya zauna a kan bencin da Malam Ilan ke kai, suka kuma gaisawa, kafin Malam Ilan ya ba shi abincin da ya siya ya aje masa, kamar yanda suka saba kullum.

Don a kwanakin kullum idan ya zo sai ya ba shi abinci, karɓa ya yi sannan ya ci, suna 'yar hira jifa-jifa.

Kuma a cikin hirar ne Malam Ilan ya sosawa Zaid inda ke masa ƙai-ƙayi.

“Ya kamata ka je ka dubo ƙanin naka, ka ga fa yau kusan satinsa ɗaya a can!”
Aliyu ya aje kwanon hannunsa sannan yace.

“Ai wai kar su ga gaggawata ne shi yasa, amma ina kewarsa, don ba mu taɓa nisa da juna irin haka ba...

Tazarar awa ɗaya ne tsakanina da shi a haihuwa, kuma bayan wannan tazarar ba mu sake samun wata tazara ba...

A ko da yaushe muna tare”
Cike da tausayawa Malam Ila ya girgiza kansa.

“Ka ga abun da za ayi shi ne; zuwa gobe sai muje mu duba shi ko?”
Cike da zumuɗu Zaid ya ɗagaa kafaɗarsa.

“Allah ya kaimu goben, na gode Malam Ila, Allah ya saka maka da alkairi...”
Washegari da sassafe Zaid ya dira a ƙofar shagon Malam Ila, ko fitowa ma bai yi ba, haka ya zauna ya na jiran fitowar Malam ilan.

Sanye yake da wani farin yadi, wanda Malam Ila da kansa ya bashi, don yace ba ya san ganinsa da wannan uniform ɗin.

Kana ganin kayan za ka san cewa ba nasa ba ne, saboda yanda kayan ya masa yawa.

Ya na zaune a wurin har Malam Ila ya fito, babu yanda be yi da Malam Ila kan su wuce gidan marayun katsaye ba.

Amma Malam Ilan ya dage kan sai ya sai masa abinci ya ci tukunna.

Hakan kuwa aka yi, sai da ya sai masa abincin ya ci ya yi taf, sannan suka kama hanyar gidan marayun.

“Bawan Allah, Lafiya kuwa na ga kamar gidan marayun nan a kulle, kuma na...

Na ga kamar ma gobara aka yi!”
Cewar Malam Ila a kiɗime, hankalinsa ya yi wata mummunar tashi, bayan da suka iso gidan marayun, suka ga gate ɗinsa a kulle, kuma ko daga bakin gate din za ka gane cewa an yi gobara a wurin.

Mutumin da Malam Ila ya tambaya ya kalle su.

“Kwana huɗu kenan da wuta ta kama a gidan, kuma babu wanda ya fita da ransa daga gidan!...”
Iyaka abinda Zaid ya iya fahimta kenan a zancen nasa, bai san sanda ya yanke jiki ya faɗi ba.

Kwanansa uku a asibiti kafin ya farfaɗo, kuma da ya tashi farfaɗowar ma ba a hayyacinsa ya farka ba.

Abubuwa ya riƙa yi kamar wanda ya samu taɓun ƙwaƙwalwa, sai zantuka yake barkatai, an kasa gane kansa.

Ganin abun ba na ƙare ba ne ya sa Malam Ila ɗauke shi daga asibitin, don ya ga abun ba na asibiti ba ne.

Tashin farko gidansa ya kai shi, amma matarsa tace fafur ba za ta karɓi tsinttaciyar mage ba.

“Wa to kai ga ka juju ko?, Ub*n yaye-yaye, to Wallahi ba za ta saɓu ba!, a ina zan saka wannan gardin ƙaton?, A gida ɗaki ɗayan?, Ga ka, ga ni, ga 'ya'yana, to Wallahi Malam da sake!”
“Haba Gambo, be kamata kike faɗin haka ba, yaron nan na faɗa miki cewar maraya ne, idan ba ki manta ba; babarsa ce ta ba ni kuɗin da na miki yankan sunan Audu...”
“Wallahi ba ka isa ba, wato dan kawai uwarsa ta ba ka kuɗi ka sai mana ragon suna, sai na karɓi ɗanta ko ?, na rantse maka da Allah wannan yaron ba zai zauna min a gida ba!”
Duk da Zaid ba ya hayyacinsa sosai, amma yana iya tuna yanda matar kewa mijinta masifa da bala'i, ya na iya tuna yanda ta haƙiƙance kan ba zai zauna da ita ba.

Tun bayan da ya fuskanci cewa Aliyun da ya rage masa ya bar duniya, rayuwarsa ta shiga halin ƙaƙa na ka yi.

Ya ji gaba ɗaya ya gaji da duniyar, babu abun da ya fi buƙata sama da mutuwar shi ma, ya ji cewar yana son ya mutu kamar Momma da Aliyu, tun da da ma su ne kaɗai gareshi, to ga shi ya rabu da su, to ina zai sa kansa?.

Ba dan Malam Ila ya so ba, sai dan babu yanda zai iya, ya ɗauki Zaid ya mayar da shi gidansu na da, amma kullum sai ya kawo masa abinci da ruwan rubutun da yake karɓo masa a gun wani malami mai almajirai da yasa a yi masa, don ya temaka masa wurin dangana da halin da ya shiga ciki.
Chapter 26 · 0% Book details