← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 80

Sashe 43

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wai hausawa suka ce rashin sani ya fi dare duhu, domin da ace ta san abun da zai iya faruwa a wannan tafiyar tata, da ba ta fara ba, domin babbar ƙaddarar rayuwata ta faru ne ta sanadiyyar wannan aikin da aka sakata a wannan lokacin.

Haka suka yi sallama, Rabi ta tafi ɓangaren kwanan ɗaliban ta fara aikin sharar, aikin yau har ya fi na kullum, don ba ita ta gama ba sai wajejen ƙarfe 5, kuma bayan ta gama da can ta dawo ɓangaren ajujuwa, zuwa lokacin an jima da tashi, haka ta bi aji bayan aji ta share ta goge, har lokaci ya ƙure mata, don ba ta gama ba sai 7.

Wani abu sabo da ba ta taɓa yinsa ba, shi ne kaiwa magariba a makarantar, duk da akwai mutane a cikin makarantar, don akwai masu kula da ɗaliban da suke makarantar kwana, ga shi gaba ɗaya ta gaji, haka ta fito a gajiye tiƙis.

Sai da ta ɗan tsaya ta kalli ƙofar estate ɗin su Raja, ta cikin hasken fitilun da aka kunna ta ko ina a layin, sannan ta kama hanyar fita zuwa babban titi.

Yanayin tafiyarta ne kaɗai zai tabbatar maka da gajiyar da ta yi, kamar daga sama ta ji ƙaran harbi a bayanta, hakan ya sa wani abu ya yi ƙulululu!, a cikinta, tsoro mara adadi ya mamayeta, idanuwanta suka zaro waje saboda tsoro, kamar kwaɗon da mota ta take shi a kan titi, haka ta juyo a tsorace ta kalli bayanta.

Wani irin bugu da zuciyarta ta yi ya sa ta dafe ƙirjinta da sauri, don ji ta yi kamar zuciyar tata za ta fashe ne lokaci guda, nan take ta ji kanta ya sara, wani gumi da ba ta san ta inda yake fita ba ya jiƙa jikinta sharkaf, ta cikin waddataccen hasken da ya haske ko ina, ta ga RAJA tsaye a kan wani mutum, hannunsa na dama riƙe da bindiga wadda ya yi pointing ɗinta kan mutumin dake yashe a ƙasa babu rai, alamun dai shi ne ya harbin, wani irin yamutsawa cikin ya yi, hakan ya sa ta rafka wani uban salati.

“Innallillahi wa inna ilaihi raji'un!”
A firgice Raja ya ɗaga kansa ya kalli setin inda ya ji salatin cikin muryar Rabi'a, hasken fitilun wurin ya haske masa fuskarta tar, saboda har ya na iya ganin gumi da hawayen da suka jiƙa fuskarta.

Karo na farko a rayuwarsa ya saki bindiga daga hannunsa, a karo na farko ya yi na damar karɓar wannan assignment ɗin, a karo na farko a rayuwarsa tsoron wanke kansa a gaban wani ya kama shi.

A dai-dai lokacin Rhoda, Alandi, Jagwado da Zuzu suka iso wurin cikin gudu, su ma a tsorace suke kallon Rabi'a, wadda ke kuka tana girgiza musu kai, sai kuma ta juya da gudu tana fashewa da kuka.

“Raja ka bita ka mata bayani”
Rhoda ta faɗi hankali a tashe, cikin sanyin jiki Raja ya girgiza mata kai ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama.

Ko yau ma sai da ya fito ya tsaya a ƙofar estate ɗinsu ko zai ga wucewarta, amma haka ya tsaya a wurin har na tsawon awa biyu, amma babu ita babu dalilinta, hakan ya sa ya ɗauka cewar ba ta zo ba.

Haka ya koma gida cikin rashin jin daɗin zuciya, ba don ransa na so ba, suka shiga dudduba makaman da suka karɓa a wurin wannan mutumin shi da su Rhoda, kuma a lokacin kamar da aka ce ya kalli window ya hango inuwar mutum.

Hakan tasa ya tashi ya fita waje don ya duba, kamar yanda ya yi zato, ɗan leƙen asiri ne aka turo musu, daren gudu suka shiga yi a layin shi da mutumin, har zuwa lokacin da Allah ya ba shi iko ya harbi mutumin, ashe rabom Rabi'a za ta gani ne.

“Duk abin da zan faɗa mata yanzu ba za ta fahimta ba.

May be next time?”
Ya yi maganar cikin raunin zuciya, kuma ya na gama faɗin hakan ya juya ya fara tafiya.

Abun da be sani ba shi ne, da ace ya bi Rabi'a a wannan lokacin, da wata ƙaddarar ba ta faru ba, wata ƙaddara da za ta tarwatsa komai, ta kuma zama sanadiyyar shiryuwar wasu lamura.

Don a wannan juyawar da ya yi, wata mota ƙirar Lamborghini ta wuce ta gefensa.

Har su Rhoda na tare gawar mutumin dake yashe aƙasa, gudun kada me motar ya samu danar ganin gawar.

Sosai Rabi ke kuka, zuwa lokacin ta dena gudun, tafiya kawai take, ba tare da tasan inda take cilla ƙafarta ba.

Wai me ya sa ne?, me ya sa ita ba ta da sa'a a rayuwa?, me ya sa komai yake cakuɗe mata?, shin sai yaushe ne za ta saku dawamammen farin ciki?, sai yaushe?, sai yaushe?.

Ta na cikin waɗanan saƙe-saƙen nata, wata mota ta tsaya a bayanta, kuma duk da ta ji kamar tsayuwar mota a bayanta bai sa ta waiga ba.

USMAN POV.

Shi da abokansa biyar ne ke cikin sabuwar motarsa ƙirar Lamborghini, Bash, J-boy, Jaz, Bareeki sai kuma shi kansa. dawowarsu kenan daga wani club, inda suka je suka yi tatul a can, kuma yawon shaɗancin nasu ne ya biyo da su ta Joy Emodi CI.

“Guys!

Kun ga wata can!”
Cewar Bareeki ya na nuna wata yarinya dake tafe a gefen titi, yanayin tafiyar yarinyar kaɗai zai sa ka fahimci cewar ba a hayyacinta take ba, Daga gidan ba ya na motar Usman ya furzar da hayaƙin shishar da ya shaƙa daga bakinsa, sannan ya furta abun da ya zama sanadiyyar faruwar ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta a cikin wannan daren.

“Sanƙamoma mana ita!”
Su duka suka kwashe da dariya, kafin Bareeki ya yi parking motar ba tare da ya kasheta ba, shi da J-boy suka fita daga motar, suka shiga bin yarinyar a baya suna dudduba layin, ko za su ga wani, sai da suka tabbatar da babu wanda ke ganinsu, kafin suka yi sauri suka suntumi yafinyar, Bareeki ya riƙe ƙafafunta, J-boy kuma ya riƙe kafaɗunta yana rufe mata baki, suka yi maza suka dannata a mota, da mugun gudu suka bar layin.

Kai tsaye suka nufi gidan Usman ɗin Kubwa.

MISHAL POV.

Yau a gajiye ta dawo gida, hakan ya sa tana yin wanka ta yi sallah sannan ta kwanta don ta huta, ba tare da ta ankara ba bacci ya kwasheta.

Ba ita ta farka ba sai ƙarfe huɗu, haka ta tashi jiki a mace, saboda baccin yamman da ta yi, banɗaki ta shiga ta yi brush, haɗi da alwala, ta futo ta yi sallah.

Saboda yunwar da take ji tana idar da sallahr ta wuce kitchen, ba za ta iya jira sai ta girka wani abu ba, don haka ta ɗauki youghurt da cake, ta zauna ta ci har ta bawa Ayra.

Bayan ta kammala ta tashi ta shiga share gidan, kuma tana cikin sharar falon ne ta ji an turo ƙofar falon, hakan ya sa ta ɗago daga sunkuyen da take, ta kalli ƙofar falon, mata biyu ne suka shigo, ɗayar kawai ta iya ganewa, ita ce wannan wanda Annan ta kira da ƙanwar Kuliya.

Amma ba wannan ne abun dubawar ba, kallon da ɗayar ke mata ne abun tuhuma.

Saboda wani irin kallo ne da ta saba samun irinsa daga wurin Hajjara, wato kallon tsana.

KULIYA POV.
_“Abu Aswad.Magungunana sun ƙare, please ka siyomin idan ka fita”._
Abun da ta faɗa masa kenan da safe, kuma a lokacin sai ya aje mug ɗin hannunsa wanda yake ɗauke da coffee me zafi, ya kalleta, sannan ya kalli takardar hannunta, hannunsa ya kai ya karɓi takardar, kafin ya karanta, sunayen magunguna ne guda biyu kacal, kansa ya ɗan karkatar gefe yana kallonta.

A gefe guda kuma ya na shaƙar ƙamshin ƙwan da ta gama soyawa a kitchen, wanda ta haɗa sandwich da shi, sai da ta masa bismillahr sandwich ɗin, amma ya ƙi ci, don har yanzu miskilancin ba zai bar shi ya ci ba, duk da a kullum idan ta yi girki sai ya burgeshi.

Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama a yayin da yake juya sitiyarin motar zuwa kwanar da za ta kaishi gidansa.
_“Shin ka san wani abu a kan Hysteria?”_
Abun da ya tambayi me pharmacyn da ya siyi maganin a kenan a ɗazu, dom a dazu bayan da ya siyi magungunan ya juya zai tafi, sai kuma ya tsaya ya juyo ya cilla masa wannan tambayar.

A ɗazun mutumin sai ya ɗan taɓe bakinsa cikin faɗin.
_“Eh to, a gaskiya ba sosai ba.

Amma dai na san cewa cutar ta na kama da hauka.

Haka dai kamar jinni, mafi akasarin masu ɗauke da cutar mata ne, za ka ga mace ta na gasping kamar me asthma, a wasu lokutan ma harda suma.

Abun da kan haddasata kuma shi ne ongoing stress, sannan kuma abun na kama da tsoro, ko tsana.

Misali; kai abokina ne, sai muka samu wata matsala a tsakaninmu, sai nake ji a raina ba na san ganinka kwata-kwata, wata ƙila kuma wurin aikin mu ɗaya, wata ƙila kuma ɗakin kwanan mu ne ɗaya, ko kuma dai ya zaman dole da akwai wani aabu da zai haɗamu, to wannan dolen ita take haddasa ciwon, duk abun da kasan ba ka so, kuma ya zama dole ka haɗu da shi, ko ka ji shi, shi ne yake haddasa hysteria, wannan samuwar dolen ita ce sila.

Dalilina na cewa abun ya na kama da iska shi ne, yanzu zan ga abun da ba na so, nan take zan shiga gasping, ina breathing kamar me asthma, amma daga zarar wannan abun ya tafi, ko ya bar inda nake, zan dawo normal, kamar komai bai taɓa faruwa ba, kamar ma ba nine na ke gasping ko na suma ba.

Sannan akwai hanyoyin magance ta, dole ne a ƙauracewa yin abun da me ɗauke da cutar ba ya so, sannan kuma a duk sanda za ta tashi, a kwantarwa da mutum hankali, a faɗa masa soothing words, a kuma yi gaggawar kawar da abun da ya jawo tashin ciwon.

Iyaka abun da na sani kenan!”_
Ɗaya bayan ya ɗauke kalaman mutumin, babu abun da ya bari ƙwaƙwalwasa ta yi missing.
Chapter 43 · 0% Book details