← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 80

Sashe 24

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aliyu ya zauna yana kallon yayansa, yanda yake miƙa hannu yabna barar sai da ya sa shi kuka.

Wai yanzu su ne rayuwarsu ta koma haka, su ɗin da suke da gata, suke da uwa, wadda ta ɗauke musu kewar uba, su ɗin da ba su nemi komai sun rasa ba, amma cikin ƙiftawar ido, komai ya sauya, LABARINSU ya sauya, rayuwar ma baki ɗayanta ta sauya.

“A taimaka mana sadaka fi sabillilahi...”
Cewar Zaid yana miƙawa wani me shago hannu, mutumin ya miƙe a fusace.

“Kai!

Ba ɗazu ma ka zo ba?!...”
Kafin ya ƙarasa yaron shagonsa yace.

“Jiya ma sai da ya zo”
“Sh*ge, da ma da irinku ake haɗa baki ana mana sata, bar nan wurin!”
Ya ƙarashe yana hankaɗashi, har sai da Zaid ɗin ya faɗi ƙasa, da yake hakan ba komai ba ne a wurinsa, sai ya miƙe yana bawa mutumin haƙuri, don ba yau aka fara masa irin hakan ba.

Kamar wucewar walƙiya haka ya ga tahowar Aliyu da gudu, kuma kafin ya fahimci abun da Aliyun ke ƙoƙarin yi, har Aliyun ya yi tsallen albarka, ya kifawa me shagon nan mari.

“Kut!, Babbar buhun ub*ncan!, kayyasa!

Ni ka mara yaro ?!”
Cewar me shagon yana kama baki.

Aliyu da ya gama fusata a sanda ya ga an hankaɗa masa ɗan uwa yace.

“Eh ɗin, na mareka, ko akwai abun da za ka iya?”
Ya faɗi idonsa ƙyam a kan mutumin, babu wani alamun tsoro tare da shi, ji yake ma kamar zai iya kikkifa masa marin da ya fi haka, ga shi dai ba shekaru gareshi masu yawa ba, amma zafin zuciyarsa ya fi na ɗan shekara ashirin, ji yake a kan yayansa babu abun da ba zai iya ba.

Ko dan sunansa Aliyu ne ?, Oho.

Zaid ya kamo hannunsa ya na jansa baya.

“Zo mu tafi Aliyu...”
“Rabu da ni Zaid, sai na nuna masa martaba da kimarka a wajena”
Nan fa me shagon nan ya shiga zage-zage yana masifa, har maƙotan shagunansa suka fito.

Ɗaya daga cikin masu shagunan ne ya kamo hannunsu Zaid, ya ja su zuwa gefe.

“Ni kuwa yara ku ba 'ya'yan wannan likitar ba ne ta bayan layi ?”
Mutumin ya tambaya, yana ganin kammanin customern tasa a fuskar kowannensu.

Aliyu bai iya bashi amsa ba, kasancewar zuciyarsa na tafarfasa, har yanzu ji yake marin da ya yi wa me shagon nan bai wadatar ba, kamar ya na buƙatar a ƙara masa, soboda abinda ya yiwa Zaid ɗinsa.

Zaid ne ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan yace.

“Eh, mu yaranta ne”
“Kwana biyu ba na ganinta, fatan dai lafiya ?”
Zaid ya sunkuyar da kansa ƙasa.

“Yau wata biyar kenan da rasuwarta, gobara ce ta kama a gidanmu, kuma a lokacin da gobarar ta kama tana cikin gidan...”
“Innallillahi wa inna ilaihi raji'un...

Wallahi yara ban sani ba....

To yanzu ku da wa kuke zaune?”
“Ba mu da kowa, mu kaɗai ne”
“Subhannallahi, shi yasa kuke bara ?”
Zaid ya gyaɗa masa kai, don da ma shi ne yake bashi amsar.

“To kunga, ku zo ku zauna a shagona, na sai muku abinci ku ci, da yamma idan Allah ya kaimu, zan kaiku gidan marayu, ai za ku iya zama a can ko ?”
Da sauri suka kalleshi, sannan kuma suka kalli juna, ba musu suka gyaɗa masa kai.

Mutumin me suna Ila ya yi murmushi, har wa yau ya na tuna irin alkairin mahaifiyarsu gareshi.

Domin akwai wata rana da ta taɓa zuwa shagonsa ta iskeshi ya yi tagumi, ta tambayarsa; lafiya? shi ne ya shaida mata da matarsa ce ta shaihu, ga shi ko na yanka ba shi da shi.

Har wa yau ya na iya hango murmushin da ta yi a lokacin, sannan ta lale maƙudan kuɗaɗe ta damƙa masa, tare da faɗin a sha hidumar bikin suna lafiya.

Har da kukansa a lokacin, don Allah ya sani yanda yake a cikin buƙatar kuɗi.

Da ma jarin nasa ma bai taka kara ya karya ba.
*
“Na ji buƙatarka Malam Ila, sai dai a gaskiyar batu, ba mu da gurin zaman mutum biyu, yaro ɗaya kawai za mu iya karɓa, saboda yanzu haka ma gidan nan a cike yake da yara, yaro ɗayan ma za mu karɓeshi ne kawai dan ka dage”
Cewar shugar gidan marayun da Malam Ila ya kai su Zaid, zaune take a kan kujera, yayin da take kallon Malam Ila dake tsallaken kujerarta, Zaid da Aliyu kuma na tsaye daga bayansa.

A yau sun ci abincin da rabonsu da cin irinsa tun watanni biyar da suka wuce, wato ranar da Mommansu ta rasu, Malam Ila sai da ya tabbatar da sun ci sun ƙoshi, sannan ya kawo su nan wurin.

Cike da fatan zuwansu wurin zai sauya rayuwarsu, amma maganar da matar ta yi ita ta murmushe wannan fatan nasu har garinsa.

“To yara kun dai ji...

Yanzu mecece mafita ?” Cewar Malam Ila yana juyowa ya kallesu.

“Malam Ila mun gode da temakonka....

A gaskiya ba za mu iya rabuwa da juna ba, gwara kawai mu haƙura...”
Cewar Aliyu.

Bai ko rufe bakinsa ba Zaid ya ɗora da:
“A'a Malam Ila, ba za ayi haka ba, ku ɗauki Aliyun kawai, ni na haƙura!”
*
Tsaye suke a harabar gidan marayun, yayin da Malam Ila ke kallonsu yana sharar ƙwalla, Aliyu kuma na kuka, Zaid na bashi baki.

“Hey!

Don't cry, na ce maka zan riƙa zuwa ina dubaka...”
Shi dai Aliyu hankalinsa bai kwanta ba, dan ba ya jin zai iya zama a wurin nan.

A kan idonsa Malam Ila da Zaid suka fice daga wurin.

Ashe ƙarshen ganawarsu kenan, ahse ba za su ƙara ganawa ba sai bayan wasu shekaru masu tarin yawa.

Dan a cikin kwana uku kawai ƙaddarar da ta sauya LABARINSU ta afku.

Malam Ila da Zaid na fita, Malam Ilan ya kalli Zaid.

“To Zaidu, tun da ka zaɓi ka koma gidanku ka ci gaba da zama, sai ka koma can ɗin, amma duk safiya, rana kuma dare, ka riƙa zuwa kana karɓar abinci a wurina”
“Na gode Malam Ila, Allah ya saka da alkairi”
“Kai ai ba komai, ku yaran kirki ne, 'ya'yan mace ta gari, Allah ya maka albarka”
*Present day...*
*Room No.45, National Hospital, Abuja.*
KULIYA POV.

Daga kan gadon marasa lafiya, Abubakar ne kwance, yayin da na'urar oxygen ke maƙale a kan fuskarsa, kasancewar ba ya iya numfashi me kyau.

Daga gefen gadon kuma, Kuliya ne tsaye, riƙe da hannunsa, hawaye ya ke sharewa akai-akai.

Idan zai iya tunawa, rabonsa da kuka tun ranar da ya bar garin kano, ranar da ƙaddarar da ta sauya LABARINSU ta afku.

Amma a yau sai ga shi ya na kukan tsoron rasa amininsa, babban abokinsa, wanda idan ka ɗauke Anna, kaf duniya babu me iya jurar halinsa in ba shi ba, kuma ba ma haka ba, a yau ɗinan Aabubakar ya sadaukar da rayuwarsa don ceton tasa rayuwar.

Shi ɗin da bai aje kowa ba bayan Annan, shi kuma da yake da mata, yara har da ƙanwa da kuma 'yan uwa, ya iya sadaukar da rayuwarsa don kawai ya ceceshi.

Daga gefe kuma Symon da hannunsa ke ɗaure da bandage ne, sakamakon raunin da ya samu a artabun da suka yi da 'yan ta'addar nan, sai Sharon wadda ke hawaye, sai kuma Kamis, Sani da Mubarak sun yi jigum-jigum cike da jimamin abun da ya samesu, don gaba ki ɗayansu abun ya shafa.

Ƙofar ɗakin ce ta buɗe, kawun Abubakar wato Alhaji Musa ya shigo, tun bayan da aka gamawa Abubakar ɗin tiyata yace su kira masa shi, su kansa ba su san dalilin hakan ba.

Jin sautin muryarsa ne yasa Abubakar buɗe ido a wahalce, sannan ya kalli kawunsu wanda gaba ɗayansa yake a ruɗe.

“Abubakar?!

Me ya sameka haka?”
Da ƙyar Kamis ya iya masa bayanin abun da ya faru.

Kawu Musa ya zauna a kusa da Abubakar ta ɓangaren dama, yayin da Kuliya ke riƙe da hannunsa ta ɓangaren hagu.

Da ƙyar Abubakar ya kai hannunsa kan abun oxygen ɗin yana ƙoƙarin cire shi daga kan hancinsa.

Ganin hakan yasa Kuliya saurin kai hannunsa kan na Abubakar domin hanashi yin abun da yake ƙoƙarin yi.

Cike da dauriya Abubakar ɗin ya girgiza masa kai.

Hakan yasa jiki a sanyaye Kuliyan ya janye hannunsa daga kan na Abubakar ɗin, har ya samu ya cire abun, sannan ya kalli Kawu Musa.
”Kawu...

Za... ka... iya...

Tuna...

Wassiyar Ummuna...

Ta ƙarshe ?”
A rarrabe maganara take fita, haka kuma a wahalce, cikin wani sauti mara amo.

Hawaye na yi wa Kamu musa zuba ya gyaɗa kansa, don bi da bi maganganun matar wan nasa ta dawo masa, a sanda take kwance a aibiti cikin halin ciwon naƙuda, rai a hannun Allah, kamar dai yanda ke faruwa ɗanta a yaunzu.

Hawaye ya gangaro daga idon Abubakar, da ƙyar ya iya haɗiye wani abu sannan yace.

“Dukkan wasiyyunta na cika su, na reni Mishal da kaina...

Na bata kyakkyawar rayuwa...

Na...

Na bata farin ciki...

Abu ɗaya ne ya rage...”
Ya ƙarshe yana ritse idonsa, yayin da Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama cike da tausayawa.

Kawu musa ya gayɗa kansa.

“Na mata alƙawarin in dai Allah ya yarda zan aurar da Mishal ga miji na gari, sannan kafin... kafin na bar duniya, zan barta a hannu na gari...”
Kawu musa ya girgiza kai cike da sallalami.

“Ka dena faɗin haka Abubakar, Insha-Allah za ka miƙe a kan ƙafafunka...”
Abubakar ya yi wani murmushi me ciwo.

“Ba na tunanin haka Kawu Musa...

Ba...

Ba na jin zan ta...

Tashi, don haka nake so a ɗau rawa Mishal aure yanzu-yanzun nan!...”
Wani irin dokawa zuciyar Kuliya ta yi a cikin kunnuwansa.

Ya ji wata ƙara a ƙirjinsa kamar ta fashewar glass, kamar glass ɗin windown da aka jefa da dutsi.

Wai me ma yake ji ne ?, kawai dan an ce za ayi wa wata yarinya aure ?, sai gabansa ya yi irin wannan dukan ?, wai shikan wata jaraba ce ke damunsa kan wannan yarinyar ?.

Kafin ya gama shawara da zuciyarsa, Kawu Musa yace.

“Waye mijin ?”
Abubakar ya ƙara matse hannun Kuliya dake cikin nasa, sannan ya juyo ya kalli Kuliyan.

“Al...

Aliyu Zaid...

Bichi...

Ku...

Kuliya!, Babban abokina...
Chapter 24 · 0% Book details