← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 80

Sashe 56

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Rabi”
Ta furta a raunane ta na rungume Rabin, tare da fashewa da kuka, har mutanen dake wucewa ta lungun suna kallon su, duk dauriyar Rabin sai da ta zubar da hawaye, Anti Saratu ta saketa ta na dudduba fuskarta ta ɗan hasken dake layin.

“Rabi ina kika shiga haka?...

Kusan kullum sai Fu'ad ya je nemanki makarantar da kike aiki, amma haka zai dawo yace min ba a sameki ba, har police station ya kai ƙara, amma babu wani bayani”
Rabi ta ɗan yi murmushi ta na share hawayenta, a ƙalla de tana da wani wanda ya damu da ita a duniya, Allah ya sa har yanzu akwai wani wanda yake santa har zuciyarsa, kuma ta san da ma duk wannan tsawon kwanakin da ta shafe bata gidan babu wanda zai nemeta bayan Saratun.

“Ƙaddara ce ta zaunar da ni a can, ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta a kaina, irin abun da mahaifinmu yake shi ne aka aikata min, mutum biyar Anti Saratu, su biyar suka haikemin!”
Saratu ta ƙara fashewa da kuka ta na rufe bakinta, tare da girgiza kanta.

“Ki dena kuka Anti Saratu, ya wuce fa, Allah ya hukunta cewar dole sau hakannta faru da ni, kuma ga shi ya farun!”
“Yanzu ina za ki je?”
“Gidan kawu Habu zan tafi”
Ta faɗa don ta san babu inda za ta iya zuwa a yanzu da ya wuce can ɗin.

Anti Saratu ta gyaɗa kanta tana saka hannu a aljihun doguwar rigar jikinta, sannan ta zaro kuɗi wurin dubu goma ta kamo hannun Rabin ta danƙa mata.

“Ga shi, ban sani ba ko za su amfane ki”
Rabi ta karɓa, sannan ta gode mata, Saratu na tsaye a ƙofar gidan har Rabin ta fice daga lungun.

Rabi na fita daga lungunsu ta wuce shagon Yaya, don ba za ta iya zuwa ko ina ba tare da ta sanar masa da halin da take ciki ba.

“Ka yi shiru Yaya?”
Rabi ta faɗi cikin hawaye, yayin da take zaune a kan benci tana kallon Yaya, bayan da ta gama tsara masa duk halin da ta shiga, da farko da Yayan ya ganta ya yi farin ciki, amma tun da ta fara bashi labarin abun da ya faru da ita sai ta ga yanayin fuskar Yayan ya sauya.

“Ba komai”
Yayan ya faɗi ya na kawar da kansa, mamaki ya bala'in kama Rabi, yau ita Yaya yakewa magana a haka?, ita ce ta masa magana ya amsa mata ciki-ciki?, me yake faruwa ne?.

“Yanzu ya kake ganin za ayi”
“Ai yanda za ayi kawai shi ne ki kama gabanki, dan ni babanmu ya min mata, kuma nan da wata ɗaya za ayi auren!”
Da farko sai da Rabi ta ji wani irin duka a ƙirjinta, daga baya kuma sai ta yi murmushi me ciwo, to ita wai yanzu ma miye zai bata tsoro ne?, ai taskun rayuwa ba yau ta fara shigarsa ba, halayen ɗan adam babu kalar wanda bata gani ba, uban da ya haifeta ma ya ƙita, waye wani Yaya?, da dan har ya gujeta za ta ji ciwo?, ai da ma haka rayuwar take, wani zai soka da yini, sai ya ƙika da daddare,wani da ma can ba da zuciya ɗaya yake sanka ba, amma kai da ka so shi da zuciya ɗaya idan ka yi haƙuri Allah zai nuna maka ƙarshensa, ga shi yau ita ma ta ga zahirin Yaya.

Hawayenta ta goge, dan babu amfanin barinsu su zuba, ba za ta ƙara barin hawayenta su zuba a gaban wani ba, ko kukan za ta yi gwara ta ɓoye a wani wurin ta yi, ganin hawayen mutum na ɗaya daga cikin lagonsa, 'A strong woman will always turn pain into power' haka ta faɗawa kanta, dan haka za ta yi iya bakin iyawarta don ta yaƙi abun da zai durƙusar da ita, saboda haka Yaya bai bata mamaki ba.

Miƙewa ta yi tana murmushi ta kalli Yaya a tsakar ido tace.

“To Yaya, Allah ya sanya da alkairi, ka gaida sabuwar amaryar, ni na tafi, sai bayan saduwa kuma!”
Daga haka ta juya ta fice.

Yaya ya ja wani dogon tsaki ya na jan wayarsa, shi mahaukacin ina ne zai yarda ya aureta bayan ta faɗa masa cswar maza har biyar sun mata fyaɗe?, ai yanzu a yanda take bata da maraba da karuwa, ko karan hauka ne ya cije shi ai ba ya yi wannan gangancin ba, gwara ta je ta can, ta ƙarata, wata ƙila ta samu wani ɗan tasha kamar babanta, sai ya temaka mata ya aureta, amma shi dai bai ga abun da zai yi da ita ba, da ma ba ita kaɗai ba ce budurwarsa, idan auren yake so ai sai ya zaɓi ɗaya daga cikin 'yan matansa ya ce zai aura, amma ba Rabi ba, dan a yanzu ta riga ta zama tarihi a rayuwarsa, shi da ma can don kyanta yake santa, yanzu kuwa da aka mata bajo a fuska ub*n wa ya aikeshi aurenta.
*
“Haka shi Ɗan Lamin yace”
Cewar kawu Habu, bayan da Rabin ta gama masa bayanin abun da ke faruwa.

Dan tana barin shagon Yaya gidansa ta nufa, durƙushe take a gabansa, yayin da shi kuma yake zaune a kan kujera.

Rabi ta gyaɗa masa kai, idanunwata a bushe ƙamas, babu wani damshin ƙwalla ko ɗaya a ciki.

Kawu Habu ya ci gaba da kallon Rabi cike da tausayi, ya girgiza kansa sannan yace.

“Babu damuwa, tashi ki shiga ɗakin Laure”
Miƙewa ta yi sannan ta shiga ɗakin matarsa ta biyu, wato Anti Laure, mace me kirki da karamci.

Yaranta biyu da Kawu Habun.

Zama ta yi daga bakin gadon Anti Lauren, inda ta sameta tana matsar ƙwalla, kasancewar inda suka yi maganar kusa da windown ɗakinta ne, dan haka Rabi ta fahimci cewar zancen nasu ta ji.

“Sannu kin ji Rabi”
Rabi ta yi murmushi ta na kauda kai.

A hankali Ramatu matar Kawu Habu ta farko ta saki labulen ɗakinta, bayan da ta gama leƙen kawu Habun da Rabi, sannan duk abun da suka tattauna kaf a kunnenta, ita kuma a matsayinta na aminiyar Habiba, ba za ta yi shiri ba tare da ta sanar mata da labarin ba.

Dan haka ta lalubo wayarta ta fesawa Habiba kaf abun da ya faru.
*
Cike da takaici Habiba ta wurga wayarta kan gado, bayan da ta gama sauraron bayanan Ramatun, ita ta ma manta da gidan Habun, ta manta cewar idan aka kori Rabi daga nan can za ta nufa, amma ba komai, wannan ma ba zai gagara ba, ita ta san abun yi.
*No.181,Guzape, Abuja...*
MISHAL POV.

Tana kunna tv a falo aka turo ƙofar falon, hakan ya sa ta juya da sauri ba tare da ta kunna tvn ba, yanayinsa kawai ya bayyanar mata da halin da yake ciki, don ta riga da ta gama gane shi, abu ƙanƙani yake fusata zuciyarsa, kuma kusan kullum haka yake dawowa gidan.

Ba ta ce masa ƙala ba face kallonsa da ta yi har ya wuce ɗakinsa, dan ta riga ta gano cewar idan ya na a fusace baya san a masa magana.

Bakinta ta taɓe ta kunna tvn, sannan ta juya ta koma kitchen.

Girkinta ta ƙarasa, sannan ta ɗebe komai ta shirya a kan danning.

Ta dawo falo ta zauna tana kallo, ba ta shirya masa magana ba sai bayan shuɗewar muntuna kusan ashirin.

Ta miƙe daga kan kijera, sannan ta nufi ɗakinsa.

Bata ƙwanƙwasa ba, dan ta san ko ta ƙwanƙwasa ba lalle ya amsa mata ba, yaya lafiyar kura, balle ta yi zawo, tsaye ta ganshi jikin mirror, ya na taje sumar kansa.

Ta ci kin mirror kawai ya kalleta, sanye take da wata farar off shoulder shirt, sai wani baƙin short culottes, wanda bai ƙarasa kan guwarta ba, ya ɗauke kansa ya na ci gaba da taje sumar kansa.

Mishal ba ta damu ba, dan idan da sabo ta saba da wannan abun nasa , babu me iya zama da Kuliya sai me haƙuri, tsayawa ta yi a gefensa tana kallonsa, amma bai ko kalleta ba, sai ta rakaɓa ta gefensa ta shiga gabansa ta tsaya, wata gajeriyar harara ya maka mata, sannan ya kauce ya na ci gaba da tazar, Mishal ta ƙara matsawa ta tsaya a gabansa, sannan ta saka hannayenta ta karɓi matajin hannunsa, ta yi tattage dan ta ƙara tsayi, sannan ta shiga taje masa sumar.

Memakon ya tanka mata, sai ya mata banza ya juya ya barta tsaye da matajin a hannu, Mishal ta girgiza kanta ta na mitar halin wanga bawan Allah, sannan ta aje matajin a kan mirror, ta biyo bayansa.

Zama ya yi a bakin gado ya na kawar da kai.

Mishal ta yi murmushi ta na tsayawa a gabansa, hannunta ta sa ta kamo haɓarsa ta juyo da fuskarsa gareta.

“Me nene?”
Fuskarsa ya ƙwace sannan ƙara juyar mata da kai, sunkuyawa ta yi ta kai hannunta kan buttons ɗin gaban rigarsa ta buɗe guda huɗu, duk bai kulata ba, sannan ta hau kan gadon ta zagaya ta bayansa, ta tsaya a kan gwiwoyinta, tare da saka hannayenta a kan kafaɗunsa, ta fara masa tausa.

“Me nene ?”
Muryarta ta tambaya bayan wani lokaci, memakon ya amsa mata, sai ya saka hannunsa na dama ya kamo nata, tare da ƙoƙarin janyota zuwa gabansa, hakan ya sa ta miƙe ta sauƙa daga kan gadon ta tsaya a gaban nasa, sai kuma ya kamo hannunta ya zaunar da ita a kan cinyarsa ta dama.

Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na sofara gashin da ya sauƙo mata kan fuskarta a bayan kunnenta, a lokaci guda yana kallon fuskarta.

Mishal ta lumshe idonta ta buɗe, sannan a hankali hannayenta suka kewaya bayansa, kafin ta saka kanta a cikin wuyansa.

“Me ya faru ?”
Muryarta ta fito a kan fatar wuyansa, yanayin ya sa Kuliya lumshe idonsa sannan ya buɗe, ya saka hannayensa ya ƙara rungumeta a jikinsa.

“Game da binciken yayarki ne...”
Sai kuma ya yi shiru.

Mishal ta sumbaci wuyansa ta na ƙara matse hannunta a bayansa.

“Ummhum?”
Muryar tata ta kuma faɗi a wuyansa.
Chapter 56 · 0% Book details