← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 80

Sashe 39

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ga kayan girki, kuma nagode”
Sunan ɗazu ta kuma faɗa, hakan ya sa ya ɗago da kansa daga barin kallon wayar ya kalleta, a wannan karon ita ma shi take kallo, me makon ya bata amsa da baki sai ya gyaɗa mata kai.

Yana ɗaga kafaɗa.

“Ga abinci nan na rage maka.

Za ka ci?!”
Yawu ya haɗiya a fakaice, ya ɗan saci kallon abincin nata, a kan me zai ci wannan abinci?

Zai fiye masa sauƙi ya sha coffeen sa, duk da ransa ya biya abincin, ga ƙamshinsa da ya cika masa hanci.

Sai ya daure ya girgiza mata kai alamun a'a.

Juyawa ya yi ya kashe coffee maker ɗin, sannan ya fara firfita shi.

Mishal ta taɓe baki cikin faɗin.

“Ba dole ma mutum ya gamu da ulcer ba, ba tare da ka ci abicin ba ka tashi ka ɗirkawa cikinka baƙin shayi da sassafe, kuma fa ita ciyawar shafin nan, amfanita a jikin mutu shi ne saka digestive system aiki cikin gaggawa...

To ka tashi ka sha baƙin shayi ba tare da ka ci abinci ba, me zai faru kenan?!”
Kuliya ya aje mug ɗin hannunsa ya na kallonta, wai da shi take?, to ai shi ba ma baƙin shayi yake sha ba, coffee ne.

Sai ya ƙi ya kulata, ya shiga shan coffeensa a nutse, har ta gama surutanta ta cinye abincinta ta wanke kwanukan ta ɗauki Ayra ta bar kitchen ɗin shi bai gama shan coffeen ba.

Ko da ya fito daga kitchen ɗin a falo ya sameta, zaune kan kujera tana kallo tv.

“Sai na dawo”
Ya faɗi murya ƙasa-ƙasa ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama.

Mishal ta miƙe tsaye, hannunta na hagu riƙe da Ayra.

“Na raka ka ne?”
Ya ɗan ja da baya ya na kallon kayan jikinta, har yanzu pyjamas ne, da alama ko wanka ma ba ta yi ba.

“Na gode.

Ki kula da kanki”
Ya na ƙarashewa ya kama hanyar fita, bakinta ta taɓe tana zama, ai shi ya jiyo.

Yinin ranar haka ta ƙarashe shi cikin farin ciki, da rana sakwara da miya ta girka, kuma har me gadin gidan ta zubawa, da daddare kuma ta girka tuwon shimkafa, bayan ta ci, sai ta ɗan yaɓa aikin makaranta, kafin ta kwanta, ita zama cikin kaɗaicin ma sam be dameta ba, don ta saba zama ita kaɗai, bare kuma akwai girki, ga kallo ga kuma Ayra.

Mamakinta ɗaya, ta na som sanin dalilin da ya sa ya fita yau, bayan yau ana cikin weekend, kuma har ta kwanta bai dawo ba.
*Hotoro, Ring Road, Kano...*
“Sai na dawo Mesoma”
Cewar Uchechi tana rungume da yayarta, sakin juna suka yi Mesoman na mata murmushi, a satin da ya wuce Uchechi ta riga ta yankewa kanta shawarar tafiya Abuja, kuma ta yarda da za ta yi abun da Mesoman ta ce mata, don ta samu ta cimma burinta a kan Raja.

Wato bugar da shi ta hanyar saka masa maganin bacci a cikin abun sha, ta riga ta yankewa kanta hukuncin za ta iya, kuma ba ta jin akwai abun da zai dakatar da ita daga yin hakan.

A da ta na tunanin ta ya za ta aikata masa hakan saboda su Rhoda dake tare da shi a koda yaushe, sai kuma ta samo mafitar ɗaukarsa ta bar gidan da shi.

Za ta cemasa ya ɗauketa su fita yawo, kuma a wannan yawon da zai kaita za ta samu damar da za ta cimma manufarta a kansa.
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja...*
“Nemo min lambar Nimra”
Cewar Jadda wadda ke danƙawa Hajjara wayarta, Hajjara ta karɓa tana yatsina fuska, don Allah ya san,i ita Wallahi ta gaji da zama da wannan masiffafiyar tsohuwar, duk ta bi ta isheta, Allah-Allah take ta koma Maiduguri.

Zaune suke a falo, daga can gefe kuma Mama Ladi ce ke bawa Daala abinci.

“Ga shi.

Ta shiga”
Ta ƙarashe tana miƙawa Jadda wayar, Jadda ta karɓa tana tsara kalar masifar da zatawa Nimran.

“Falmata!

Tun muna sheda juna da ke ki saka wanan ɗan yankan kan da ya aurar min jiki ya saketa, Wallahi idan ba haka ba zan ɗau mummunan mataki a kanku daga ke har shi!”
Kalamanta na farko kenan, bayan da Nimra ta ɗaga wayar, daga cikin wayar Nimra dake zaune a office ɗinta ta yi murmushi.

“Da ma na san mijin Mishal ɗin ne?”
“Ko kin san shi ko ba ki sanshi ba wannan be shafe ni ba, abun da na sani kawai shi ne ke ce kika danƙa masa jikata ya tafi da ita, don haka tun muna sheda juna ki nemo mun gidan da ya kaita, in ba haka ba!...”
Daga haka ta kashe wayar tana kumfar baki, A fakaice Hajjara ta saci idon Jadda tana watsa mata harara.

Jadda ta miƙe tare da nufar hanyar ɗakinta rai a ɓace.

“Mtswww!, aikin banza, wai ita a nan me san jikoki, ƙaaaa!”
Ta ƙarashe da ƙwafa.
*
Jadda na sauƙe wayarta, Nimra ta lalubo lambar wani masanin kan na'ura me ƙwaƙwalwa dan ya binciko mata lambar Kuliya.

Jim kaɗan sai ga saƙo ya shigo wayarta, kuma ba jira ta aika masa kira.

Daga can DSS Headquarter, Kuliya dake tsaye a ɗakin horo ya na hora wani me laifi ya ji kamar wayarsa na vibrating, hakan ya sa ya saki wayoyin lantarki dake hannunsa ya juya ya fice daga ɗakin, don ya samu ya amsa wayar, abakin ƙofar ɗakin ya iske Sharon, don haka ya yi mata alama da ita ta shiga ta ci gaba.

Ganin baƙuwar lamba ya sa shi ɗan jinkirtawa kafin ya ɗaga, kuma kamar ma ba zai ɗaga ɗin ba, sai da kiran ya shigo a karo na uku sannan ya ɗaga.

Tun daga jin muryarta ya ganeta, hakan yasa suka gaisa a mutunce, kafin dalilin kiran ya taso.

“Magana ce a kan Mishal, ɗazu kakarta Jadda ta kirani.

Wai ta na so ta san inda aka kai mata jikarta.

Na san ko ni ban faɗa mata ba, za ta iya nemo address ɗin gidanka, Jadda bata san zaman lafiya, don haka ko da wasa kada ka bari ta ɗauki Mishal daga cikin gidanka.

Saboda ko a sanda tana ƙarama Abubakar be bata renonta ba, bare yanzu da ta girma, zamanta a wurin Jadda ba ƙaramar matsala ba ce!”
Kuliya ya ɗan yi jimm, to a kan me ma zai bari wata Jadda ta ɗauketa?, ai a yanzu ba ya jin ko ita kanta Nimran za ta iya raba shi da Mishal, Mishal amanarsa ce, babu yanda za ayi ya bar wani abun cutarwa ya sameta, zai yi duk iya iyawarsa don ganin be bari an cutar da ita ba.

Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya amsa mata da.

“Insha-Allah”
Daga haka ya mata godiya ya sauƙe wayar.
*Joy Emodi CI St.*
RABI'A POV.

Tafe suke ita da Raja a kan titin, hira yake mata jifa-jifa, sama-sama take ba shi amsa, don yau gaba ɗaya tunaninta ba ya jikinta, tunaninta ya lula kan maganarsu da Yaya ta jiya.
_“Rabi'a da ace kina sona, da za ki bi abun da na faɗa.

Saboda Allah ya za'ayi ki riƙa kula wani da sunan me kamarki, kika sani ma ko ɗan satar mutane ne, ni dai gaskiya ki dena kula shi.

Dan har ga Allah ba na so!...”_
Kalamansa gareta kenan a jiya da daddare da ya zo fira, ita ba ta ɓoye masa komai game da Raja, duk ranar da suka haɗu da shi sai ta faɗa masa sun haɗu da wannan me kamarta tata, abun da ko Anti Saratu ba ta faɗawa ba, shi ne; Raja na kama da ita, kawai ta faɗa mata cewar suna mutunci da shi.

“Ammata?”
Ya kira sunanta a lokacin da suka fita kan babban titi, juyowa ta yi ta kalleshi, a zahirin gaskiya ba za ta iya dena kula Raja ba, don tana da tabbacin shi ɗan uwanta ne, alaƙar jinin da suka haɗa ce ta sa ba za ta iya haƙura da shi ba, don a yanda take ji za ta iya rabuwa da Yaya a kan Raja, kuma akwai wani abu a kan Rajan dake motsi a ƙasan zuciyarta, duk da ta na amfani da duka ƙarfinta wurin danne shi, don bisa ga dukkan alamu hakan ba me iyuwa ba ne.

Ko kafin Raja ya kuma faɗin wani abu, wata motar taxi da ta tsaya a bakin titin ta ɗau hankalinsa, hakan ya sa ya ci gaba da kallon motar har zuwa lokacin da aka buɗe gidan baya na motar, Uchechi ta fito, fuskarta ɗauke da wani abu me kama da fushi da kuma ɓacin rai.

Hakan yasa fuskar Raja rikeɗewa zuwa mamaki, yaushe ta zo?, wa ya bata address ɗin inda yake?.

Ganin yanda Raja yake kallon bayanta ya sa Rabi'a juyawa, kuma tana juyawar idonta ya sauƙa a kan wata budurwa dake tsaye kisabda wata motar taxi.

Kallo ɗaya za ka mata kattabatar da cewa ita Cristian ce, saboda yanayin shigarta.

Amma kuma ita Raja yake kallo ?, ko me?.

To mi ye haɗinsa da ita?.

Kuma ga shi ma ta ahiga tunkarosu.

Ba ta ankara ba ta ji hannun Raja cikin nata, sanna a hankali ya ja ta ya mayar da ita zuwa bayansa, dai-dai da isowar Uchechi gabansa, kuma tana zuwa ta ɗaga hannunta sama ta shararawa Raja mari.

Har saida ya karkatar da fuskarsa, Rabi ta tsorata sosai, ido waje take kallon gefen fuskar tasa.

Zuwa lokacin har Uchechi ta fara hawaye, ta nuna Raja da ɗan yatsa ta na faɗin.

“Macuci.

Ma ci yi amana, da ma ashe yaudarata kake?.

Saboda wannan 'yar talakawan kake yaudarata?”
A hankali Raja ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya juyo ya zuba lumsassun idanuwansa a kan Uchechi.

Kafin ya furta abun da ya wargazo da duniyar Rabi da kuma Uchechin zuwa ƙasa.

“Uchechi!

She is my wife to be.

So show some respect!”
Bakin Rabi ya faɗo a har ƙasa, kallon bayan Raja kawai take tana ƙarawa, ai ba ta ganin fuskarsa, wata ƙila ma daga wani wurin maganar ta fito, ba daga bakinsa ba, inaa, wai Raja?, kai!

Wallahi da sake, ba shi ya faɗi wannan zancen ba.
Chapter 39 · 0% Book details